Manyan ƴantakarar shugaban ƙasar Senegal a zaɓen 2024

A ranar 24 ga watan Maris ɗin 2024 ne za a gudanar da babban zaɓen ƙasar Senegal.

A baya an tsara gudanar da zaɓen ne a ranar 25 ga watan Fabararun 2024, sai dai shugaban ƙasar mai barin gado ya sanar da ɗage zaɓen sai abin da hali ya yi.

Amma a ranar 15 ga watan Fabarairu Majalisar shari'a ta Senegla ta yi watsai da matakin shugaban ƙasa da na majalisar dokokin ƙasar, inda ta bayar da umurnin gudanar da zaɓen ba tare da ɓata lokaci ba.

Bayan haka ne gwamnatin ƙasar ta amince da gudanar da zaɓen a ranar 24 ga watan Maris.

Ga ƴan takarar da ake tunanin za su taka rawar gani a lokacin zaɓen.

Ku latsa bayanin ɗantakar domin karanta ƙarin bayani kan kowane ɗantakara.