Amurka ta kai harin ramuwa a kan Iraqi da Syria

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kakakin majalisar tsaron Amurka, John Kirby

Amurka ta ƙaddamar da hare-hare a Iraqi da Syria domin ramuwar harin da aka kai mata da jirgi maras matuƙi, wanda ya kashe sojojin ta uku a ƙarshen makon da ya gabata.

Wasu rahotanni sun ce jiragen yaƙin Amurka sun kai hari a wasu yankuna a Gabashin Syria, inda suka kashe mayaƙa masu samun goyon bayan Iran.

Sa’oi kaɗan bayan mayar da gawarwakin sojin uku gida, an fara ƙaddamar da hare-haren ramuwa da ake tsammani tun bayan kisan su.

Tuni dai wamnatin Amurka ta ce za ta kai hare-hare cikin Iraqi da Syria domin kawar da mayaƙa masu samun goyon bayan Iran, waɗanda suka shafe watanni suna kai hari a sansanin Amurka.

Washington ta kuma faɗi ƙarara cewa ba za ta kai wa Iran hari ba, duk da cewa ta ɗorawa ƙasar alhakin bayar da makamai da dabarun kai hari ga ƙungiyoyin da ke kai hare-hare kan sojin Amurka.

Babban abin da fadar White House ke nufi da hakan shi ne kaucewa duk wani abu da zai ƙara rikita halin da ake ciki a a yankin.

Ko shakka babu, shugaba Joe Biden zai fuskanci suka daga abokan hamayyarsa, waɗanda za su ce rashin kai hari Iran kai-tsaye wata alama ce ta nuna rauni.

Abubuwan da muka sani kawo yanzu

MAP

-Amurka ta kai hari kan dakarun juyin juya-halin Iran (IRGC) da sauran ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya a Iraqi da Syria

-An yi amfani da jiragen yaƙin Amurka da dama wajen kai harin, ciki harda ƙirar 'B1 bombers' mai tafiyar dogon zango wanda ya yi takakkiya tun daga Amurka.

-An kai harin ne a sassa 7, huɗu a Syria da kuma uku a Iraqi, uinda aka yi ɓarna 85 a cikin minti 30

-Wuraren da aka kai wa harin sun haɗa da cibiyar tsare-tsaren ƙungiyoyin, da sauran maɓoyar su.

-Hare-haren dai martanin Amurka ne a kan wani harin jirgin sama maras matuƙi da aka kai wani sansanin sojin Amurka a Arewa Maso Yammacin Jordan, a ranar 28 ga watan Janairu.

-Amurka ta ce mayaƙan da Iran ke goyon baya ne suka kai harin.

-John Kirby ya ce Amurka ba ta yi magana da Iran ba tun bayan kai harin na ranar 28 ga watan Jnairu.

-Bayan harin, shugaba Biden ce ''After the attack, President Joe Biden said "Za mu mayar da martani, idan ka taɓa wani BaAmurke"