Abin da ya sa ba na shakkar Trump - Shugaban Brazil

Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, sanye da jan nekatayil da shudiyar kwat a cikin fadarsa lokacin hira da BBC.
    • Marubuci, Ione Wells
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, South America correspondent in Brasília
    • Marubuci, Leandro Prazeres
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • Lokacin karatu: Minti 6

A cikin wata ƙebantacciyar hira da BBC, shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva ya ce ba shi da wata alaƙa da shugaban Amurka, Donald Trump.

Lula ya sha sukar Trump, to amma waɗannan kalaman nasa alama ce ƙarara ta yankewar alaƙa tsakaninsa da shugaban Trump.

Duk da cewa Amurka na da alaƙar kasuwanci mai gwaɓi da Brazil, A watan Yulin da ya gabata Donald Trump ya ƙaƙaba wa kayyakin Brazil karajin kashi 50 a watan Yuli, yana mai nuni da shari'ar juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar Brazil Jair Bolsonaro na hannun damansa.

Lula ya bayyana ƙarin harajin da "bi-ta-da-ƙullin siyasa" sanna ya ce masu sayen kayayyaki a Amurka za su fuskanci tsadar kayayyakin Brazila saboda ƙarin harajin.

Ƙarin harajin da Trump ya sanar ya shafi fitar da kayyakin Brazil zuwa Amurka, kamar gahawa da nama, waɗanda Lula ya ce za su yi tsada a Amurka: ''Amurkawa ne za su ji a jikinsu kan wanna kuskure da Trump ya tafka a dangantakarsa da Brazil.''

Shugabannin biyu ba su taɓa magana baki-da baki da juna ba. Da aka tambaye shi me ya sa ba ya kira Trump a waya ko ƙoƙarin ƙulla alaƙa da shi, sai Shugaba Lula ya ce: ''Ban taɓa yunƙurin kiransa ba saboda ba ya buƙatar wata magana da mu.''

A baya Trump ya ce Lula zai iya ''kiransa a kowace lokaci.'' Amma Lula ya dage cewa jami'an gwamnatin Trump ''ba sa buƙatar magana''.

Ya shaida wa BBC cewa a jaridu ya ga labarin ƙara wa kayayyakin Brazil haraji.

Da yake magana da Trump din kuwa, ya ce shugaban na Amurka ''Ba ya isar da saƙo ta hanyar da ta dace. Kawai ya wallafa (harajin) a shafinsa na sada zumunta.

Da aka tambaye shi yadda zai bayyana alaƙarsa da takwaransa na Amurka, Lula ya ce ''babu wata alaƙa''.

'Ai shi ba shugaban duniya ba ne'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lula ya ce rashin kyakkyawar alaƙar tsakaninsa ne kawai da Trump, inda ya bayyana yadda ya gina alaƙa mai kyau tsakaninsa da tsohon shugabannin Amurka, da Firaminsitan Birtaniya da shugabannin Turai da na China da Ukraine da venezuela da ma ''duka ƙasashen duniya''.

Shugaban na Brazil ya halarci taron bikin tunawa da yaƙin duniya na biyu a Rasha cikin wannan shekara, sannan ya ƙi yanke alaƙa da Shugaba Putin.

Da aka tambaye shi tsakanin Trump da Putin wa ya fi ƙarfin alaƙa da shi, sai ya kare alaƙa da Putin, yana mai cewa alaƙar tasu ta samu asali ne tun lkacin da suka zama shugabannin ƙasashe ''a shekarun baya''.

"Bani da alaƙa da Trump saboda a lokacin da aka fara zaɓen Trump a wa'adi na biyu, ba na matsayin shugaban ƙasa. Alaƙarsa da Bolsonaro be ba ƙasar Brazil ba," a cewar Lula.

Ya kuma idan ya haɗu da Trump a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi mako mai zuwa zai gaisa da shi ''saboda ni wayayyen mutum ne'', .

Ya ƙara da cewa Trump fa shugaban Amurka ne ba sarkin duniya ba''.

A lokacin da aka tuntuɓi fadar Shugaban Amurka kan sukar shugaban da Lula ke yi, kakakin fadar ya aika wa BBC kalaman da shugaban Amurka ya yi a baya-bayan nan kan Brazil.

Toshon shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, sanye da riga mai launin ruwan ɗorawa, tsaye a cikin gidansa yana kallon kyamara, lokacin da aka ɗauki hoton ta taga.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An yanke wa tsohon shugaban Brazil, Jair Bolsonaro hukuncin ɗaurin shekara 27 a gidan yarin saboda samunsa da laifin kitsa juyin mulki.

Lula ya kuma yi magana dangane da wanda ya gada, Jair Bolsonaro, da aka samu da laifi a makon da ya gabata.

Alƙalai huɗu cikin biyar na Kotun Ƙolin Ƙasar sun samu tsohon shugaban ƙasar da laifin kitsa juyin mulki bayan shan kaye a zaɓen a hannun Lula, inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 27 a gidan yari.

Lula ya shaida wa BBC cewa Bolsonaro da waɗanda ya haɗa baki da su, sun ''cutar da ƙasar tare da kitsa juyin mulki, da kuma shirya kashe ni''.

