Mece ce manufar ganawar Trump da Putin a Alaska ba tare da Zelensky ba?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, BBC News and Global Journalism
- Lokacin karatu: Minti 7
Shugaba Donald Trump ya ce yana da burin ganawa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a Juma'a mai kamawa yayin da suke ci gaba da ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen yaƙin Rasha a Ukraine.
Wannan ne yunƙuri na baya-bayan nan a ƙoƙarin Trump na dakatar da yaƙin kuma an sanar da hakan ne a ranar cikar wa'adin da ya bai wa Rasha na ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine ko kuma ta fuskanci ƙarin takunkumai.
Taruka uku da aka gudanar kan Rasha da Ukraine a wannan bazarar har yanzu ba su kai ga cimma ƙudirin dakatar da yaƙin ba.
Ga abin da muka sani game da taron tsakanin shugabannin biyu.
Me ya sa Trump da Putin za su gana?
Kafin Trump ya hau karagar mulki a Janairu, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine inda a lokacin ya yi ta iƙirarin cewa zai iya kawo ƙarshen yaƙin a ranar da ya hau kan mulki.
Sai dai tun lokacin, gwamnatinsa na ta ƙoƙarin ta cimma muradinta amma hakan ba ta samu ba.
Tun farko, tattaunawar ta janyo fata na gari sai dai daga bisani al'amuran suka dagule.
A watan da ya gabata, Trump ya tabbatarwa BBC cewa Putin ya ba shi kunya bayan ziyarar da jakadan Amurka Steve Witkoff ya kai lokuta da dama.
Lamarin ya ƙara fusata Trump lamarin da ya sa ya ƙaƙaba wa'adin ranar Juma'a ga Putin ya amince a gaggauta tsagaita wuta ko kuma su fuskanci ƙarin takunkumai.
Yayin da wa'adin ke ƙaratowa, Trump ya kuma sanar cewa shi da Putin za su yi ganawar gaba da gaba ranar Juma'a, 15 ga watan nan na Agusta.
Ganawar ta zo ne bayan da Witkoff ya yi wata muhimmiyar tattaunawa da Putin a Moscow ranar Laraba, kamar yadda Putin ya shaida.

Asalin hoton, ORI AVIRAM/Middle East Images/AFP via Getty Images
A ina za a yi zaman?
Yayin da ake jita-jitar wurare kamar Roma da Hungary da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a matsayin wajen yin taron, zaɓin ƙarshe ya fi kusa da gida ga shugaban Amurka.
A yammacin Juma'a, Trump ya wallafa a manhajarsa ta sada zumunta Truth Social cewa "muhimmin taron da ake dako" tsakaninsa da Putin zai gudana ne a ranar 15 ga Agustan a "jihar Alaska".
Ya kuma ce "ƙarin bayani na nan tafe."
Trump ya ce wurin taron "zai kasance sananne saboda dalilai da dama."
Har yanzu dai ba a ayyana takamaimen wurin da taron zai gudana ba a Alaska.
Ko Ukraine za ta halarci taron?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babu alama sai dai rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Amurka na cewa ana iya gudanar da wani taron tare da Trump da Putin da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, idan wannan ya yi nasara.
Zuwa yanzu dai, babu haske kan wani da zai halarci taron ban da Putin da Trump.
An shafe watanni, Zelensky na roƙon Amurka ta bai wa Turai dama a zaman tattaunawar, yana fatan za su samar da wata dabara mai tsauri ga Moscow.
"Yaƙin a Turai yake, kuma Ukraine muhimmiyar ɓangare ce a Turai, kuma tuni muka shiga tattaunawa kan yadda za mu shiga Tarayyar Turai," in ji Zelesnky. "A don haka, dole a dama da Turai a tattaunawar."
A wannan makon, Trump da Zelensky sun kasance suna tuntuɓar juna da kuma ƙawayensu na Turai.
Bayan da jakadan Amurka na musaman ya gana da Putin a Rasha, Trump ya yi magana da shugabannin Turai inda ya sanar da su ƙuririnsa na ganawa da Putin domin tattauna yiwuwar cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Zelensky ya ce ya yi tattaunawa mai ma'ana da Trump a ranar Talata inda ya shaida wa shugaban cewa Rasha na ƙara zafafa "munanan hare-harenta."
Shugaban Ukraine a baya ma ya bayyana cewa ba zai amince da duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta da Kremlin ba, idan ba a ji daga Ukraine.
Zuwa yanzu dai Ukraine ba ta fito ta yi martani game da labarin ganawarda ke tafe ba.

