ƙasashe shida da dakarun Ecowas suka taɓa kai wa yaƙi

...

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Juma'a manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen yammacin Afirka suka amince da wani tsarin kai samame a jamhuriyar Nijar matuƙar jagororin juyin mulkin ƙsar suka gaza mayar da mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnati kafin ranar Lahadi.

Tuni dai Ƙungiyar ci gaban tattalin arziƙin yankin (ECOWAS) ta ƙaƙaba wa ƙasar ta Nijar takunkumi, tare da barazanar cewa za ta iya yin amfani da ƙarfin soji wurin mayar da hamɓararren shugaban ƙasa, Mohamed Bazoum kan mulki.

Bari mu kawo muku wasu lokuta a baya da dakarun ƙasashen yammacin Afirka suka taɓa kai agaji a wasu ƙasashen yankin.

LIBERIA

Dakarun Ecomog a kusa da Monrovia, babban birnin Liberia

Asalin hoton, Getty Images

A shekarar 1990 shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun tura sojoji domin shiga tsakani a yaƙin basasa da ya ɓarke a Liberia tsakanin dakarun gwamnatin shugaba Daniel Doe da na ƙungiyoyin ƴan tawaye biyu.

Shiga tsakanin na dakarun ƙasashen da ake yi wa laƙabi da ECOMOG ya taimaka wajen dawo da tsaro a ƙasar, sai dai an zargi dakarun da tafka laifukan take haƙƙin ɗan'adam, kamar yadda ƙungiyar Human Rights Watch ta bayyana.

An tura dakarun ECOMOG 12,000 zuwa ƙasar ta Libaria. Kuma an kammala janye dakarun a shekarar 1999, shekara biyu bayan zaɓen tsohon jagoran ƴan tawaye, Charles Taylor a matsayin shugaban ƙasa.

Sai dai an sake tura dakarun zuwa ƙasar gabanin kawo ƙarshen wani mummunan faɗa da aka gwabza a ƙasar na tsawon shekara 14, wanda ya zo ƙarshe a 2003.

An mayar da sojoji 3,600 na ƙungiyar a ƙarƙashin dakarun wanzar da tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda suka ci gaba da aiki a ƙasar har shekarar 2028.

SALIYO

A 1998, dakarun ECOMOG ƙarƙashin jagorancin sojojin Najeriya sun shiga tsakani a yaƙin basasan da ake tafkawa a Saliyo, inda suka samu nasarar kawar da sojojin juyin mulki da mayaƙan da ke mara musu baya da Freetown, babban birnin ƙasar.

Hakan ya ba su nasarar mayar da shugaba Ahmed Tejani Kabbah kan mulki, shekara ɗaya bayan yi masa juyin mulki.

A shekara ta 2000 dakarun ECOMOG sun janye daga ƙasar, inda suka miƙa ragamar shirin wanzar da zaman lafiya ga dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Yaƙin ƙasar wanda aka kwashe shekara 10 ana gwabzawa ya zo ƙarshe a shekara ta 2002.

GUINEA-BISSAU

A shekarar 1999, ECOWAS ta tura dakarun ECOMOG guda 600 zuwa Guine-Bissau domin tabbatar da ɗorewar wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, sanadiyyar barzanar juyin mulki da ake fuskanta.

Bayan wata uku da tura dakaru sai ƴan tawaye suka karɓe mulki, wanda hakan ya sanya aka janye dakarun na ECOMOG daga ƙasar.

Bayan wani juyin mulkin, ECOWAS ta sake tura dakarunta zuwa ƙasar inda suka yi aiki tsakanin 2012 zuwa 202, domin hana sojoji tsoma hannu cikin siyasa da kuma kare ƴan siyasa.

An kuma ƙara tura wasu sojoji 631 a 2022 domin samar da zaman lafiya a ƙasar bayan wani yunƙurin juyin mulki a shekarar.

IVORY COAST

A shekara ta 2003 an tura dakarun na yammacin Afirka zuwa Ivory Coast domin taimaka wa dakarun Faransa wajen tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƴan tawaye, lamarin da ya raba kan ƙasar zuwa gida biyu na kimanin shekara takwas.

A 2004 an mayar da sojojin na ƙasashen yammacin Afirka a ƙarƙashin shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Dakarun ECOMOG a birnin Freetown na ƙasar Saliyo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dakarun ECOMOG a birnin Freetown na ƙasar Saliyo

MALI

ECOWAS ta tura dakaru zuwa Mali a 2013 a wani ɓangare na ƙoƙarin korar mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Al-Qa'ida daga arewacin ƙasar.

Kamar yadda ya faru a wasu ƙasashen, dakarun sun miƙa aikin ga sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar.

Yanzu haka mayaƙa masi alaƙa da al Qa'ida da kuma IS suna cin karensu babu babbaka a tsakiya da kuma arewacin Mali, waɗanda ɓarnar da suka kwashe sama da shekara goma suna tafkawa ta yaɗu zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar, masu maƙwaftaka.

GAMBIA

A 2017, ECOWAS ta tura dakarunta 7,000 zuwa Gambia daga Senegal domin tursasa wa tsohon shugaban ƙasar Yahya Jammeh sauka daga mulki.

Lamarin ya sanya Jammeh ya yi gudun hijira tare da miƙa mulki ga Adama Barrow, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar.

Dakarun Jammeh ba su nuna wata turjiya da sojojin ECOWAS da aka tura ba, waɗanda aka yi wa laƙabi da masu Aikin maido da dimokuraɗiyya.

Bayanai: Daga Reuters