Me ya janyo gagarumar zanga-zangar da ake yi a Isra'ila?

Zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zanga-zangar ta kasance mafi girma da Isra'ila ta taɓa gani a tarihi

Isra'ila ta shiga wani hali na fuskantar gagarumar zanga-zanga da ba ta taɓa gani ba a tarihi, inda mutane ke adawa da tsarin da gwamnatin ƙasar ke son yi na sauya yadda ɓangaren shari'ar ƙasar ke aiki. Ga takaitaccen bayani kan abin da ke faruwa a ƙasar a halin yazu.

Me yake faruwa a Isra'ila?

Tun farkon wannan shekara,mutane suka fara haɗa manya-manyan zanga-zanga ta mako-mako domin nuna adawa da shirin gwamnati na kawo sauyi a wasu tsare-tsarenta. Zanga-zangar ta yi ta yaɗuwa, inda dubban ɗaruruwan mutane suka mamaye titunan Tel Aviv - birnin kasuwancin ƙasar - da kuma da wasu birane da garuruwa a faɗin ƙasar.

Masu zanga-zanga sun yi kira da a soke shirin kawo sauyi da Firaminista Benjamin Natenyahu ke son yi, inda suka bukaci da ya sauka daga mulki. Ƴan adawarsa na siyasa su ke jagorantar zanga-zangar, ko da yake tsananin adawa da sauye-sauyen ya kasance cikin ƴan siyasa.

Wasu sojoji ma da suka kasance kashin bayan sojojin Isra'ila - sun nuna adawarsu da sauyin ta hanyar kin zuwa aiki, inda hakan ya ƙara nuna fargabar da ake da ita na cewa yanayi tsaron ƙasar na cikin barazana.

Me ya tunzura mutane?

Abokan adawar mista Netanyahu sun ce sauye-sauyen za su saɓa wa tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar ta hanyar gurgunta tsarin shari'a wanda a tarihi ke bibiya ko sanya ido kan yadda gwamnati ke amfani da ikonta.

Wannan shi ne adawa mai karfi ga irin gwamnatin da ke kan karagar mulki a halin yanzu - na masu tsassaurar ra'ayi a tarihin Isra'ila - da kuma shi kansa Mista Netanyahu.

Masu sukar sun ce sauye-sauyen za su kare mista Netanyahu, wanda a halin yanzu ake tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa - tuhume-tuhumen da ya musanta - da kuma taimakawa gwamnati wajen zartar da dokoki ba tare da taka-tsan-tsan ba.

Wane irin sauyi ne ya janyo zanga-zangar?

Damuwar ita ce karfin gwamnati da kuma karfin kotuna na ganin sun tantance har ma da yin watsi da bukatun gwamnati. Gwamnatin - da wasu - sun ce sake fasalin ya ma wuce lokacinsa, kodayake tsare-tsaren sun wuce fiye da yadda mutane da yawa ke so.

Karkashin tsare-tsaren gwamnati:

. Ƙarfin Kotun Koli na sake duba ko fitar da dokoki zai ragu, tare da mafi rinjaye na ɗaya daga cikin Knesset (majalisar dokoki) na iya soke hukuncin kotu.

. Gwamnati za ta yanke hukunci kan wanda zai zama alkali, ciki har da Kotun Koli, ta hanyar kara yawan wakilci a kwamitin da ya naɗa su.

. Ba za a buƙaci ministoci su yi biyayya ga shawarar masu taimaka musu ba na ɓangaren shari'a ba - wanda babban lauyan gwamnati ke jagoranta - wanda a halin yanzu doka ta bukaci da su yi.

An riga an zartar da wani sauyi guda ɗaya a matsayin doka - cire ikon da babban lauyan gwamnati ke da shi na ayyana shugaba mai ci a matsayin wanda bai cancanta ya yi jagoranci ba.

Shin gwamnati za ta janye batun sauyin da take son yi ne?

Mista Netanyahu ya nuna turjiya ya zuwa yanzu, yana zargin shugabannin masu zanga-zangar da yunkurin kifar da gwamnati.

Ƴan adawar dai sun yi watsi da shawarwarin da gwamnatin ƙasar ta gabatar na sauya wasu sassa na shirin, suna masu cewa suna son a dakatar da su gaba ɗaya kafin a shiga tattaunawa, yayin da gwamnatin ta yi watsi da matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka.

Gwamnati dai ta ce masu kaɗa kuri’a sun zaɓe ta ne bisa alkawarin yin garambawul a ɓangaren shari’a, inda ta ce yunkurin hana ta ya saɓa wa tsarin dimokraɗiyya.

Haka kuma ana ganin ɓangaren shari'a na da sassaucin ra'ayi sannan kuma tsarin naɗa sabbin alkalan ba shi da wakilci.

Sai dai matsin lamba kan gwamnati na ƙaruwa a kullu-yaumin kuma ministan tsaron ƙasar damista Natenyahu ya naɗa, ya yi magana kan sake fasalin ɓangaren shari'a - lamarin da ya sa firaministan ya kore shi daga mukaminsa.