Me ya sa Majalisa ke son ƙayyade jarin naira biliyan 500 ga kamfanonin rarraba lantarki?

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar wakilan Najeriya ta bayar da shawarar ƙayyade naira biliyan ɗari biyar, a matsayin jari mafi ƙankanta da kamfanoni goma sha ɗaya da ke rarraba wutar lantarki na ƙasar, wato DisCos, za su mallaka, muddin suna son ci gaba da gudanar da wannan harka.
Hakan ya biyo bayan damuwar da ake ta nunawa, cewa kamfanonin rarraba lantarkin suna fama da ƙarancin kuɗin aiwatar da ayyukansu yadda kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, har a ci ribar da ta kamata.
Ƴan majalisar wakilan Najeriyar suna ganin matuƙar ba ƙara yawan jarin kamfanonin raba wutar lantarkin aka yi ba, to ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba.
Asali ma dai za su yi ta zama wata babbar barazana ce kawai ga ci gaban tattalin arziki Najeriya da jin daɗin jama'ar ƙasar.
Saboda haka, majalisar ta ƙarfafa cewa, wajibi ne kamfanonin raba wutar lantarkin na Najeriya su ƙara jarinsu da aƙalla naira biliyan ɗari biyar ba.
Masana harkar wutar lantarki kuwa, irin su Injiniya Danliti Inusa, suna ganin wannan shawara ce da ta dace:
‘‘A halin yanzu su kamfanonin, mafi yawan su za ka ga suna da matsaloli waɗanda yake ya kamata a gyara su, saboda a samar da wuta yadda ya kamata ga al’umma. A misali akwai buƙatar ƙara yawan ita na’urar raba lantarkin watau ‘transformer’ a wasu wurare da yawa. Sannan shi kuma shi kanshi layin da ke bayar da wutar ya kamata a ƙara yawansa, sannan akwai maganr wadata jama’a da mitoci.
‘‘Dukkan waɗannan abubuwa suna buƙatar kuɗi, to idan ya zamto kamfanonin basu da kuɗin lallai za ai ta tafiya ne ana dawowa’’
Injiniya Danliti Inusa ya ce fa'idar gwaɓaɓa jarin kamfanonin raba wutar lantarkin kuma ba kaɗan ba ce, a cewar Injiniya Ɗanliti Inusa:
To, amma abu ne mai yiwuwa kamfanonin rabar wutar lantarkin na Najeriya su samar da waɗannan kuɗaɗe da ake magana?
Injiniya Danliti Inusa ya ce hakan za ta tabbata saboda a cewar sa ‘’akwia harkai kasuwanci babba a wutar lanatarki’’.
Ya ce kamfanonin suna da zaɓi ta yadda za su iya sayar da hannayen jari ga jama’ar gari domin ganin sun shigi an dafa wajen bunƙasa ayyukan kamfanin.
Ana ganin idan har aka inganta harkar wutar lantarki a Najeriya, hakan zai taimaka wa al'umma ta fuskar bunƙasa masana’antu da samar da ayyukan yi, da kasuwanci da lafiya da ilimi da dai sauransu. Al'amarin da jama'ar ƙasar ta ƙishirwar gani a ƙas.











