Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne suka lakaɗa wa Danbilki Kwamanda duka a bidiyo?
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Tun daga safiyar Alhamis zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu abin da ƴan arewacin Najeriya suka fi tattaunawa a kansa kamar ɗan siyasar nan na jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdulmajid Danbilki wanda aka fi sani da Danbilki Kwamanda.
Ba wani abu ne dalili illa bidiyon da ya ɓulla a shafukan sada zumuntar da ke nuna yadda wasu mutane ke dukan ɗansiyasar mai yawan magana a kafofin yaɗa labarai da bulala bayan sun ɗaure hannunsa da ankwa.
An ji mutanen da ba a ganin su a bidiyon na tuhumar sa kan dalilin da ya sa "yake zagin" gwamnan Kaduna Uba Sani, yayin da shi kuma yake musanta zargin.
BBC Hausa ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a Abuja ranar Laraba da dare.
Lamarin ya faru ne ƴan kwanaki bayan Kwamanda ya soki Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani game da rikcin da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai a wani gidan rediyo da ke birnin Kano.
Kwamanda ya shahara wajen sukar gwamnatoci da ƴan siyasa tsawon shekaru a kafofin yaɗa labarai na jihar Kano da wajenta. Yakan soki ƴan adawa da kuma jam'iyyarsa ta APC mai mulkin Najeriya.
Zuwa yanzu bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, musamman Facebook da WhatsApp, inda mutane da dama ke bayyana mabambantan ra'ayi.
Tuni wasu suka fara yeƙuwar nema wa Danbilki adalci ta hanyar amfani da maudu'in JusticeForDanbilkiCommander.
Me muka gani a bidiyon?
Wata majiya ta kusa da Danbilki Kwamanda ta shaida wa BBC cewa ɗansiyasar yana Abuja kuma bai koma Kano ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Daga cikin abin da muke iya ji da gani a bidiyon akwai sunan Abdul, wanda ɗaya daga cikin masu dukan Danbilki ke tambayar sa ko bidiyon da yake ɗauka yana fitowa da kyau.
"Mene ne sunanka," ɗaya daga cikin mutanen ya tambayi Kwamanda, inda shi kuma ya ba da amsa da cikakken sunansa.
"Me ya sa kake zagin gwamnan Kaduna," ya ƙara tambayarsa, yayin da shi kuma Danbilki ya musanta cewa zaginsa yake yi, har ma ya yi ƙoƙarin wayar da kan mutumin game da ƴancinsa na faɗar ra'ayi a matsayinsa na ɗan Najeriya.
Daga nan ne kuma suka fara dukan sa da wani abu da ya yi kama da bulala, kamar yadda aka ji mutumin yana cewa "miƙo min bulala, abin da za ka faɗa min ke nan, abin da za ka faɗa min ke nan".
Har sai da suka tilasta masa ya durƙusa kan guyawunsa yana ba su haƙuri yayin da suke ci gaba da yi masa bulala.
Ɗaya daga cikin masu yi masa bulalar yana sanye ne da dogayen kaya kamar na jikin Kwamanda.
Jim kaɗan bayan fara ɗaukar bidiyon, an ji mutumin da ya yi ta magana tun daga farko har ƙarshe yana tambayar mai ɗaukar cewa "yana fitowa da kyau kuwa Abdul", shi kuma ya ba da amsa cewa "yana fitowa da kyau".
An ɗauki bidiyon ne a gefen hanya kuma cikin dare, ana iya jin ƙarar motoci na wucewa daga gefe.
Ƴansanda ne suka dake ni - Danbilki Kwamanda
Jim kaɗan bayan faruwar lamarin aka kai kwamanda asibiti domin duba lafiyarsa.
Daga gadon asibitin ne kuma ya yi magana cikin wani bidiyo da aka wallafa a Facebook yana zargin cewa gwamnatin Kaduna ce ta tura ƴansanda suka dake shi. Sai dai gwamnatin ta musanta zargin.
"Ƴansanda ne suka kama ni, suka saka min ankwa suna tambaya ta me ya sa nake zagin Gwamnan Kaduna Uba Sani," in ji shi, yana mai cewa: "Ka ga ke nan Uba Sani ne ya saka a yi min wannan."
Bidiyon ya nuna shatin bulala a jikinsa yana zaune a kan gadon da ya yi kama da na asibiti.
"Haka suka dinga duka na da bulala, da ƙafa, da hannu, suka yi min bidiyo. Bakin ruwa ma suka kai ni, suka ce za su jefa ni ciki," in ji shi.
Ba ni da hannu a dukan Danbilki - Uba Sani
Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin na Danbilki, inda ta ce "babu al'umma mai hankali da za ta amince da irin wannan rashin imanin".
Wata sanarwa da kakakin fadar gwamnatin Kaduna, Muhammad Lawal Shehu, ya sanya wa hannu ta ce gwamnatin Uba Sani ta kafu ne "kan doka da oda".
"Saboda haka Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin gudanar da yin cikakken bincike kan lamarin, kuma ya jajirce don gano haƙiƙanin abin da ya faru tare da tabbatar da doka ta yi aikinta kan duk wanda aka kama da laifi," a cewar sanarwar.