Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku gane yaron da ke fama da ciwon hakin wuya
- Marubuci, Habiba Adamu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 2
Ciwon hakkin wuya cuta ce da aka fi gani tsakanin yara ƙanana, a cewar hukumar lafiya ta Burtaniya.
Wasu ƙwayoyin cuta da suka haɗa da virus da bacteria ne ke janyo ciwon a maƙogwaro.
Ciwon hakin wuya wanda ake kira 'Tonsillitis' da ƙwayar cutar virus ta haddasa kan zo da sauƙi a kan wadda ƙwayar cutar 'bacteria' ke haddasawa, in ji likitoci.
Idan ciwon hakin wuya ya yi tsanani yana taɓa ƙoda da ƙwaƙwalwa, yakan kai ga asarar rai.
Sai dai baya ga yara akan samu matasa ƴan sama da shekara 10 da kan kamu da shi, kuma manyan mutane ma sukan yi fama da shi.
Hukumar lafiya ta Birtaniya (NHS) ta ce cutar ba mai yaduwa ba ce, amma mafiya yawan kwayoyin cutar da ke haddasa cutar, suna yaduwa, inda ta bayar da misali da mura.
A cewar hukumar alamomin ciwon kan tafi bayan kwana 3 zuwa 4, yayin da a wasu lokutan sukan dauki dogon lokaci.
Alamomin hakin wuya
Wasu daga cikin alomomin cutar sun haɗa da:
- Zafin maƙogwaro
- Kasa haɗiyar abinci ko shan ruwa
- Warin baki
- Kumburin hakkin wuya a cikin maƙogwaro
- Ciwon kai
- Zazzaɓi
- Gajiya
Wata ƙwararriyar likitar yara da ke aiki a Najeriya, Dokta Aisha Musa Zaidu ta ce yana da muhimmanci idan an ga waɗannan alamomi a je asibiti domin tabbatar da cewa ciwon hakkin wuya ne ke damun yaro.
Inda ta ƙara da cewa kula da tsaftar jiki, musamman ma na baki da na muhalli na daga cikin muhimman matakan kare yara daga kamuwa da cutar.
Latsa makunnin da ke sama domin samun ƙarin bayani a cikin shirin Lafiya Zinariya.
Tsanani da sauƙin cutar
Haka kuma hakkin wuya kan yi sauki da kansa bayan 'yan kwanaki, sai dai akwai lokutan da ya kan yi tsanani.
Amma idan bai yi tsanani ba, ta ce akwai wasu matakan za a iya dauka a domin samun sauki. Wadanda suka hada da samun hutu sosai, shan maganin kashe zafin ciwo da kurkure baki da ruwan dumi mai gishiri, Ko da yake ta yi karin haske da cewa kada a baiwa yara ruwan gishirin don kuskure baki.
To idan muka dawo Najeriya wata kwararriyar likitar yara da ke aiki da asibitin koyarwa na Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi ta ce ana daukarsa ba abin damuwa ba ne idan yaro ya samu ciwon kamar sau bakwai a cikin shekara guda.
A cewarta yara kanana na haduwa da kwayoyin cuta kuma jikinsu na samar da sojojin da za su ba su kariya ta yadda idan nan gaba sun kamu da kwayoyin cutar, sojojin za su iya yaki da su.
Idan ta bayyana tsaftar jiki, musamman wadda ta shafi baki da na muhalli na da muhimmanci saboda yara kan dauki kwayoyin cuta daga muhalli mara tsafta, lamarin da ke kaiwa ga ciwon hakkin wuya.