Matar da tsananin yunwa ya sa ta kasa binne ‘yarta da ta mutu

.

Kananan yara da yawa na ta mutuwa a Somaliya a sanadiyyar fari mafi tsanani wanda kasar ba ta taba gani ba a cikin shekara 40.

Jami’an gwamnati sun ce bala’in da ya fi wanda ake gani ma zai iya samun kasar cikin ‘yan kwanaki ko makonni muddin ba ta samu taimakon gaggawa ba.

Habiba Mohamud
Bayanan hoto, Habiba Mohamud ta ce ba za a iya gane kauyensu ba

Jami’an gwamnati sun ce bala’in da ya fi wanda ake gani ma zai iya samun kasar cikin ‘yan kwanaki ko makonni muddin ba ta samu taimakon gaggawa ba.

Kananan yara da yawa na ta mutuwa a Somaliya a sanadiyyar fari mafi tsanani wanda kasar ba ta taba gani ba a cikin shekara 40.

Jami’an gwamnati sun ce bala’in da ya fi wanda ake gani ma zai iya samun kasar cikin ‘yan kwanaki ko makonni muddin ba ta samu taimakon gaggawa ba.

Wannan dai fari ne da sauyin yanayi yake ta haddasawa cikin gaggawa, abin da ke kawo karshen al’ada ta makiyaya a kuryar gabashin Afirka.

Wani sabon bincike da aka gudanar yan una lkusan kashi biyu bisa uku na kananan yara da mata masu juna-biyu a sansanin ‘yan gudun hijirar na Baidoa na fama da tsansanin tamowa ko yunwa, wanda wannan ken una bala’in yunwa da kasar ke fama da shi.

 Wata mata mai suna Fatuma ta bayyana wa BBC yadda tana ji tana gani ‘yarta ta mutu ta tafi ta barta ba tare da ta binne ta ba, yayin da kuraye kuma ke tunkaro inda suke.

 "Ina ji ina gani ‘yata Farhir mai shekara uku ta rasu a gabana, ban iya yi mata komai ba,’’ in ji Fatuma wadda ta shafe kwana 15 tana tafiya a kasa tare da ‘ya’yanta tara daga kauyensu da ake kira Buulo zuwa Baidoa.

 Ta ce "Tsawon kwana 10 ina dauke da ita. Dole ne mu tafi mu barta a gefen hanya. Ba mu da ko karfin da za mu iya binne ta. Kuma muna jin kukan kuraye daga nesa suna matsowa."

"Ba ni da komai. Ba abin da ya rage mana a gida. Shanun duka sun mutu. Gonaki sun bushe,’’ in ji wata matar mai suna Habiba Mohamud, mai shekara 50, wadda ta ce ba za ta sake komawa kauyensu ba.

Kamar dai sauran sabbin isa wannan sansani, Habiba taba rike da ‘yan karerayi da sauran abubuwa tana ta faman yadda za ta yi wa ita da ‘ya’yanta ‘yar bukkar da za kasance dakinsu a wannan sansani kafin sanyin dare ya kunno kai.

 Sai ta gama wannan ne sannan kuma ta shiga neman abinci daga bisani kuma ta fada neman lafiya ga sauran ‘ya’yanta biyar.

 Can a dakin da ake kwantar da marassa lafiya na babban asibitin birnin Dakta Abdullahi Yussuf na kewayawa yana duba marassa lafiyarsa wadanda yawancinsu yara ne ‘yan shekara biyu zuwa uku wadanda yunwa ta yi tsananin kama su.

Wasu sun kamu da cutar sanyin hakarkari ta numonia (pneumonia), wasu ma kuma har da kyanda.

Yara ‘yan kalilan ne suke iya kuka domin wasaunsu bas u da hatta karfin da za su iya kukan.

Da yawa daga cikinsu duk fatarsu ta tamushe ta baci.

"Da dama daga cikinsu suna mutuwa kafin ma siu iso asibiti, in ji likita Abdullahi wanda yake duba ma’aikatansa na kokarin kara wa wani yaro dan shekara biyu ruwa.

Ana auna nauyin wani yaro
Bayanan hoto, Mata da yara na barin yankunan da ba za su samu taimako ba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ko da yake akwai bambancin alkaluma, amma yawan al'ummar Baidoa ya ninka kusan hudu a 'yan watannin da suka gabata zuwa kusan 800,000.

Amma duk wanda ya ziyarci garin zai ga cewa kusan dukkanin sabbin zuwa garin mata ne.

Somalia ta fada cikin yanayi na halin-kaka-ni-ka-yi, tun bayan da gwamnatin kasar ta fadi shekara 30 da ta gabata.

Wannan ya shafi kusan dukkanin bangarorin kasar, abin da ke raba maza magidanta da iyalansu domin su je su yi yaki a wata kungiya.

kamar dai yawancin wadanda ke isa Baidoa, a kwanan ne Hadija Abukar ta samu tsira daga yankin da kungiyar masu ikirarin jihadi ta al-Shabab ke iko da shi.

Ta ce "Har yanzu 'yan uwana na kirana ta waya. Suan gaya min cewa ana fada tsakanin 'yan al-Shabab da sojojin gwamnati.

Dangina duk sun gudu suna boye a daji, ta yi wa BBC bayani tana zaune kusa da dan karamin danta maras lafiya a asibitin Baidoa.

Haka wasu mmatan ke bayar da suma irin labaransu, inda suke bayyana cewa an hana mazajensu da manyan 'ya'yansu ficewa daga kauyukansu inda kungiyoyin 'yan bindiga ke rike da iko da su.

Da kuma yadda kungiyoyin ke tilasta musu bayar da kudi da sauran abubuwa tsawon shekaru.

Kiyasi na nuna cewa sama da rabin yawan mutanen da fari ya fada wa a yanzu suna yankunan da ke karkashin ikon al-Shabab.

Kuma tsauraran dokokin Amurka da suka hana yankuna da kungiyoyin 'yan ta'adda suke sun kara tsananta al'amarin.

To amma hukumomi na aiki da hadin kan wasu kungiyoyi na yankuna domin kokarin jefa kayan taimako ga jama'a ta sama.

Sai dai duk da haka wani jami'i da bai yarda a ambata sunansa ba ya ce wannan ma ba lalle ba ne ya hana mayakan kungiyar samun kayan ba.

Baidoa

Asalin hoton, BBC/ ED HABERSHON

Bayanan hoto, Birnin Baidoa ya zama tudun-mun-tsira ga 'yan gudun hijira

Hatta a Baidoa wanda birni ne mai hada-hada, wanda ake iya ganin alamun rikici na shekara da shekaru, da rashin kulawa, farashin kayan masarufi kusan ya ninka biyu a watan da ya gabata.

Yayin da sabuwar gwamnatin Somaliya ke fama da rikicin al-Shabab sai kuma ga wannan bala'i na fari.

To amma duk da haka, gwamnatin na da kwarin guiwa na fuskantar wadannan matsaloli, ta hanyar samun tallafi daga waje da al'ummarta da ke cike da buri da kuma tarin 'yan kasar da ke sassan duniya.