Su wane ne Isra'ilawa 48 da Hamas ta saki a yau?

Lokacin karatu: Minti 8

Hamas ta kammala sakin duka Isra'ilawa 20 masu rai da suka rage a hannunta da take garkuwa da su a Gaza.

An saki mutanen ne a rukuni biyu, na farko mutanen bakwai a Gaza, sai kuma rukuni na biyu na mutum 13 a Khan Younis da ke kudancin Gaza.

A cikinsu, ɗaya ne kawai ba ya cikin mutum 251 da suka yi garkuwa a su a lokacin da aka kai harin a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda ya ci mutum 1,200.

Isra'ila ta mayar da martani, inda ta ɗaiɗaita Gaza sannan ta kashe aƙalla mutum 67,000, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta fitar.

Waɗanda ake tunanin suna raye

Ariel Cunio: Mai 28 ne wanda aka yi garkuwa da shi a Kibbutz Nir Oz a ranar 7 ga Oktoba. Ɗan'uwanda Eitan, wanda ya sha ƙyar a harin ya ce Ariel ya tura masa saƙo cewa, "muna cikin ƙunci." Budurwarsa Arbel Yehud na cikin waɗanda Hamas ta saka a watan Janairun 2025 a musaya tsakaninta da Isra'ila.

David Cunio: Mai shekara 35 shi ma ɗan'uwan Ariel ne da aka yi garkuwa da su a tare. Matarsa da ƴaƴanu ƴanbiyu na cikin waɗanda Hamas ta saka a yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwamban 2023. A watan Fabrailu, ƴanuwansa sun ce waɗanda aka sako sun bayyana musu cewa yana raye.

Gali da Ziv Berman: Ƴanbiyu ne masu shekara 28 da aka yi awon gaba da su a Kibbutz Kfar Aza da maƙwabciyarsu Emily Damari. Sun kasance a tare da Emily na kwana 40 kafin a raba su. An sake ta a watan Janairun 2025, amma iyalan Gali da Ziv sun ce sun samu labarin suna raye.

Matan Angrest: Sojan Isra'ila ne mai shekara 22 da ya kasance a cikin motar sojoji a lokacin da Hamas ta kai harin na 7 ga Oktoban.

A farkon wannan shekarar ne ƴanuwansa suka ce waɗanda aka sako sun bayyana musu cewa yana da rai, amma yana fama da cutar asma da kuma raɗaɗin raunuka a jikinsa.

Matan Zangauker: Matashin mai shekara 25 yana tare da matarsa Ilana Gritzewsky ne aka ɗauke su a Nir Oz. An saki Ilana a yarjejeniyar tsagaita wuta ta Nuwamban 2023. A watan Disamba Hama ta saki wani bidiyo, inda a ciki ya yi jawabi.

Eitan Horn: Ɗan asalin Ajantina mazaunin Isra'ila ne mai shekara 38, shi ma an yi garkuwa da shi ne tare da ƙaninsa Yair a Nir Oz. An saki Yair a yarjejeniyar watan Fabrailun 2025. Sannan Hamas ta fitar da bidiyon Eitan yana sumbatar ɗan'uwansa Yair suna kuka a lokacin zai tafi.

Nimrod Cohen: Sojan Isra'ila ne mai shekara 21 da Hamas ta kama a lokacin da ta kai harin a Nahal Oz. A watan Fabrailun 2025 ne wani wanda ya kuɓuta ya faɗa a ƴanuwansa cewa yana raye.

Omri Miran: An yi garkuwa da shi ne Nahal Oz. A watan Afrilun 2025 Hamas ta saki bidiyon Omri yana bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Guy Gilboa-Dalal, matashi ne mai shekara 24 da aka yi garkuwa da shi a taron bikin Nova da ya halarta tare da ɗanuwansa Gal. Gal ya tsira. Hamas ta fitar da wani bidiyo wanda a ciki aka ga Guy da wani mai suna Alon Ohel a cikin mota a lokacin da Isra'ila ke shirin afka wa birnin Gaza a watan Agusta.

Alon Ohel, matashi ne mai shekara 24 da aka hango a cikin wata motar Hamas tare a Guy a birnin Gaza a watan Agusta.

Yosef-Chaim Ohana, shi ma a wajen bikin na Nova aka yi awon gaba da shi. A watan Mayun 2025 Hamas ta fitar da wani bidiyo da aka ga Yosef tare da wani Elkana Bohbot a ciki.

