Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwiwarmu ba ta yi sanyi ba domin mu zamu ci zaben gwamna a Adamawa — APC
Jam’iyyar APC a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce ko kadan gwiwarta ba ta yi sanyi ba bayan kammala zaben shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta samu nasara a jihar.
APC, wadda ke da ‘yar takara mace daya tilo a jihar - ta ce domin samun nasarar PDP a zaben shugaban kasa ba abu ba ne da zai tsoratasu.
Jami’in yada labarai na jam’iyyar a jihar, Muhammad Abdullahi, ya ce zaben gwamna daban na shugaban kasa ma daban.
Ya ce,’’ Ba mamaki ba ne zaben gwamna yazo mu ci zabe, domin alkaluman zabe a Najeriya yanzu sun canja, duka bin da mutum ke tsammani ba haka ba ne don masu zabe sun waye sun san abin da suke so.”
Muhammad Abdullahi, ya ce duk da jam‘iyyar PDP ita ke mulki a jihar, suna fatan samun nasara a zaben gwamnan da ke tafe.
Sanata Aishatu Dahiru Binani, ita ce ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar ta APC a jihar ta Adamawa, wadda kuma jam’iyyarta ke mata hasashen samun nasara a zaben gwamna da ke tafe.
Bisa ga dukkan alamu dai fafatawa ce mai zafi da ke gaban dukkan ‘yan takarar gwamna a jihar Adamawa a zaben 2023, domin kuwa dukkan jam’iyyun da suka fitar da ‘yan takara a jihar na ganin cewa lokacin da za su samar da gwamna daga jam’iyunsu ya zo.
Ga jam’iyyar APC dai, idan har ta ci zaben gwamnan, to za ta kafa tarihin samar da mace ta farko a matsayin gwamna a Najeriya.