‘Ɗana ya dinga kumbura saboda yunwar da ake fama da ita a Somaliya’

Bayanan bidiyo, ‘Ɗana ya dinga kumbura saboda yunwar da ake fama da ita a Somaliya’
‘Ɗana ya dinga kumbura saboda yunwar da ake fama da ita a Somaliya’

A yayin da fari ke ƙara muni kuma farashin kayan abinci ke tashin gwauron zabi a duniya, Majalisar Dinkin Duniya MDD, ta yi gargadin cewa za a fuskanci mummunar yunwa a wasu sassan Somaliya daga watan Oktoba zuwa Disamba.

Shugaban hukumar agaji ta MDD Martin Griffiths ya ce akwai alamun cewa za a yi fama da yunwa a wannan lokacin a yankuna biyu na Somaliya – gundumomin Baidoa da Burhakaba.

BBC ta zanta da wasu da tuni suka fara jin jiki sakamakon yunwar da suke fama da it a Baidao.