Elkana Bohbot, mai shekara 36 ɗin ya shiga hannu ne a lokacin da yake aiki a bikin na Nova.

Isra'ila ta ce ta gano yana raye amma yana shan baƙar wahala kasancewar yana da cutar asma.

Avinatan Or, mai shekara 32 da aka yi garkuwa da shi tare da budurwarsa Noa Argamani. Sojojin Isra'ila sun ceto budurwar tare da wasu mutum uku a Gaza a watan Yunin 2024. A watan Maris na 2025 ƴanuwansa sun ce sun samu labarin yana raye.

Eitan Mor, mai gadi ne ɗan shekara 25 da ka aiki a wajen bikin. Mahifinsa Mor ya ce ɗansa ya ceci mutane da dama kafin a yi garkuwa da shi.

A watan Fabrailun 2025 ne iyayensa suka ce sun samu labarin yana raye kuma shi ne yake magana da yawun sauran.

Maxim Herkin, ɗan Isra'ila ne mai shekara 37 kuma ɗan Rasha ne da aka gayyata bikin. Abokansa biyu na cikin waɗanda aka kashe.

A watan Maris an ga Maxim a cikin bidiyon da Hamas ta fitar.

Bar Kupershtein, shi ma ma'aikaci ne a wajen bikin da ya riƙa taimakawa wajen ceton waɗanda suka samu rauni.

A watan Afrilun 2025 ne Hama suka fitar da wani bidiyo da yake ciki.

Segev Kalfon, ya shiga hannu ne a lokacin da yake yunƙurin tserewa daga dandalin biki.

A watan Fabrailun 2025 Ohad Ben Ami da aka sako ya faɗa wa iyayen Segev cewa yana raye.

Evyatar David, mai shekara 24 shi ma an sace shi ne a dandalin bikin.

A watan Agustan 2025 ne aka gan shi a cikin wani bidiyo da Hamas ta fitar.

Rom Braslabski, shi ma wani mai gadi ne mai shekara 21 da aka kama a lokacin da yake ƙoƙarin ceton wani wanda ya ji rauni.

A watan Agustan 2025 an ga Rom a cikin wani bidiyo da Hamas ta fitar yana kukar yunwa.

Waɗanda ba a ji ɗuriyarsu ba

Tamir Nimrodi, malami ne mai shekara 20 a rundunar sojin Isra'ila. Mahaifiyarsa ta masa ganin ƙarshe ne a bidiyon da aka fitar lokacin da ake kama shi.

Bipin Joshi, ɗalibi ne mai shekara 24 da aka ace a Kibbutz Alumim. A bidiyon harin na 7 ga Oktoba an ga Bipin yana tafiya a asibitin al-Shifa da ke Gaza.

Sannan an gan shi a wani bidiyon da aka fitar a Nuwamban 2023, wanda shi ne lokacin ƙarshe da aka gan shi.

Waɗanda aka tabbatar sun mutu

Tamir Adar, mai shekara 38 mai gadi ne da aka tabbatar da mutuwarsa a harin na 7 ga Oktoban, amma Hamas ta tafi da gawarsa.

Sonthaya Akrasri, ɗan asalin ƙasar Thailand ne da yake samun horon noma a ƙasar, amma aka kashe shi a Kibbutz Be'eri. Ministan harkokin wajen Thailand ya bayyana a watan Mayu cewa gawarsa na hannun Hamas a Gaza.

Muhammad al-Atarash, sojan Isra'ila ne mai shekara 39 da aka tabbatar da mutuwarsa a Nahal Oz a ranar 7 ga Oktoba, amma ba a ga gawarsa ba.

Sahar Baruch, matashin mai shekara 24 an yi garkuwa da shi ne, amma Isra'ila ta ce an kashe shi a lokacin da sojojinta suke yunƙurin ceto su a Gaza.

Uriel Baruch, an sace shi ne a wajen bikin Nova. A watan Maris iyalansa suka ce rundunar sojin Isra'ila ta faɗa musu cewa an kashe shi a Gaza.

Inbar Hayman, mai shekara 27 ce macen da ta rage a hannun Hamas da aka sace a dandalin bikin Nova. Ƴanuwanta sun ce an kashe ta a Gaza.

Itay Chen, sojan Isra'ila ne mai shekara 19 da aka tabbatar an kashe a harin na ranar 7 ga watan Oktoba. IDF ta ce an kashe shi ne Nahal Oz amma Hamas ta tafi da gawarsa.

