Yadda burin cin jarrabawa ke sa ɗalibai kashe kansu a India

Dalibai na rubutu

Asalin hoton, Dipankar

Lokacin karatu: Minti 2

Kotun kolin Indiya ta fitar da wasu tsauraran matakai na kokarin shawo kan karuwar da ake ta samu ta daliban da ke kashe kansu saboda matsin lamba ko buri na karatu da kuma tsangwama da ake nuna musu.

Alkalan sun ce halin da ake ciki na nuni da gagarumar matsala ta lafiyar kwakwalwa a tsakanin matasa.

Alkaluman hukuma a kasar ta India na nuna cewa sama da dalibai dubu goma sha uku sun kashe kansu da kansu a shekarar 2022.

Dalibai na duba takarda

Asalin hoton, Getty Images

Kwararru sun ce daliban na samun kansu a yanayi na matsin lamba kan su ci jarrabawa sosai su samu maki mai yawa domin a dauke su a jami'a ko kuma su samu aikin da ake biyan albashi mai yawa.

Kotun kolin ta bayar da umarni cewa duk makarantar da take da daliban da suka wuce dari daya ta tabbatar da nada kwararrun masu bayar da shawara kan lafiyar kwakwalwa, sannan kuma su samar da sauran hanyoyi na kula da lafiya.

Kwararru sun ce sam-sam ba a koyar da yara yadda za su iya fuskantar matsala ko rashin samun nasara ko gazawa a rayuwa a duk lokacin da suka samu kansu a irin wannan yanayi ko rashin tabbas.

Kuma sun ce an fi mayar da hankali kan ganin matasan sun yi zarra a jarrabawa amma ba kalubalen rayuwa ba.

Wasu na nuni da cewa batun lafiyar kwakwalwa abu ne da kusan ba a mayar da hankali sosai a kanshi.

Sannan ana sanya buri da matsi sosai a kan dalibai da hakan kan janyo gogayya a tsakaninsu ta ganin sun fi abokan karatunsu.

Bincike ya nuna cewa daga cikin manyan abubuwa ko hanyoyi biyu da ke janyo mutuwa a tsakanin matasa a India - kashe kai na ciki.