Firaministan Birtaniya ya yi watsi da barazanar Putin kan ba wa Ukraine manyan makamai

Firaministan Birtaniya tare da 'yanjarida a jirgin sama
Lokacin karatu: Minti 3

Firaministan Birtaniya ya sa kafa ya shure tsattsauran gargadin da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wa gwamnatocin yammacin duniya, a kan bai wa Ukraine dama ta yi amfani da makamai masu linzami da ke cin dogon zango da suka ba ta zuwa cikin Rashar.

Keir Starmer ya ce Rasha ce ta fara yakin ta hanyar mamayar makwabciyarta, a don haka Ukraine din tana da ‘yancin da za ta kare kanta.

Firaministan na Birtaniya ya yi watsi da gargadin da Mista Putin ya yi ne a kan barin Ukraine ta yi amfani da manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zango, wadanda kasashen kungiyar kawance ta tsaro ta Nato ke bai wa Ukraine, a wuraren da za ta hara can cikin ainahin Rashar, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Amurka.

Mista Starmer ya ce, koma mene ne, Rasha ce ta faro yakin inda haka siddan ta mamayi makwabciyar tata, a don haka Ukraine tana da dama da ‘yancin da za ta kare kanta, sannan ita Rashar idan ta ga dama za ta iya dakatar da yakin.

Sai dai ya kara da cewa kalaman nasa ba wai suna nufin, yana neman rikici ba ne da Rashar.

Ana sa ran Firaministan na Birtaniya zai tattauna wannan magana da mai masaukin nasa, Shugaba Biden a fadar gwamnatin Amurkar, White House a ranar Juma’a.

Tun da farko Shugaba Putin ya ce, barin Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami na kasashen yamma, da ke cin dogon zango zuwa cikin kasarsa, zai sauya ainahin yanayin yakin.

Firaministan da sauran shugabannin kasashen yammacin duniya suna kaffa-kaffa a kalamansu a kan sauya manufa a kan amfani da makamai masu linzami da ke cin dogon zango, to amma karakainar diflomasiyya da ake ta yi a kan batun don cimma matsaya a kan batun a fili take.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A kan batun ne ma sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy da takwaransa na Amurka, Anthony Blinken suka kasance a Kyiv, a makon nan.

A ranar Lahadi Firaministan na Birtaniya zai nufi, birnin Rum – kasancewar Italiya ce ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar manyan kasashe masu masana’antu, ta G7.

Bugu da kari shugabannin duniya za su hadu a babban taron majalisar dinkin duniya a New York, mako daya bayan nan.

Firaministan ya ce, lalle-lalle akwai muhimman abubuwa da za su iya faruwa a ‘yan makonnin da ke tafe, da watanni, saboda haka akwai bukatar a dauki muhimman matakai, ko matsaya.

Zuwa yanzu dai lissafin da shugabanni a Amurka da saurn kasashen yamma ke yi shi ne – shin barazana ce kawai Shugaba Putin yake yi ko kuma da gaske ne zai mayar da martani a zahiri?

Masu goyon bayan a bai wa Ukraine damar amfani da manayan makaman masu linzami a kan Rashar, na ganin cewa ai duk barazana ce kawai – kasancewar duk kumajin da ya rika yi a baya idan an yi wani abu, ba wanda ya mayar da martani na zahiri.