Amiram Cooper, dattijo ne mai shekara 85 da aka yi garkuwa da shi Nir Oz. A Yunin 2024 ne IDF ta ce an kashe shi tare da wasu mutum uku - Nadav Popplewell da Chaim Peri da Yoram Metzger - a lokacin da sojojin na Isra'ila suka kai hari a Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Oz Daniel, 19 soja ne da aka kashe a a wata gwabzawa a aka yi da Hama a ranar harin na 7 ga Oktoba, amma suka tafi da gawarsa.

Ronen Engel, 54 na cikin waɗanda aka sace a Nir Oz tare da matarsa Karina Engel-Bart da ƴaƴansu mata biyu Mika da Yuval. An saki Karina da Mika da Yuval a yarjejeniyar Nuwamban 2023, sai a watan Disamba IDF ta tabbatar da mutuwarsa a hannun Hamas.

Meny Godard, an kashe shi ne a Be'eri tare da matarsa Ayelet, amma aka tafi da gawarsa Gaza.

Ran Gvili, ɗansandan Isra'ila ne mai shekara 24 da aka kashe a ranar harin a Kibbutz Alumim, amma Hamas ta tafi da gawarsa zuwa Gaza.

Tal Haimi, mai shekara 41 na cikin dakarun ƙasar da aka kashe a ranar 7 ga Oktoban, amma aka tafi da gawarsa Gaza.

Asaf Hamami, shi ma kanal ɗin soja ne da aka kashe a kusa da Kibbutz Nirim a harin, amma Hamas ta tafi da gawarsa Gaza.

Guy Illouz, matashi ne mai shekara 26 da aka harbe shi a dandalin bikin na Nova, amma ya mutu a Gaza bayan Hamas ta tafi da shi, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

Eitan Levi, direban motar haya ne mai shekara 53 da Hamas ta kashe a ranar harin amma suka tafi da gawarsa.

Eliyahu Margalit, dattijo ne mai 75 da Hamas ta kashe a Nir Oz a ranar harin, amma sojojin Isra'ila suka ce gawarsa na Gaza.

Joshua Mollel, matashin ɗalibi ne mai shekara 21ɗan asalin ƙasar Tanzania da harin ya rutsa da shi. Gwamnatin Tanzania ta tabbatar a watan Disamban 2023 cewa an kashe a harin, amma Hamas na riƙe da gawarsa.

Omer Neutra, kwamandan sojin Isra'ila ne da Hamas ta kashe a bakin iyakar Gaza. IDF ta ce a ranar ya mutu, amma Hamas ta tafi da gawarsa.

Daniel Peretz, hafsan sojin Isra'ila ne amma ɗan asalin ƙasar Afirka ta Kudu da aka kashe a harin a kusa da Nahal Oz amma aka tafi da gawarsa Gaza.

Dror Or, shi ma an kashe shi ne tare da matarsa Yonat sannan aka tafi da ƴaƴansa biyu Noam da Alma. An saki yaran a yarjejeniyar Nuwamban 2023, amma gawarsa na hannun Hamas.

Suthisak Rintalak, mai shekara 43 manomi ne ɗan asalin Thailand da aka kashe a Kibbutz Be'eri. Ministan harkokin wajen Thailand ya ce sun tabbatar da gawarsa na hannun Hamas a Gaza.

Lior Rudaeff, dattijo ne mai shekara 61 da aka kashe a harin, amma aka tafi da gawarsa Gaza.

Yossi Sharabi, an sace shi ne a Be'eri tare da ɗanuwansa Eli. A watan Janairun 2024 ana tabbatar da an kashe shi a Gaza, sannan daga bisani IDF ta ce gini ne ya faɗo masa ya mutu a sanadiyar harin da ta kai, amma gawarsa na hannun Hamas.

Arie Zalmanowicz, dattijo ne mai shekara 85 da aka sace a Nir Oz a ranar harin na 7 ga Oktoba. A watan Nuwamba Hamas ta fitar da bidiyo yana cewa yana fama da rashin lafiya, sannan bayan wata ɗaya aka tabbatar da mutuwarsa.

Hadar Goldin, sojan Isra'ila ne mai shekara 23 da aka kashe a Gaza a 2014, amma Hamas ta ci gaba da riƙe gawarsa tun lokacin.