Za a binne dan kwallon Ghana Astu da ya mutu a Turkiyya

Christian Astu

Asalin hoton, Getty Images

A yau Juma'a ne za a binne gawar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Ghana Christian Atsu, wanda ya mutu sakamakon Girgizar kasar da ta afkawa kasashen Turkiyya da Syria a farkon watan Fabrairu da ya wuce.

Makwanni biyu bayan ibtila'in girgizar kasar ne aka gano gawar Atsu, tare da maida ta kasar Ghana domin yi masa jana'izar ban girma.

Za a gudanar da jana'izar ban girman a birnin Accara na kasar ta Ghana. Dubun dubatar masoya daga ciki da wajen kasar ne za su yi wa akwatin gawar Astu kallon karshe kafin binne shi.

Zakakurin dan wasan kwallon kafar Christian Atsu, ya shafe shekaru da dama ya na taka leda a kungiyoyin premier league da kulub kamar Chelsea, Newcastle da Everton.

Dan wasan mai shekara 31, ya bugawa mahaifarsa Ghana wasa har sau 65.

Ya kuma taimakawa kungiyar kwallon kafar kasa zuwa wasan zagayen karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015 da kasar Equatorial Guinea ta karbi bakunci, inda aka bashi kyautar dan wasan da ya fi zura kwallo a raga da kuma taurron wasa.

Duniyar tamaula za ta din ga tunawa da Atsu kan halayyarsa ta son taimakon jama'a, da taimakon na kasa da shi da talakawa a kasarsa ta Ghana.