Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda sabon kuɗin fiton man fetur zai shafi farashinsa a Najeriya
Bayan matakin da gwamnatin Najeriya ta fito da shi na sanya harajin kashi 15 a kuɗin fito na man fetur da iskar gas ne ƴan ƙasar suna ta tafka muhawara kan abin da hakan ke nufi.
Tun bayan da matatar Dangote ta fara aiki, sai Najeriya ta rage amfani dogaro da shigo da fetur, sannan masana suka ce hakan ya taimaka wajen ƙarfafa darajar naira.
Amma duk da haka, hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce sama da kashi 65 na man fetur da ake amfani da shi a Najeriya shigo da shi ake yi.
A ranar Alhamis da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya amince da dokar kashi 15 na kuɗin fito, wanda ke nufin duk wanda ya shigo da man fetur, zai biya ƙarin kashi 15 a matsayin haraji.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Sunday Dare ya ce an fito sa sabon tsarin ne domin ƙarfafa gwiwar matatun cikin gida, inda a cewarsa zai sa farashin man fetur na matatun cikin gida ya yi sauƙi.
Abin da masana suke cewa
Yakubu Dimka jigo ne a ƙungiyar manyan dillalan man fetur wato IPMAN, ya bayyana wa BBC cewa lallai sabon tsarin zai taimaki matatun man fetur na cikin gida.
"Muna tunanin idan sabon tsarin ya fara aiki, farashin litar man fetur zai iya komawa kusan naira 600," in ji Dimka.
"Ba don matsalar Pengassan da Nupeng ba, ai farashin man ya kusa zuwa naira 820 a wani lokacin baya. Amma sai ƙarancin ɗanyen man fetur ya sa farahin ya tashi sama."
Ƙungiyoyin Pengasan da Nupeng na da tasiri sosai, inda ko a kwanakin baya suka ja daga da matatar Dangote a watan Satumba, har suka shiga yajin aiki da ya haifar da ƙarancin man fetur na wani ɗan lokaci a ƙasar.
Sai dai Dimka ya ce tsarin zai fi aiki ne idan ya kasance akwai matatun mai da dama a ƙasar, saboda a cewarsa idan matatun ba su da yawa, ƴar ƙaramar matsala sai ta jefa ƙasar cikin ƙarancin mai.
Haka ma ƙungiyar ƴankasuwar fetur ta Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria (Petroan) ta fitar da sanarwa, inda a ciki ta yaba wa Tinubu da fito da sabon tsarin, inda ta ce matakin zai ɗauki matatun mai na cikin gida.
Sai dai ƙungiyar ta ce matuƙar ba a sa ido sosai kan harkokin matataun na gida ba, "hakan kuma zai iya haifar da ƙoƙarin mamaye komai da kaka-gida a harkar."
Sai ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gyara matatun man fetur na Najeriya na Fatakwal da Warri da Kaduna su koma aiki ba tare da ɓata lokaci ba.
Ƙarin haraji ne wannan - Jam'iyyun adawa
Sai dai kuma wasu jam'iyyun hamayya a ƙasar sun soki matakin na Tinubu, inda suka ce gwamnatin na so ne kawai ta ƙara tatse ƴan Najeriya.
Adewole Adebayo, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar SDP, ya ce alamu na nuna cewa "nan gaba Tinubu zai iya fito da harajin shaƙar iskar numfashi, inda ƴan Najeriya za su riƙa biyan kuɗin iskar da suke shaƙa."
Ɗansiyasan ya ce kamata ya yi Tinubu ya fara gyara matatun man fetur na ƙasar su koma aiki gadan-gadan kafin ya kawo tsarin da zai hana masu shigo da man fetur daga waje sakat.
"Mun ba ka matatun man fetur ka lura da su, ka naɗa kanka a matsayin ministan man fetur. Ana kashe biliyoyin kuɗi wajen gyara da lura da su duk shekara, amma ka kasa gyara su. Don haka kai ne dalilin da ya sa dole ake shigo da fetur daga waje ai."
"Abin da ya kamata shugaban ya yi shi ne ya kira minista a ma'aikatar man fetur Heineken Lokpobiri da shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL Bayo Ojulari ya faɗa musu ga da ga cewa yana so matatun ƙasar su koma aiki. Ya ce ya ba su wata shida su gyara komai da komai. Ya bayyana musu a fayyace cewa, 'ina so a daina shigo da man fetur Najeriya baki ɗaya," in ji Adewole.