Asalin hoton, EPA
Me ƙawayen Ukraine ke cewa?
Ƙawayen Ukraine a Turai sun dage cewa duk wata tattaunawar zaman lafiya da Rasha dole ta kasance da Kyiv.
Iƙirarin nasu na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa daga shugabannin Birtaniya da Faransa da Italiya da Jamus da Poland da Finald da Hukumar Tarayyar Turai.
Wata jami'ar Fadar White House ta ce Trump a shirye yake ya gana da shugabannin biyu har da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky amma uwa yanzu, taron ya ƙunshi Trump da Putin, kamar yadda shugaban Rasha tun farko ya nema.
Zelensky ya ce duk wata yarjejeniya da ba a sanya Ukraine ciki ba, na nufin "matakan da ba su da amfani".
A baya Trump ya bayar da shawarar cewa yana iya ganawa da Putin shi kaɗai, inda ya shaida wa ƴanjarida cewa yana da ƙudirin "farawa da Rasha."
Sai dai shugaban Amurka ya kuma ce yana ganin "muna da damar" shirya taron mutum uku tare da Putin da Zelensky.
To ko dai Putin zai amince da wannan, abu ne da bai fito fili ba - ya yi watsi da damarmaki na ganawar gaba da gaba kuma shugabannin biyu ba su gana ido da ido ba tun bayan da Putin ya ƙaddamar da yaƙin mamaye Ukraine tsawon fiye da shekara uku.
Wane tagomashi ɓangarorin biyu ke fatan samu daga taron?
Ƙudirin Trump a bayyane yake: kawo ƙarshen yaƙin, ɗaya daga cikin alƙawuran zaɓe da ya ɗauka.
"Zan yi duk mai yiwuwa don dakatar da yaƙin," in ji Trump a wannan makon.
Shugaban Amurka ya yi iƙirari a ranar Juma'a cewa "an kusa cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu."
Yayin da ƙasashen biyu ke cewa, suma suna son a kawo ƙarshen yaƙin, Ukraine da Rasha da alama na son abin da ɗaya ɓangaren ke adawa da shi.
Ukraine ta kafe cewa ba za ta amince da burin Rasha na ci gaba da iko da yankunan da ta ƙwace, musamman Crimea.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi watsi da batun kai tsaye. "Babu abin tattaunawa a nan. Wannan ya saɓawa kundin tsarin mulkinmu," in ji shi.
Zuwa yanzu, Putin dai bai sauya buƙatarsa ta neman ƙwace yankunan Ukraine ba da batun rashin ɗaukan ɓangare na Ukraine da kuma makomar yawan sojinta.
Ya yi wa ƙasar ƙawanya, a wani ɓangare, saboda tunaninsa cewa Ukraine na son zama wani ɓangare na Turai inda kuma ya zargi ƙungiyar tsaro ta Nato ta ƙasashen yama, da yin amfani da ƙasar wajen girke sojojinta kusa da iyakokin Rasha.
Fadar White House ta ce tana ƙoƙarin farantawa duka ɓangarorin biyu da wani shiri mai yiwuwa.
Gwamnatin Trump ta daɗe tana ƙoƙarin janyo ra'ayin shugabannin Turai ga batun yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta sa a miƙa yankunan Ukraine zuwa ga Rasha, kamar yadda rahotanni daga CBS News suka bayyana.
Yarjejeniyar za ta bai wa Rasha damar ci gaba da riƙe iko da Crimea tare da ƙwace yankin Donbas na gabashin Ukraine, wanda ya ƙunshi Donetsk da Luhansk, a cewar majiyoyi da suka san da tattaunawar.
Rasha ta mamaye Crimea ba bisa doka ba a 2014 kuma sojojinta sune riƙe da akasarin yankin Donbas.
Aƙarƙashin yarjejeniyar, sole Rasha ta miƙa yankunan Ukraine na Kherson da Zaporizhzhia, inda a nan sojojinta ke da iko.
"Za a yi musayar yankuna domin amfanin duka ƙasashen amma za mu tattauna kan haka ko dai anjima ko kuma gobe," kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai a Fadar White House a ranar Juma'a.

Asalin hoton, Justin Sullivan/Getty Images
Mene ne dalilin yin taron a Alaska?
Akwai dalilai da dama.
Yanki ne a Amurka, wanda yake da sauƙin matsalar tsaro.
Garin kuma na nuna cewa Trump ne mai masaukin baƙi ga takwaransa na Rasha a filin da Amurka ta siya daga hannun Rasha fiye da ƙarni guda da rabi da ya gabata.
Mai taimaka wa shugaban Rasha Yuri Ishakov ya ce akwai "ma'ana" a zaɓar wurin kuma ya nanata cewa duka ƙasashen biyu maƙwabtan juna ne, inda mashigar Bering ta raba tsakaninsu.
"Rasha da Amurka maƙwabtan juna ne, sun haɗa iyakoki," in ji shi, "Da alama akwai ma'ana ga wakilanmu su je mashigar Bering kuma don irin wannan muhimmin taro da aka daɗe ana jira na shugabannin ƙasashen biyu da za a yi a Alaska."
Lokaci na ƙarshe da aka yi wani taro a Alaska shi ne a Maris ɗin 2021 inda aka yi wani taron diflomasiyya na Amurka, lokacin da tawagar tsaro da diflomasiyya ta shugaban ƙasa a lokacin Joe Biden ta gana da takwarorinta na China a Anchorage.
Zaman da aka yi da China ya yi tsami inda ƴan Chinan suka zargin Amurkawa da "munafunci".
Zaɓin Alaska na da muhimmanci saboda dalilai na daban, in ji masu sa ido.
Amurka ba ta sa hannu ba - kuma ba ta amince da hurumin da kotun duniya ta ICC ke da shi ba wadda ta bayar da umarnin kama Putin. Tun da Alaska yanki ne a Amurka, babu barazanar cewa za a kama shi idan ya ziyarci wajen domin tattaunawa.r.
Ya batun ganawar gaba da gaba da aka yi a baya?
Trump da Putin sun tattaunawa ta waya a Fabarairu a ganawar ƙeƙe da ƙeke ta farko tsakanin shugabannin tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a 2022.
Daga nan kuma, bayan kiran wayar, Trump ya sanar cewa za a yi tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka, wadda ba ta haɗa da Ukraine ba.
Duka shugabannin sun amince su ziyarci juna a ƙasashensu.
Lokaci na karshe da wani shugaban Amurka ya gana da Putin shi ne a 2021 - gabanin mamayar Rasha a Ukraine - lokacin da Biden ya gana da shugaban Rasha a wani taro da ke Geneva a Switzerland.











