An tilastawa minista yin murabus kan mabarata a ƙasar Cuba

Asalin hoton, others
An tilastawa ministar ƙwadago da walwala ta ƙasar Cuba, Marta Elena Feitó Cabrera, yin murabus daga muƙaminta bayan ta yi tsokaci a wani zama na majalisar dokokin ƙasar inda ta musanta kasancewar mabarata a tsibirin da ke ƙarƙashin mulkin masu ra'ayin gurguzu.
Ministar ta ce babu wani abu kamar "mabarata" a Cuba kuma mutanen da ke tsintar bola a ƙasar, a zahiri, suna yin hakan ne kawai don samun " kuɗi", kamar yadda ta ce.
Kalaman nata sun janyo suka daga al'ummar Cuba a gida da waje, kuma sun sa shugaban tsibirin, Miguel Diaz Canel ya maida martani . Ta yi murabus ba da jimawa ba.
Ministar ƙwadago da walwala ta yi wannan tsokaci ne a farkon makon nan a wani zama na Majalisar Dokokin ƙasar, inda ta yi magana game da barace-barace da ma su tsintar bola a Cuba.
Marta Elena Feitó Cabrera ta musanta kasancewarsu tana mai cewa "babu mabarata a Cuba. Akwai mutane da suka fake da yin bara don samun kuɗi cikin sauki," in ji ta. Bugu da ƙari, ta zargi mutanen da ke tsintar shara da kasancewa " ƴan jari bola waɗanda ke yin haka ba bisa ƙa'ida ba."
Ministar dai ba ta yi tunanin cewa kalamanta za su janyo fushin jama'a ba da kuma irin yadda suke bayyana shugabancin ƙasar a matsayin maras tausayi, mai mulkin kama karya wadda bata da damu da halin ƙuncin a ƴan ƙasar suke ciki ba .
Wasu masu fafutuka da masana a ƙasar sun wallafa wata wasiƙa da ke kiran a tsige ta suna masu cewa kalaman "abin cin fuska ne ga al'ummar Cuba". Shugaban Cuban, Miguel Diaz-Canel, sannan ya soki Ms Feitó Cabrera a zaman majalisar duk da cewa bai ambaci sunanta ba - yana mai cewa shugabancin ba zai iya "yin aiki tare da masu rena mutane ba " ko kuma " waɗanda ba su da damu da halin da mutane suke ciki ba".
Yanzu Ms Feitó Cabrera ta yi murabus daga mukaminta, wanda jam'iyyar gurguzu ta Cuba da gwamnatin ƙasar suka amince da shi.
Yayin da gwamnatin Cuba ba ta fitar da alƙaluma a hukumance kan adadin mutanen da ke bara ba, ƙaruwar adadinsu ya bayyana kansa ga galibin ƴan ƙasar a cikin mawuyacin halin matsin tattalin arziki na tsibirin.












