Me ya sa wasu maza ke zuwa neman kwaskwarimar gyaran jiki?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmed Abdullah
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Aiko rahoto daga, Beirut
- Lokacin karatu: Minti 5
A lokacin da na fara aiki da gidan talbijin, na ɗauka cewa ba iya saƙon da zan bayyana ne kawai abin la'akari idan na bayyana a akwatin talbijin ba, har kwalliyata abin la'akari ne.
Shekarata 22, kuma duka da ƙananan shekaruna, ina jin takaicin yadda fatar goshina ta faratattarewa, haka kuma hancina ya yi girman da ba na jin daɗin bayyana a gaban kyamara.
Kan haka ne na yanke shawarar zuwa wajen abokin ƙuruciyata, wanda a yanzu likitan fata ne, ya kuma bani shawarar cewa na yi wata allura da ke rage bayyana tauyewar fatar, ya kuma shaida min cewa a ganinsa wannan hanya ce mai kyau idan aka ɗauki matakin fara ta da wuri.
Ba wannan kaɗai ba, na kuma yi amfani da damar wajen tiyatar kwaskwarimar hancina, sannan aka yi min ta fata duka a lokaci guda, lamarin da ya ƙara fito da ni fes cikin akwatin taljibin
Labarina na daga cikin abin da ya fi samun karɓuwa tsakanin maza a ƙasashen Larabawa da ma duniya baki ɗaya, inda kwalliyar gyaran jiki ke neman zama wani abin gogayya tsakanin mata da maza.
Adadin mazan da ke tiyatar gyaran jiki na ƙaruwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar likitocin tiyatar kwaskwarimar jiki ta Amurka, ta ce an samu ƙaruwar maza masu ɗaukar matakan gyara halittarsu da kashi 24 cikin 100 tsakanin 2012 zuwa 2022.
Ana samun ƙaruwar wannan buƙatar tsakanin maza a Amurka, kama daga waɗanda ake yi wa tiyata zuwa waɗanda ke bin wata hanyar, inda ƙungiyar ta ce an kuma samu ƙaruwar sosai tsakanin 2022 zuwa 2023.
A 2022, tiyatar gyaran hanci ta kasance wadda ta fi yawa, tsakanin ayyukan kwaskwaroimar jiki da aka yi a ƙasar, bayan da aka yi wa mutum 650,121, inda kashi 24 cikin 100 na wannan adadi suka kasance maza.
Sai kuma allurar kwaskwarimar halitta ta 'Botox injections' da aka yi wa mutum 473,354 domin rage tattarewar fatarsu, da kuma wasu nau'ikan magunguna da aka bai wa mutum 99,148, domin ƙara fito da ƙwalliyar mutum.
A Amurka kaɗai an yi wa maza aikin cire musu gashi musamman na hammata da ƙirji.
A shekarar 2023 kaɗai, allurar kwaskwarimar jiki tsakanin maza, ta ƙaru da kashi 6 idan aka kwatanta da shekarar 2022 da ta gabata, inda aka yi wa mutum 569,438 allurar.
Tiyatar gyaran hanci ma ta ƙaru da kashi 10, inda aka yi wa mutum 6,867.
Daɗin daɗawa, tiyatar cire gashi ta ƙaru da kashi 7, inda aka yi wa mutum 242,600.
Alƙaluma sun nuna cewa masu shekara tsakanin 30 zuwa 50, maza da mata ne suka fi yawa a masu buƙatar kwaskwarimar jiki, sakamakon wasu dalilai da suka haɗa da buƙatar aiki da sauransu.
Ya batun yake a ƙasashen Larabawa?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƙasashen Larabwa, Saudiyya ce ta 22 daga cikin ƙasashe 25 da ke aikin kwaskwarimar jiki ga maza da mata a duniya, lamarin da ke nuna ƙaruwar buƙatar irin wanan aiki a Saudiyyar, a cewar mujallar 'Otorhinolaryngology' mai nazari kan cutukan da suka shafi hanci da kunne da kuma maƙogoro ta ƙasar.
Wani likitan kwaskwarimar jiki, mai suna Fadi Abi Azar, da ke aiki a Beirut da Kuwait, ya tabbatar wa sashen Larabci na BBC cewa ya fahimci ana samun ƙaruwar buƙatar kwaskwarimar jiki tsakanin maza.
Ya ƙara da cewa tiyatar kwaskwarimar hanci ne kan gaba a abin da maza suka fi buƙata, saboda dalilai na ƙara kyau da magance matsaloli numfashi.
