Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa albasa ta yi tsadar gaske a Najeriya
- Marubuci, Abubakar Maccido
- Aiko rahoto daga, Kano
- Lokacin karatu: Minti 3
Albasa na daga cikin kayan miyar da aka fi amfani da su a kodayaushe.
Ana fuskantar tsananin tsadar albasa a wannan shekara ta 2024, farashin ya yi tashin da ba a taɓa ganin irinsa ba a baya-bayan nan.
Wannan ya sanya mutane da dama na mamakin ko mene ne ya haifar da hakan, kuma yaushe ne albasar za ta yi sauƙi?
BBC ta gano cewa a wasu yankunan na Najeriya ana sayar da buhun albasa kan kuɗin da ya kai naira 200,000 zuwa 200,000.
Amma a cikin ƴan watannin da suka gabata, ana sayar da irin wannan buhu a kan kuɗi naira 30,000 zuwa 40,000.
Me ya sa farashin ya tashi a wannan shekara?
Manoma da dama sun shaida wa BBC cewa babban dalilin da ya sa albasa ta yi tsada shi ne ambaliyar ruwa da aka samu a wurare da dama a daminar da ta gabata.
Ɗaya daga cikin manoman ya shaida wa BBC cewa ambaliyar ta lalata irin albasar da ya tara.
Sa'adu Gata, wani ɗan kasuwa mai sayar da kayan lambu ya ce mamakon ruwa da aka riƙa samu a lokacin damina shi ne abin da ya haifar da matsalar.
"A wannan shekarar an samu ruwan sama sosai, kuma hakan ya lalata irin albasa."
Ya ƙara da cewa "Bukukuwan kirsimeti da ke matsowa kuma sun ƙara ta'azzara matsalar, to amma ruwan da aka samu shi ne maƙasudi. Hakan ya sa muna sayen (buhun) albasa a yanzu kan kudi naira 220,000 zuwa 230,000 a Kano, dangane da kyawun albasar."
A wasu biranen da ke kudancin Najeriya kamar Port Harcourt, babban buhun albasa ya kai naira 270,000 yayin da ake sayar da ƙaramin buhu a kan naira 160,000 zuwa 170,000.
Wannan ya sa yanzu farashin kashin albasa mai ƙwara huɗu ke kaiwa naira 1,000, babban kashi kuma naira 2,000.
Shi kuwa Aliyu, wanda babban mai kasuwancin albasa ne a jihar Sokoto ya ce wannan ne karo na farko da suka ga albasa ta yi mummunar tsada irin haka.
"Wannan ne karon farko da ake sayar da buhu ɗaya na albasa kan naira 220,000 a Sokoto, kuma hakan ya faru ne sanadiyyar mamakon ruwa da ya lalata irin albasa a daminar da ta gabata.
"Haka nan ma ƙaratowar kirsimeti na daga cikin abubuwan da suka ƙara tsadar albasar," in ji shi.
A jihar Legas, farashin buhu ɗaya na albasa ya kai naira 300,000. Kuma hakan ya faru ne saboda tsadar sufuri daga inda ake kawo albasar zuwa Legas.
Wata ƴar kasuwa a kasuwar Mile 12 da ke Legas ta ce suna sayen albasa ne daga masu kawo ta daga arewacin Najeriya, kuma sai suna sanya kuɗin sufuri cikin kudin da suke sayar da albasar.
Sai dai Ƙungiyar manoma ta Najeriya ta ce duk da cewa mamakon ruwa da aka samu a daminar da ta gabata ya taimaka wajen haifar da tsadar albasa a Najeriya, amma sun yi amannar cewa fitar da albasar da ake yi zuwa ƙasashen waje ya bayar da gudumawa wajen tashin farashin.
Yunusa Halidu, wanda shi ne sakataren ƙungiyar na ƙasa ya ce bincikensu ya nuna cewa abubuwa biyu - mamakon ruwan sama da kuma yawan buƙatar albasar - su ne suka haddasa tsadar.
"Ana buƙatarta da yawa saboda komai mutane za su dafa sai sun yi amfani da albasa."
Ya ƙara da cewa "haka nan kuma ruwan sama mai yawa da aka samu a lokacin damina ya lalata irin albasa da mutane suka ajiye a gonaki, wannan ya sa albasa ta yi wahalar samu, shi ya sa ta yi tsada."
Halidu ya ce a Sokoto an buɗe wata kasuwar da ake saya tare da fitar da albasa zuwa ƙasashen waje, "mutane na fityar da albasar zuwa wasu ƙasashe, kuma mun gano cewa wannan na daga cikin dalilan da suka sa albasa ta yi tsada."
Ya kuma bayyana tsadar taki da tsadar ƙwadago da ma wasu abubuwan da dama waɗanda ya ce a yanzu duk suna taimakawa wajen sanya tsadar amfanin gona.
Aliyu ya ce akwai sa ran farashin albasa zai sauka bayan bikin kirsimeti da na ƙarshen shekara, "Ina ganin farashin zai fara sauka ne a cikin watan Fabarairun 2025 domin a ya zuwa wannan lokacin manoma sun fara fito da albasar daga gona."