Waiwaye: Kafa rundunar tsaron jihar Kano da musayar kalaman El-Rufai da APC

Lokacin karatu: Minti 3

Wannan maƙala ce da ke kawo muku bitar muhimman labaran da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Na faɗa wa Tinubu ba na sha'awar muƙami a gwamnatinsa - El Rufa'i

Mallam Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Others

A cikin makon da muke bankwanan da shi ne tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya ce ya faɗa wa shugaba Bola Tinubu cewa ba ya son wani muƙami a gwamnatinsa.

El Rufa'i ya bayyana haka ne a shafinsa na X, yayin martani ga babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan sadarwar tsare-tsaren gwamnati, Daniel Bwala, wanda ya ce El Rufa'i ya ji tsoron Allah bayan da ya fito fili ya caccaki jam'iyyar APC da kuma kiran ta mai mulkin da ta "sauka daga aƙidun dimkoraɗiyya da aka kafa ta a kai".

"Na faɗa wa Tinubu ƙarara cewa ba na buƙatar kowane irin muƙami a gwamnatinsa," in ji El Rufa'i.

Gwamnatin Kano za ta kafa rundunar tsaron jihar

Gwamnan jihar Kano

Asalin hoton, Kano State Govt

A farkon makon da muke bankwanan ne kuma majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da yi wa ƙudurin kafa rundunar tsaro - da gwamnatin jihar ta aike mata karatu na biyu.

Kano dai na fama da matsaloli irin na rikice-rikicen dabanci da ƙwacen waya, lamarin da ya yi sanadiyar ajalin mutane da dama.

Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙiru, Abubakar Tasi'u Ƙiru, na cikin ƴan majalisar da suke goyon bayan ƙudurin, inda ya lissafa wasu abubuwan da ke ƙunshe a cikin ƙudurin.

NLC za ta yi zanga-zanga don adawa da ƙarin kuɗin kiran waya

Shugabannin NLC

Asalin hoton, NLC

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Talata 4 ga watan Febrairun 2025, domin adawa da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 wanda Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da shi.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta hannun shugabanta Joe Ajaero, ya ce sun ɗauki matakin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba.

NLC ta ce zanga-zangar za ta zama gargaɗi ga hukumomi kan yunkurin ƙaƙaba wa mutane ƙarin kuɗin kiran waya a ƙasa kuma da albashi mafi ƙanƙanta bai wuce naira 70,000 ba, ga kuma ƙarin farashin mai da na abinci da lantarki da kuma ƙaruwar hauhawarar farashi.

Ƙungiyar ta buƙaci rassanta na jihohi da su fara shirya mambobinsu domin shiga zanga-zangar ta ƙasa baki-ɗaya, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da su ma su fito.

A farkon watan Janairun wannan shekarar ne hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa na ƙasar su ƙara kudin kiran waya da kashi 50 cikin 100.

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Max Air

Jirgin Max

Asalin hoton, Max Air/X

A tsakiyar makon ne kuma gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da ayyukan kamfanin jirgin sama na Max Air, bayan jirgin kamfanin ya yi hatsari a ranar Talata a jihar Kano.

Daraktan hulɗa da jama'a da kare haƙƙin abokan hulɗa na hukumar kula da sufurin jragen sama ta ƙasar (NCAA), Michael Achimugu ne ya bayyana matakin cikin wata sanarwa da ya fitar.

Achimugu ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne, domin bai wa hukumomin kamfanin damar tattance ayyukansa kama daga kan kamfanin da ma'aikatansa da tsarin aikinsa da jiragensa zuwa tattalin arziƙi ko ƙarfin jarin kamfanin.

Hukumar Hisbah ta kuɓutar da ƴan mata da aka yi yunƙurin safararsu

Aminu Daurawa

A farkon makon ne kuma hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin ƙasar ta sanar da kuɓutar da wasu 'yan mata 15 waɗanda aka yi yunƙurin safararsu zuwa ƙasashen waje.

Hukumar ta ce an gano yaran ne waɗanda dukkansu ƴan mata ne a tashar mota a cikin birnin Kano.

Hukumar ta HISBA ta ce ta samu wannan nasarar ce yayin wani samame da jami'anta suka kai wata tashar mota.