Matar da ake zargi mijinta ya azabtar da ita a Yobe ta rasu

Bayan mako guda da yada hotunan wata mata cikin yanayi na rama a kafafan sada zumunta, inda ake zargin cewa mijinta ne ya tsare ta a gida ba tare da kyakkyawar kulawa ba, matar ta mutu.
Matar, mai suna Sadiya Salihu, wadda ‘yar asalin jihar Kano ce a Najeriya, ta yi aure ne ajihar Yobe.
A yanzu iyaye da dangin matar na zaman makoki bayan rasuwarta sakamakon bakar azabar da ta sha a lokacin da take tsare.
Daya daga cikin ‘yan uwan matar Aisha Salihu, ta shaida wa BBC cewa bayan sun dauko ‘yar uwar tasu daga Yobe sun dawo ita gida Kano don yi mata magani, sun kai ta asibiti amma duk wani gwajin cuta da aka yi mata ya nuna ba ta dauke da kowanne ciwo.
Ta ce likitoci sun shaida musu cewa akwai yunwa a tare da ita da kuma matsananciyar damuwa.
Aisha Salihu ta ce “Ko da aka dawo da ita gida aka kai ta asibiti sai da ta shafe kwana hudu ba ta yi magana ba, amma a kwana biyar ta yi magana bayan na tambaye ta ya jiki ta ce da sauki.”
‘Yar uwar marigayiyar ta ce muryarta ba ta fita sosai lokacin da ta yi maganar, don haka babu wanda ya samu damar tambayarta abin da ya sanya ta cikin wannan hali har ta mutu.
Ta ce, “ A gaskiya ba bu wanda ya sanya abin da ya jefa ta cikin wannan hali, amma ‘ya’yanta da aka taho da su gida daga can Yoben, sun ce mahaifin nasu wato miji marigayiyar ke nan baya bata abinci, sai dai ya bata kunu da ruwa rabin Kofi da kuma Hasbiya da ake gasa mata a kullum.”
Sannan sun ce yana mata wanka da ruwa mai wari da kuma yi mata turaren hayaki da barkwano, in ji ta.
Aisha Salihu, ta ce koda aka je taho da marigayiyar mijin nata ya bayar da wani sassaken magani inda ya ce a rinka yi mata wanka da shi don ciwonta bana asibiti bane.
Ta ce dama koda ‘yar uwarta ta ke da cikakkiyar lafiya ma, mijin nata baya barinta yin mu’amala da sauran mutane.
Bayanai dai sun nuna cewa rundunar 'yan sandan jihar ta Yobe ta kama mutumin da ake zargi tun a makon jiya, kuma nan bada jimawa ba za a kai shi Kano.










