Yadda wani farar fata ya kashe mata biyu ya bai wa alade gawarsu a Afirka ta Kudu

Lokacin karatu: Minti 2

Labarin matan nan guda biyu da ake zargin wani farar fata da kashe su a gonarsa sannan ya miƙa wa alade gawarsu ya cinye na ci gaba da tayar da hankali a ƙasar Afirka ta Kudu.

Matan guda biyu da suka haɗa da Maria Makgato mai shekaru 45 da Lucia Ndlovu mai shekaru 34 dai an yi zargin cewa farar fatar ya harbe su ne a lokacin da suka shiga gonarsa domin neman abinci a kusa da Polokwane da ke arewacin lardin Limpopo na Afirka ta Kudun.

An zargi farar fatar da jefa wa alade gawar matan a wani mataki na ƙoƙarin ɓoye shaidar abin da ya faru.

Yanzu haka dai wata kotu ce za ta yanke cewa za a iya bayar da belin farar fatar mai suna Zachariah Johannes Olivier mai shekaru 60 tare da masu aikinsa Adrian de Wet mai shekaru 19 da kuma William Musora mai shekaru 50, kafin ranar shari'ar da za a yi musu ta tuhumtar kisan kai.

Har kawo yanzu dai ba a nemi mutanen uku su amsa tuhumar da ake yi musu ba, wani abu da zai faru lokacin da shari'ar da za a yi musu za ta fara a nan gaba.

A zaman kotu na baya, masu zanga-zanga sun yi dandazo a wajen kotun inda suke neman ka da a ba da belin waɗanda ake zargin.

Walter Mathole wanda ɗan uwan Ms Makgato ne ya shaida wa BBC cewa al'amarin ya ƙara ƙamarin rikicin wariyar launin fata tsakanin baƙar fata da farar fata a ƙasar.

Kuma rikicin ya fi bayyana ƙarara a yankunan karkara na ƙasar duk da ƙoƙarin kawo ƙarshen mulkin wariya ga baƙar fata shekaru 30 da suka gabata.

Mutanen uku dai na fuskantar tuhume-tuhumen yunƙurin kisan kai saboda harbin da suka yi wa mijin Ms Ndlovu, wadda ta kasance a gonar da kuma mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba.

Mabutho Ncube ya tsallake rijiya da baya da yammacin ranar Asabar 17 ga watan Agusta inda ya yi jan ciki ya gudu har ya samu damar kiran likita domin ya taimaka masa.

Ya ce ya sanar da ƴansanda al'amarin kuma sun gano gawarwakin mai ɗakinsa da ta Ms Makgato da suka ruɓe a wurin da aladen yake.

Jam'iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters (EFF) ta ce ya kamata a rufe gonar da aka aikata laifin.

Hukumar Kare Ƴancin Ɗan'adam ta ƙasar ta soki kisan sannan kuma ta yi kira ga taron tattaunawa kan matsalar nuna wariyar launin fata a ƙasar.