Me ya sa ƴanmatan Sweden ke ajiye aiki suna komawa matan kulle?

    • Marubuci, Maddy Savage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
    • Aiko rahoto daga, Stockholm
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sweden tana cikin ƙasashen masu ƙoƙarin samar da daidaito tsakanin mata da maza. To amma me ya sa ƴanmatan ƙasar suke bin abin da ke tashe yanzu na ajiye aiki domin komawa gida su zauna ƙarƙashin miji ko saurayi?

Vilma Larsson, mai shekara 25, wadda a da take aiki a wani shagon kayan kwalliya da wani kamfani. Amma ta daina aiki a bara domin ta koma zaman gida ba tare da yin wani aiki ba, inda ta ce yanzu ta fi samun kwanciyar hankali.

"Yanzu rayuwata ta fi ɗadi. Ba na shan wahala."

Wani saurayinta yana aikin harkokin kuɗi ne daga gida. Don haka a lokuta da yake aiki a kwamfuta, ita kuma tana wajen mutsa jiki ko wajen shan shayi ko dafa abinci. Suna zaune ne a wani ƙauye a tsakiyar Sweden, amma yanzu suna yawan tafiye-tafiye, inda yanzu sun je hutu a Cyprus.

"Duk wata yana ban albashi daga cikin kuɗin da yake samu, amma idan ina nema ƙarin kuɗi, sai in tambaye shi. Idan kuma kuɗin ya min yawa, sai in ajiye sauran," in ji Ms Larsson.

Tana bayyana yanayin rayuwarta a kafofin Instagram da YouTube da TikTok, inda take da masu bibiya 11,000. Wasu daga cikin abubuwan da ta ɗora suna samun masu so wato likes har zuwa 400,000, amma ta ce ba ta samun kuɗi daga shafukan sadarwa.

Tana amfani da “hemmaflickvän” da “hemmafru” (kalmomin Sweden da ke nufin mata masu zaman gida ba tare da aiki ba) sannan ta bayyana kanta da "soft girl" -wanda ke nufin mata masu rayuwa cikin sauƙi, kuma suke mayar da hankali kan harkokin kula da gida ba aiki ba.

Ungdomsbarometern – ƙididdigar matasa mafi girma a Sweden - ta fara bayyana waɗanda suke shiga tsarin ne a bara, sannan tsarin ya ƙara fitowa fili ne lokacin da ake tambayar matasa ƴan tsakanin 15 zuwa 24 su tsara yadda suke tunanin 2024 za ta kasance musu.

Wata ƙididdigar, wadda Ungdomsbaromatern ta fitar a Agusta ta nuna cewa tsarin ya fara zama abin sha'awa a tsakanin ƴanmata ƴanmakaranta, inda kashi 14 na ɗaliban masu shekara bakwai zuwa 14 suke ƙaunar tsarin.

"Magana ce ta fara janyewa daga tunanin zama 'shugaba mace' da muke yi na tsawon shekaru," in ji Johanna Göransson, mai bincike a cibiyar Ungdomsbarometern.

Babu takamammen adadin matan da suke barin aiki su koma zaman gida kamar Ms Larsson, amma Ms Göransson da alama ba su da yawa.

Amma tsarin na samun karɓuwa a Sweden, daga rubuce-rubucen ra'ayi a jaridu da tattauna batun a taruka da tashoshin talabijin.

Gudrun Schyman – tsohuwar shugaban cibiyar ƙwato wa mata ƴanci ta Feministiskt initiativ - ta ce tana cikin waɗanda suke tattauna batun sosai. Ta ce mata su riƙa barin domin koma ƙarƙashin mazansu "koma-baya" ne kuma "abu mai hatsari." wajen samar da daidaito.

Ta ce akwai rashin wayewa game da rayuwa a Sweden musamman kan tsare-tsaren inganta daidaito, kamar hutun aiki na haihuwa da raino da sauransu. "Ƴanmatan yanzu ba su da masaniya kan irin gwagwarmayar da aka sha domin ƙwato musu haƙƙi - ƴancin aiki da albashi da zama da ƙafafunsu."

A wani ɓangaren kuma, jam'iyyar Sweden Democrats ta Sweden ta yi na'an da tsarin.

"Yana da kyau mutane kowa ya zaɓa wa kansa yadda yake so rayuwarsa ta tafi," in ji Denice Westerberg, kakakin ɓangaren na jam'iyyar.

"Idan kuma mutum na ganin hakan ne zai fi sama kyau, shi ke nan."

"Muna rayuwa ne a ƙasar da akwai damarmakin aiki. Amma duk da haka, zai fi kyau kowa ya tsara wa kansa yadda yake so ya yi rayuwa."

Ƙasar Sweden na da tsari mai kyau na aiki - yawancin ma'aikata suna samun hutun mako shida a shekara.

Sannan kuma, binciken Ungdomsbaromatern ya gano cewa ana samun ƙaruwar yawaitar gajiya a tsakanin matasa, sannan Ms Göransson ta yi amannar cewa tsarin barin aikin na cikin ire-irensa na duniya kamar "quet quitting" wanda ke ba ma'aikata shawara su rage takura wa kan su.

Bayan haka, matasan yanzu (waɗanda aka haifa tsakanin 1997 zuwa 2012), kafofin sadardwa suna sauya yanayin rayuwarsu.

"Idan ka lura da da yadda ake gudanar da rayuwa a kafofin sadarwa a yanzu, babu batun aiki, an fi mayar da hankali kan lafiya da motsa jiki," in ji Ms Göransson.

Amma babbar abin da ke jawo hankali shi ne shin akwai rashin tsari mai kyau na samar da daidaito a wuraren aiki a ƙasar?

Sweden da Slovenia ne ƙasashen da suka fi yawan mata ma'aikata a turai, amma duk da haka matan aure suna gudanar da aikace-aikacen gida da kula da yara sama da maza.

Haka kuma su ne suka fi samun hutu iyaye, da hutun rashin lafiya. Amma duk da haka, bambancin albashi tsakanin maza da mata ya fi ƙaranci kan yawancin ƙasashen turai.

Ms Larsson - wadda take son haihuwa nan gaba - ta ce ta yanke shawarar komawa zama a gida ne saboda yadda ta ga mata manya suna fama da ƙoƙarin haɗa aiki da kula da harkokin gida.

"Mutane da dama suna fama da gajiya saboda aiki," in ji ta. "Ina nufin kowace uwa. Mahaifiyata da kakata da ƴanuwana da sauransu."

Shoka Åhrman, masaniyar tattalin arziki a babban asusun fensho a ƙasar, SPP, ta ce ba ta tunanin mata da ƴanmata da dama na Sweden za su bar aiki.

Sai dai tana aiki domin wayar da kan matan ƙasar cewa barin aiki zai shafi tattalin arzikinsu.

Ms Åhrman ta ce tana fata tattaunawa kan yadda matan suke barin aiki zai buɗe wa ƴansiyasa ido domin fahimtar cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaba domin magance matsalar daidaito.