Babbar tiyatar kwaskwarimar gyaran jiki da maza suka fi yi a cewar Abi Azar, ita ce tiyatar rage kitse, musamman a ciki da mazaunansu da kuma rage tudun nononsu - wata matsala da kashi ɗaya biyu uku na mazan duniya ke fama da ita.
Ya ci gaba da cewa ''tudun nono a wajen maza kan shafi ƙwarin gwiwarsu, lamarin da ke da dama ke yin tiyata domin cire shi''.
A cewar ƙungiyar likitocin kwaskwarimar jiki ta Amurka, a 2020 alƙaluma sun nuna cewa an yi aikin cire tudun nono 40,775 tsakanin maza a Amurka.
Ko hakan na shafar mazantakar namiji?

Asalin hoton, Getty Images
Mun tattauna da Petra Halawi, wata ƙwararriya kan jinsi, domin jin ko hakan na shafar mazantakar ganin yadda mazan ke rububin tiyatar kwaskwarimar jiki domin inganta adon da kwalliyarsu.
Halawi ta faɗa wa BBC cewa ''har yanzu ana ɗaukar abin a matsayin wani abin kunya ga mazan da suka yi kwaskwarimar jiki. Murtum mai siffar maza da murya ta maza, amma a same shi da gyararren hanci ko wasu siffofi, ana ganin bai dace a yi masa wannan aiki ba''.
"Da dama daga cikin al'umma na kallon hakan a matsayin siffofin mata, duk da cewa wannan hasashe da ake yi na raguwa sannu a hankali, kuma mutane na ci gaba da rungumar waɗannan sabbin hanyoyi,'' kamar yadda ta bayyana.
Dangane da chanjin mahangar namiji, kuwa da wasu al'ummomi ke yi wa wannan ɗabi'a, Halawi ta ce: "A gargajiyance ana alaƙanta mazantaka da siffofi na ƙarfi, da jarunta, da kuma juriya, amma a yanzu siffofin mazantaka sun ƙunshi kyau da fuskar gyaran gashi da gemu da farce da kuma tufafi da ƙoƙarin bayyana kyawun siffa da bayyana sha'awa''.
Halawi ta jaddada cewa ra'ayoyi yawanci suna canzawa dangane da kowace al'umma da lokacin dake rayuwa: "A zamanin da, maza suna da ayyuka dangane da jinsinsu, amma sun canza tsawon shekaru, kuma abin da muke gani a yau shi ne ƙa'idoji (na zamaninmu)."
Wani bincike da aka wallafa sakamakonsa a mujallar kwaskwarimar jiki ta Amurka, ta nuna cewa shafukan sada zumunta ne kan gaba wajen abin da ke janyo ra'ayin mutane dangane da kwaskwarimar jiki.
Bayanan Google Trends tsakanin 2004 da 2017 sun nuna cewa an fi sha'awar hanyoyin da ba na tiyata ba, kamar Botox da filler, idan aka kwatanta da na tiyata.
Binciken ya kuma alaƙanta wannan da ƙaruwar tasirin Istagram da Facebook,inda suka ce abubuwan da likitoci da fitattun mutane ke wallafa wa a shafukan na matuƙar tasiri wajen janyo hankali mutane dangane da tiyatar kwaskwarimar gyaran jiki.
Abi Azar ya tabbatar da wannan, yana mai cewa ''shafukan sada zumunta sun taimaka matuƙa wajen janyo hankalin maza dangane da batun kyau da kwalliya, saboda a yanzu suna matuƙar damuwar da kyawun sifarsu''.
Ya ƙara da cewa ''yadda masu amfani da shafukan ke bayyana yadda aka yi musu tiyatar kwaskwarimar jiki da kuma yadda likitoci ke bayyana saukin yadda ake yin aikin duka a shafukan sun yi tasirin kwarai wajen janyo hankali mutane, musamman maza''.
Ya kuma ce wani ƙarin dalilin shi ne ''yadda likitocin suka zaftare farashin aikin domin samun kwastomomi ya taka rawa wajen samun sauƙin yin aikin a ko'ina''.
Ana sa samun ƙaruwar mazan da za su yi tiyatar kwaskwarima domin inganta siffofinsu, yayin da ake ci gaba da samun karɓuwar shafukan sada zumunta sakamakon ƙaruwar fasahar zamani, da suka ƙara saukaƙa amfani da shafukan.










