Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi

Asalin hoton, Reuters
Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta ƙaddamar da wani hari da ba a taba gani ba a kan Isra'ila, inda mayakanta suka shiga cikin al'ummomin da ke kusa da Zirin Gaza, kuma suka kashe mazauna yankin tare da yin garkuwa da wasu.
Ga abin da kuke buƙatar sani game da mutane, da wuraren da abin ya shafa - da kuma muhimman yankuna don fahimtar wannan labarin.
Wace ce Hamas?
Hamas, kungiya ce ta masu iƙirarin jihadi ta al'ummar Falasɗinu da ke mulkin a yankin Zirin Gaza.
Hamas dai ta sha alwashin halaka 'yan Isra'ila, kuma ta sha faman gwabza yaƙe-yaƙe da Isra'ila tun bayan da ta karbi mulki a Gaza a shekara ta 2007.
A tsakanin wadannan yake-yaken, ta bai wa wasu kungiyoyi damar harba dubban makamen roka kan Isra'ila, tare da kai wasu munanan hare-hare.
Har ila yau, Isra’ila ta sha kai wa Hamas hare-hare ta sama, sannan tare da Masar, sun killace yankin Zirin Gaza tun shekara ta 2007, a wani mataki da ta ce na tsaron lafiyarta.
- Bayani a kan Hamas
Hamas baki ɗayanta, ko kuma a wasu lokutan reshenta mai gwagwarmaya da makamai, Isra'ila da Amurka da Tarayyar Turai da Birtaniya da kuma sauran wasu manyan kasashe masu karfi sun ayyana ta a matsayin kungiyar ƴan ta'adda.
Hamas dai na samun goyon bayan Iran ne, wadda ke ba ta tallafin makamai da horaswa.
Mene ne Zirin Gaza?
Zirin Gaza yana da tsawon kilomita 41 da fadin kilomita 10 tsakanin Isra'ila da Masar, da kuma tekun Bahar Rum.
Zirin Gaza matsuguni ne ga kusan mutum miliyan 2.3, kuma tana ɗaya daga cikin yankuna mafi yawan cunkoson jama'a a duniya.
- Yaya rayuwa take a zirin Gaza?
Isra'ila ce ke iko da sararin samaniyar Gaza da gabar tekunta kuma ta takaita irin kayayyakin da aka bai wa izinin shiga da fita ta mashigin iyakar zirin.
Haka zalika, Masar tana iko da masu shiga da fita ta iyakarta da Gaza.

Me ya sa Isra'ila da Hamas suke fada?
Akwai zaman ɗar-ɗar a ko da yaushe tsakanin Isra'ila da Hamas, amma harin da mayakan Hamas suka kai a ranar Asabar, ya zo ne ba tare da gargadi ba.
Hamas ta harba dubban makaman roka a kan Isra'ila, yayin da mayaƙa da dama suka kutsa kai cikin iyakarta, sannan suka mamaye yankunan Isra'ila, inda suka kashe fararen hula da dama tare da kama wasu.
Isra'ila ta kai hare-hare ta sama cikin hanzari, tana cewa tana auna "wuraren da 'yan ta'addan Gaza" suke.
Ta yaya ya zama harin da ba a taɓa ganin irinsa ba?
Kamar yadda editanmu na kasashen duniya, Jeremy Bowen ya rubuta, wannan shi ne aiki mafi girma da Hamas ta taba kaddamarwa daga Gaza kuma mafi munin harin wuce gona da iri da Isra’ila ta fuskanta a cikin fiye da tsawon wani zangon rayuwa.
Mayakan sun keta shingen wayar da ta raba Gaza da Isra'ila a wurare da dama.
Harin wanda ba a taba ganin irinsa ba, ya zo ne kwana guda bayan cikar shekara 50 da harin ba-zata da Masar da Siriya suka kai a 1973, wanda ya fara yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Muhimmancin ranar ba zai rasa nasaba da shugabancin Hamas ba.
Shin wannan babbar gazawa ce kan tattara bayanan sirri daga Isra'ila?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Eh, in ji wakilinmu na tsaro, Frank Gardner tare da hadin gwiwar Shin Bet, Hukumar tattara bayanan sirri a cikin Isra'ila da kuma Mossad, hukumar leken asirinta a kasashen waje da kuma dukkan kadarorin rundunar tsaron Isra'ila, ya ce abin mamaki ne a zahiri cewa babu wanda ya ga alamun zuwan wannan hari.
Haka kuma, in ji an gaza yin komai, ko da kuwa a ce an sami gargaɗi game da harin.
Isra'ila tana da, duk da yake wasu za su iya musun haka, hukumomin leƙen sirri mafi girma da kuma samun kuɗi a Gabas ta Tsakiya tare da masu tsegunta bayanai da wakilai a cikin kungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa, da kuma a Lebanon da Siriya da sauran wurare.
A kasa, wajen katangar kan iyaka tsakanin Gaza da Isra'ila akwai kyamarori da na'urorin da aka binne waɗanda suke zuƙo dumin jikin mutum da kuma sojojin ƙasa masu sintiri.
Katangar saman da aka yi wa shinge da wayoyin ƙarfe ya kamata ta hana ainihin kutsen da aka yi a wannan hari.
Amma duk da haka mayakan Hamas sun shiga ta hanyar yanka kofofi a jikin wayoyin karfen da kuma ta hanyar shiga Isra'ila daga teku har ma da amfani da mayaka masu saukar lema.
Mene ne Falasɗin kuma mene ne alakar abubuwan da suka faru da ita?
Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza, wadanda aka fi sani da yankunan Falasɗinu, da kuma Gabashin Kudus da Isra'ila duk sun kasance wani yanki na ƙasar da aka fi sani da Falasdinu tun zamanin Romawa.
Waɗannan kuma ƙasashe ne na masarautun Yahudawa a cikin Littafin injila kuma Yahudawa suna ganin su a matsayin tsohuwar ƙasarsu.
- bayyana kan iyakokin Isra'ila a taswira
An ayyana Isra’ila a matsayin ƙasa a shekara ta 1948, kodayake waɗanda ba su amince da ’yancin wanzuwar Isra’ila ba na kiran ƙasar da Falasdinu.
Falasɗinawa kuma suna amfani da sunan Falasdinu a matsayin Yammacin Kogin Jordan da Gaza da kuma Gabashin Kudus.
Me zai iya faruwa a gaba?
Kwamandan mayakan Hamas Mohammed Deif ya yi kira ga Falasɗinawa da sauran Larabawa da su shiga aikin ‘yan ta’addan na kawar da mamayar Isra’ila.
Wani babban abin tambaya a yanzu shi ne ko Falasɗinawa da ke yankin Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gabashin birnin Kudus ko kuma a wasu wurare na yankin za su saurari kiran nasa, in ji wakilin BBC na Kudus Yolande Knell.
Babu shakka Isra'ila na ganin yuwuwar yaƙin da zai iya ɓarkewa ta bangarori da dama. Wani mummunan yanayi shi ne cewa za ta iya shiga cikin babbar kungiyar gwagwarmayar Hezbollah ta Lebanon.
Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin ba da wani gagarumin karin sojoji. Kazalika hare-haren da ta kai ta sama a Gaza, ya nuna cewa tana shirin kai farmaki a can.











