Yadda matashi ya sare bishiya mafi shahara a duniya

Ian Sproat wanda ya dauki hoton bishiyar ya bayyana takaicinsa bayan an sare ta.

Asalin hoton, Ian Sproat

Bayanan hoto, Ian Sproat wanda ya dauki hoton bishiyar ya bayyana takaicinsa bayan an sare ta.
    • Marubuci, By Andrew Webb
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Bishiyar da mutane suke yi wa laƙabi da ''Itacen tarihi'', za ta iya sake tsirowa bayan an sare ta ba bisa ka'ida ba.

Ta samu kusan shekaru 300 a Sycamore Gap, wani yanki na tsohuwar katangar Hadrian ta Romawa da ke Arewacin Ingila.

A shekara ta 2016, aka raɗa mata suna (Bishiyar shekara) yayin wata gasa da gidauniyar Woodlanad Trust ta kasar Burtaniya ta shirya.

Jami'ai sun bayyana cewar da gangan aka sare bishiyar da zarto.

Hoton bishiyar ta Sycamore Gap bayan an sare ta, ga jami'an ƴan sanda uku a kusa da ita

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yan sanda sun kama wani saurayi da ake zargi da hannu a sare bishiyar mai tsohon tarihi

Jijiyar bishiyar Sycamore za ta sake tsirowa

Masu kare dazuka sun yi hasashen kututturen bishiyar zai sake yin tsiro.

Wata Gidauniyar Kula da Tsirrai a Burtaniya ta ɗauki aniyar sanya ido don kare kututturen har ya zuwa lokacin da zai sake fitowa.

Wani ƙwararren mai ɗaukar hoto, Ian Sproat ya taɓa ɗaukar bishiyar hoto a lokacin maraice, daga nan ya ci gaba da yi mata hotuna a lokacin damina da bazara.

Ya shaida wa BBC cewar:

''Bishiyoyin Sycamore su na da juriya, tana iya sake tsirowa amma akwai buƙatar a kula da ita.''

"Abin da ya ƙara mata kyau shi ne yadda ta tsaya a tsakiyar duwatsu tare da fuskantar sararain saman Tekun Arewa yayin da hasken Tekun ya ƙara bayyana ta, yanayin da duk mai ɗaukar hoto zai so.''

Hoton farko da Ian Sproat ya 'dauki bishiyar

Asalin hoton, Ian Sproat

Bayanan hoto, Hoton farko da Ian Sproat ya 'dauki bishiyar

Mista Sproat ya bayyana yadda ya ji da samun labarin sare bishiyar:

"Da farko labarin ya fusata ni ƙwarai, amma da na je na gani sai takaici ya mamaye ni, wannan wuri ne da mutane ke zuwa don idan su na neman kwanciyar hankali, wani wuri ne na tsere wa tashin hankali da damuwar duniya, yanzu wannan ta wuce.''

Hoton bishiyar a lokacin da faɗuwar rana

Asalin hoton, Tom Wright

Bayanan hoto, Masu 'daukar hoto daga 'kasashen duniya sun kai ziyara don gani da ido.

Jami'an Tsaro sun kama wani matashi

Ƴan sanda sun kama wani matashi mai shekara 16 sakamakon zargin sa da aikata ɓarna da gan-gan.

Hoton bishiyar da tsakar rana gabanin a sare ta

Asalin hoton, Mark Beadle

Bayanan hoto, Kevin Bainbridge, ya yi wa matarsa wasiyyar idan ya mutu a barba'da tokar gawarsa a 'kar'kashin bishiyar.

Bishiyar Robin Hood

Ta fito a fina-finan Hollywood da dama, wurin da bishiyar take ya na da muhimmanci a Arewa maso Gabashin Ingila.

Ɗaya ce daga cikin abubuwan da aka fi ɗaukar hoto a Birtaniya, an fi sanin ta da bishiyar Robin Hood bayan ta fito a fim ɗin Robin Hood Prince of Thieves wanda aka haska a shekara ta 1991, taurarin fim ɗin sun haɗa da Kevin Costner da kuma Alan Rickman.

Sycamore Gap tree at night with the stars and Northern lights in the background

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ta kasance alamar komai-nisan dare-gari-zai-waye, la'akari da yadda take girma a lokacin hunturu.

Rashin Hankali

Dan Newman jarumin fin 'din da Kevin Costner ya shirya, ya yi amfani da bishiyar wajen 'buya kafin a ceto shi.

"Aiki na na farko a fim 'din kenan,"

"Hoto ne mai kyau da ma'ana, ko ba haka ba?

Picture of the tree at sunset from a distance

Asalin hoton, Tom Wright

Bayanan hoto, Jama'a su kan zauna su dinga kallon bishiyar har tsawon sa'o'i.

Jarumi Dan Newman wanda ya koma aikin horas da masu motsa jiki ya kara da cewar:

''Jama'a daga kusa da nesa na ci gaba bayyana ra'ayoyinsu game da sare bishiyar, rashin hankali ne sare wannan bishiya''.

Sycamore gap tree on Hadrian's Wall in winter

Asalin hoton, Francesca Williams

Bayanan hoto, Komai tsananin hunturu ba ta kaɗewa

Ian Sproat ya faɗa kan wata bishiya da ke maƙwaftaka da ita inda dangin mamata suke watsa tokar gawarwakin makusantan su bayan an 'kone su.

"Wannan abu ya tayar da hankulan dangin wadanda aka watsa tokar su a gurin."

Sycamore Gap tree felled

Asalin hoton, IAN SPROAT

Bayanan hoto, Catherine Cape 'daya daga cikin wadanda suke ziyarar bishirar a lokutan zaman gida saboda annobar korona

'Wasiyyar inda za a watsa toka'

Mazauna yankin da bishiyar ta ke, irin su Kevin Bainbridge wanda ya nemi auren matarsa a 'karkashin bishiyar ya ce:

"Idan wani abu ya faru da mu, a zuba tokarmu a nan.''

"Ka na ganin za ta jima tsawon lokaci saboda nan gurin tarihi ne.

Sycamore Gap tree felled

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Yan sanda sun sanya shinge a inda bishiyar ta fadi yayin da ake gudanar da bincike

Ian Sproat ya bayyana yanayin da mutane suka shiga kamar haka:

''Ta na da wata daraja ta musamman banda kasancewar ta bishiya."

A rose with police tape next to the tree

Asalin hoton, PA Media