Bidiyon matukin da ya tsinci miliyoyin kudi ya mayar a Kano
Duk da tsangwamar da wasu ke yi wa Auwalu Salisu, bayan ya yi gamon katar da tsintar miliyoyin kudi, amma bai yi kasa a gwiwa ba kawai ya yanke shawarar mayarwa masu dukiyar abinsu.
Ya shaida wa BBC cewa ya mayar da miliyoyin kudin da ya tsinta ne, saboda ya yi imani dukiyar wani ba za ta yi masa amfani ba, kuma ko ba komai shi mutum ne mai wadatar zuci.
Auwalu Salisu ya ce sakamakon mayar da dukiyar ga masu ita da ya yi, ya kara samun martaba, kuma wasu sun yi masa kyautukan da suka faranta masa rai.








