Liverpool da Bayern Munich na zawarcin Guehi, Flick zai ci gaba da riƙe Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta fice daga zawarcin ɗanwasan bayan Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 25, lamarin da ya bar ɗanwasan da zaɓi a tsakanin Liverpool da Bayern Munich. (AS - in Spanish)
Ƙungiyoyin gasar firimiya da dama na bibiyar ɗanwasan bayan Feyenoord mai shekara 19, Givairo Read amma suna fuskantar ƙalubale daga Bayern Munich. (Teamtalk)
Tottenham da Liverpool ƙoƙarin ɗauko ɗanwasan bayan Girka da Wolfsburg, Konstantinos Koulieraki, mai shekara 21. (TBR Football)
Kocin Barcelona Hansi Flick ba shi da aniyar barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana duk da rahotannin da ke cewa ya gaji da ƙungiyar kuma yana shirin sauya sheƙa.(Sky Germany - in German)
Leeds na fuskantar turjiya a ƙoƙarin ta na ci gaba da riƙe mai tsaron ragar Ingila mai shekara 18 har baya watan Janairu saboda ƙungiyoyi da dama na zawarcin sa.(Caught Offside)
Barcelona na fatan kammala sayen ɗanwasan Manchester United da Ingila mai shekara 28, Marcus Rashford, wanda ke zaman aro a wajen ta, amma ba za ta iya biyan farashin £25.5 da aka ƙaƙaba wa ɗanwasan gaban ba. (Fichajes - in Spanish)
Juventus na shirin fara tattaunawa da ɗanwasan da Liverpool da Chelsea da kuma Arsenal ke zawarci, Kenan Yildiz, kuma tana fatan ɗanwasan gaban Turkiyyan mai shekara 20, zai ci gaba da takaleda a Turin. (Teamtalk)
Roma are Za ta gabatar da tayin ɗaukar aron ɗanwasan gaban Manchester United da Netherlands mai shekara 24, Joshua Zirkzee a watan Janairu. (Fichajes - in Spanish)













