Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta nuna wa Bayern Munich ƙarfinta ya kawo
Kyaftin ɗin Barcelona Raphinha ya ci kwallo uku a wasansu da Bayern Munich, wanda hakan ya bai wa ƙungiyar nasara da ci 4-1.
Da wannan nasarar, Barcelona ta kawo ƙarshen kusan shekara 10 da ta kwashe tana shan kashi a hannun Bayern.
A mintin farko na wasan Raphinha ya jefa kwallo bayan wani kakkyawan fasin da Lopez ya yi masa shi kuma ya jefa wa Manuel Neuer ita a raga.
Kyaftin ɗin Ingila Harry Kane ya rama kwallon a minti 10 da wasan, amma daga baya VAR ta ƙi amincewa da kwallon ta ce an yi satar gida.
A minti na 18 Serge Gnabry ya kwaso wa Kane kwallon a karo na biyu ya jefa ta raga kuma aka ansa.
Tsohon ɗan wasan Bayern Lewandowski ya ci wa Barcelona kwallo ta biyu ne a minti 36 da wasan yayin da Raphinha ya ƙara kwallo ta uku gabanin a juya hutun rabin lokaci.
Da dawowa daga hutun rabin lokaci Raphinha ya ci kwallo ta uku wadda ta bashi damar kammala cin kwallo uku rigis.
An riƙa yaɗa jita-jitan Barcelona za ta sayar da ɗan wasan gefen wanda ta sayo daga Leeds kan kuɗi fan miliyan 55 a 2022.
Kocin ƙungiyar Hansi Flick zai yi farin cikin yadda ɗan wasan Brazil ɗin ya ci kwallo tara cikin wasa 13 da ya buga a wannan kakar.
Barcelona na matsayi na tara a jadawalin Champions da maki shida cikin wasa uku da aka yi, yayin da ita kuma Bayern ke matsayi na 23 da maki uku, bayan rashin nasara biyu da ta yi a jere.