Dangane da ɗaukaka ƙara da lauyoyin Bolsonaro suka ce za su yi, Lula ya ce yana fatan Bolsonaro zai ci gaba da ''bayyana hujjojinsi'' amma dai a yanzu ''kotu ta same shi da laifi''.

Ya kuma soki Trump da "kirkirar karya" ta hanyar iƙiarin cewa ana tsananta wa Bolsonaro tare da yin tir da abin da shugaban na Amurka ya ce rashin dimokuradiyya a Brazil.

Lula ya kuma shaida wa BBC cewa, inda ce zanga-zangar da aka gudanar a harabar majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairun 2021, a Brazil aka yi ta, ba Amurka ba, to da wataƙila Trump na cikin waɗanda ake yi wa shari'a.

A hirar mai faɗi da BBC, ya kuma yi kiran kawo sauye-sauye a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya kuma soki batun kujerun dindindin da ƙasshe biyar ke da su a kwamitin sulhu na Majalisa Dinkin Duniya -

Ya soki batun kujerun dindindin da ƙasashe biyar ke da su a kwamitin sulhu Majalisar Dinkin Duniya - mai ikon yin watsi da shawarar da aka yanke, yana mai cewa hakan kawai manyan ƙasashen duniya ne ke amfana da tsarin. waɗanda suka yi nasara a yaƙin duniya na biyu, ban da ƙasashe masu biliyoyin mutane kamar Brazil da Jamus da Indiya da Japan da kuma kasashen Afirka.

A sakamakon haka ya ce Majalisar Dinkin Duniyar ba ta da ''ƙarfin magance rikice-rikice'', kuma ƙasashen biyar masu kujerun dindindin na ɗaukar ''ɓangaranci'' game da yaƙoƙin da ake yi.

Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva da Vladimir Putin ke tafiya a cikin fadar shugaban Rasha da ke birnin Moscow suna murmushi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Mayu ne Lula ya je Moscow taron tunawa da nasarar yaƙin dunya na II

Ya ci gaba da kare kawancensa da Rasha da China - ƙasashe biyu da ba sa bin tsarin zaɓe mai inganci kuma masu tarihin cin zarafin bil'adama - yayin da ya yi kiran samar da ƙarin "dimokiradiyya" a Majalisar Dinkin Duniya.

Da yake tsokaci kan yadda Brazil ke ci gaba da sayen man Rasha, yayin da Rashar ke yaƙi a Ukraine, ya ce Brazil na ɗaya daga cikin ƙasashe na farko da suka yi Allah wadai da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, kuma "Brazil ba ta bai wa Rasha tallafi, muna sayen man fetur daga Rasha saboda muna buƙatar sayen mai kamar yadda China da Indiya da Birtaniya ko Amurka ke buƙatar sayen mai."

Ya ce da a ce Majalisar Dinkin Duniya tana "aiki" to da yaƙin Ukraine da na Gaza - wanda ya bayyana a matsayin "kisan kare dangi" - da ba su zai faru ba.

BBC ta kuma tambayi shugaba Lula game da taron kolin sayin yanayi na COP30 da za a yi a watan Nuwamba, lokacin da Brazil za ta karɓi baƙuncin shugabannin duniya a birnin Belém na Amazon.

A cikin gida, shugaban na Brazil ya fuskanci suka kan goyon bayan da ya bayar na aikin haƙar mai a kusa da bakin kogin Amazon.

Kamfanin mai na ƙasar Brazil Petrobas da wasu kamfanoni sun sayi yankuna don fara tono man, sai dai har yanzu suna jiran lasisi.

Ministar muhallinsa, Marina Silva, ta yi kakkausar suka ga shirin kuma wasu ƙungiyoyin kare hakkin jama'a na fargabar cewa zai iya janyo hatsarin malalar mai a cikin ruwan da ke kusa da Amazon.

Shugaba Lula ya dage cewa Brazil na bin doka sosai a bincikenta, kuma idan aka samu malalar mai to "Brazil za ta ɗauki alhakin hakan, kuma za ta kula da waɗanda lamarin zai shafa".

Ya ƙara da cewa yana goyon bayan duniyar da za ta yi harkoki ba tare da man fetur ba, amma "wannan lokacin bai zo ba tukuna".

"Ina son sanin duk wata ƙasa da ke shirin samar da sauyi a makamashinta ta anyar daina amfani da mai," in ji shi. Amma batun ya haifar da ce-ce-ku-ce ga masu kaɗa ƙuri'a masu tsattsauran ra'aui.

Lula, mai shekaru 79, ya ce har yanzu bai yanke shawarar sake tsayawa takara ba a zaben shugaban kasa na 2026.

Ya ce lafiyarsa da jam'iyyarsa za su tantance hakan - da kuma ko yana da dama a siyasance da kuma ko yana da damar yin nasara.

A baya-bayan nan farin jinin Lula ya ɗan ragu a ƙasar a ƙuri'un jin ra'ayin jama'a, to amma ya ɗan farfaɗo bayan da Trump ya sanya wa Brazil haraji.

A ƙarshe ya ce babban tarihin da zai bari shi ne rage yunwa da rage yawan marasa aikin yi da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na ma'aikata.