Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Katafaren jirgin ruwan Amurka da yadda bishiyar almond ke yaɗuwa cikin hotunan Afirka
Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.
Wata na'ura ta haska sararin samaniya a yayin da Ukraine ke ƙoƙarin harbo jirage marasa matuƙa na Rasha da suka kawo mata hari.
Mutane na kallon wani katafaren jirgin ruwan Amurka wanda aka haɗa shi a 1950 da 1951.Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Alabama
Wasu iyalai ƴan gudun hijira a Congo da suka rasa matsuguninsu a yayin rikicin da ake a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo sun isa sansanin ƴan gudun hijira na Rugombo da ke Burundi.
Wani ƙaton rami da ya kasance a buɗe a tsakiyar ƙauyen Surrey ya hana mutane dawo wa gidajensu tsawon watanni.
Mutane na shan iska a ƙarƙasin bishiyar almond wadda ta yaɗu a wajen shaƙatawa da ke Quinta de los Molinos a Madrid ta Sifaniya
Jaker Ali ƴan ƙasar Bangladesh na taya abokiyar wasanta Towhid Hridoy murna bayan sun samu nasara a yayin wasan da suka yi tsakaninsu da Indiya a filin wasa na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Wani mutum a amalenke yana tuƙa ta a kan titin Phnom Penh da ke Cambodia.