Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɓarnar da hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna a tashoshin nukiliyar Iran
- Marubuci, Shayan Sardarizadeh & Thomas Spencer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- Lokacin karatu: Minti 6
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna sabbin alamomi na ɓarna a titunan shiga da hanyoyin ƙaƙashin ƙasa na tashar sarrafa nukiliyar Iran da ke ƙarƙashin tsaunuka a Fordo.
Ranar 23 ga watan Yuni ne Isra'ila ta kai wa cibiyar hari, kwana guda bayan Amurka ta saki bama-bamai masu tarwatsa ginin ƙarƙashin ƙasa a wurin.
Ɓarnar da ba na gani ba a baya ta kuma bayyana a kusa da mashigar cibiyar ƙarƙashin ƙasa ta Tashar Fasahar Nukiliyar Isfahan bayan Amurka ta kai mata hari. Haka kuma akwai alamomi da ke yadda ake ta aiki don cike ramukan da hare-haren Amurka suka yi a cibiyar sarrafa yuraniyam ta Natanz.
Wasu bayanan leƙen asiri na Amurka da aka tsegunta sun bayyana tantama a kan ko hare-haren sun cimma burin ruguza cibiyoyin nukiliyar Iran na ƙarƙashin ƙasa. Rahotannin kafofin yaɗa labarai a kan hakan sun fusata Shugaba Donald Trump wanda ya mai da martani cikin ɓacin rai.
Sauran sabbin hotunan tauraron ɗan'adam sun bayyana ɓarnar da ba a gani ba a baya a wata jami'a da ke arewa maso gabashin Iran da kuma a wani yanki kusa da wani babban filin jirgin sama yamma da birnin Tehran.
Isra'ila da kuma daga bisani Amurka sun ce hare-haren na da nufin hana Iran ƙera makamin nukiliya. Iran dai ta sha musanta waɗannan zarge-zarge, inda ta dage cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne.
Sabuwar ɓarnar da aka yi a Fordo
Cibiyar sarrafa nukiliyar Fordo, da ke binne a ƙarƙashin tsaunuka a kusa da birnin Ƙum, an jefa mata bama-baman lalata gine-ginen ƙarƙashin ƙasa na Amurka ranar 22 ga watan Yuni, abin da ya haifar da manyan ramuka guda shida da ake iya gani a hotunan tauraron ɗan'adam, baya ga diddigar ƙura da ɓaraguzan da suka watsu a faɗin yankin.
Bayan kwana guda kuma, Isra'ila ta ce ta sake kai hari Fordo, inda a wannan lokaci ta far wa titunan shiga cibiyar. Hukumomin Iran daga bisani sun tabbatar da harin.
Hotunan tauraron ɗan'adam masu fitar da komai sarai da aka ɗauka ranar 24 ga watan Yuni kuma Cibiyar Maxar Technologies ta wallafa sun nuna sabbin ramuka da gine-ginen da aka lalata waɗanda ba a gan su ba bayan hare-haren Amurka.
Ana iya ganin wani sabon rami a ɗaya daga cikin titunan zuwa wata mashigar hanyar ƙarƙashin ƙasa na cibiyar wadda ke arewa maso yamma. Sannan kuma ana iya ganin aƙalla ramuka guda biyu a kusa da wata hanyar ƙarƙashin ƙasa a gefen kudancin cibiyar.
Hotunan Maxar sun kuma nuna wata tasha da aka lalata a arewacin cibiyar, tare da ramukan da hare-hare ta sama suka haddasa, ga kuma burbuɗin ƙara a dai wannan yankin.
Ana kuma iya ganin ƙarin wani sabon rami da kuma alamun ƙonewa a tsakiyar wani titi a gefen yamma na cibiyar.
An yi imani an kai hare-haren ne da nufin sanya zuwa cibiyar da gyara ta, su zama da matuƙar wahala.
Tarin farar ƙurar da ake iya gani a wasu hotunan tauraron ɗan'adam mai yiwuwa alama ce ta girman ɓarnar da aka yi a can cikin ƙarƙashin ƙasa, kamar yadda masharhanta suka yi imani.
"Ƙarfin fashewa a can cikin ƙarƙashin ƙasa ta haddasa tarwatsewar kankare kamar yadda aka bayyana, abin da zai iya janyo gagarumar ɓarna ga gine-ginen ƙarƙashin ƙasa," in ji Trevor Lawrence, shugaban Cibiyar Fasahar Makamashi a Jami'ar Cranfield kuma ƙwararre a kan illar da fashewar bam kan haifar.
"La'akari da sarƙaƙiyar fasalin waɗannan gine-gine, gagarumar ɓarna idan ta faru, ba abu ne da mai yiwuwa za a iya gyarawa ba cikin taƙaitaccen lokaci."
Lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa a tashar Isfahan
Cibiyar Fasahar Sarrafa Nukiliya ta Isfahan da ke kudu maso gabashin Isfahan ita ce tashar binciken makamashin nukiliya mafi girma ta Iran. Tana kuma ƙunshe da tashar tace makamashin yuraniyam da ke gyara makamashin daga siffarsa ta asali a mayar da shi zuwa wani abu da za a iya ingantawa a cibiyoyin sarrafa makamashin ƙasar biyu na Natanz da Fordo.
Isra'ila dai kai farmaki har sau biyu a cibiyar. Kafin kuma Amurka ta jefa bama-baman tarwatsa gine-ginen ƙarƙashin ƙasa ranar 22 ga watan Yuni, lamarin da ya haddasa ƙarin gagarumin lahani a faɗin cibiyar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya kare ingancin hare-haren da Amurka ta kai wa Iran, ga alama kuma yana bayani ne a kan cibiyar tace yuraniyam ta Isfahan.
"Ba za ka iya yin makamin nukiliya ba idan babu cibiyar tace yuraniyam, har yanzu ba mu iya gano inda take ba, da inda take can baya a kan taswira - saboda gaba ɗaya komai ya koma baƙi ƙirin kawai... babu ita....ta shafe daga banƙasa."
An ɗauki hotunan gaba ɗayan cibiyar a na'urorin tauraron ɗan'adam na Maxar kuma an yi gagarumar ɓarna a ɗumbin gine-ginenta. Ɗaya daga cikin gine-gine, wanda a baya ake bayyana sunansa da Cibiyar Harkokin Kimiyya da Tsaron Ƙasashen Duniya kuma babban ginin tace yuraniyam, an yi masa raga-raga.
Ana kuma iya ganin ƙarin ɓarna a ƙarin hanyoyin shiga na ƙarƙashin ƙasa a wani hoto.
Ƙwararru daga kamfanin nazarin bayanan leƙen asiri na Maiar sun ƙididdige cewa mai yiwuwa ne hanyoyin shigar sun fuskanci "matsakaicin" lahani a gininsu. Sun lura da ƙonewa a gefen mashigun amma kuma ba su ga wata ɓarna a jikin kankaren da ke kusa ba, sannan kuma ba a ga ruftawar ƙasa a saman mashigun ba.
Ƙoƙarin baya da Iran ta yi na ƙarfafa mashigar cibiyoyin ta hanyar jibge tarin ƙasa mai yiwuwa ya rage tasirin hare-haren na Amurka.
"An ga wata hanyar ƙarƙashin ƙasa a cibiyar Isfahan kamar ta fuskanci fashewar wani abu daga ciki da kuma gobara, la'akari da baƙaƙen ɓaraguzai da suka tarwatsu a wajen hanyar. Idan ko haka ne, sai an kwashe shekaru kafin a iya gyarawa," a cewar Mark Cancian, daga Cibiyar Tsare-tsare da Nazarin Harkokin Ƙasashen Duniya.
"A ɓangare ɗaya, kwaranyewar launi a jikin ginin mai yiwuwa ya faru ne sanadin fashewar makamin shi kansa amma ba saboda ratsawar makamin zuwa cikin ginin ba. Ɗaya hanyar shigar ita ma an ga kamar yashi da ƙasa duk sun turbuɗe ta. Idan haka ne kuwa, ana iya buɗe ta a cikin 'yan makonni."
An rufe ramuka a Natanz
A lokacin yaƙin Isra'ila da Amurka duk sun kai hare-hare kan Natanz, tashar sarrafa makamashin yuraniyam ɗin Iran ta farko.
Hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar 22 ga watan Yuni, jim kaɗan bayan hare-haren Amurka sun nuna ramuka guda biyu a wani makeken yanki na tashar nukiliyar. An yi imani ramukan suna saman gine-ginen ƙarƙashin ƙasa da ke ƙunshe da zaurukan da na'urar makamashin nukiliya take, mai tace makamashin yuraniyam.
Wani sabon hoto, da aka ɗauka ranar 24 ga watan Yuni, ya nuna ramukan da tuni aka rufe da ƙasa, waɗanda mai yiwuwa ke nuna ana ci gaba da aiki don gyara ɓarnar da aka yi wa tashar.
"Yi tunanin abin da za ka yi mana idan rufin gidanka ne ya huje," in ji David Albright, " kuma mai yiwuwa suna so aƙalla su kafa wata garkuwa ga wani bam mai ratsa ƙarƙashin ƙasa da za a iya sake harbo shi wurin."
Filin Jirgin Sama na Mehrabad
Wani muhimmin wuri da Isra'ila ta kai wa hare-hare a lokacin yaƙin shi ne filin jirgin sama na Mehrabad, a yamma da birnin Tehran. Bidiyo da hotunan da BBC Verify ta haƙƙaƙe ingancinsu sun nuna yadda Isra'ila ta yi masa luguden bam a karo da dama.
Filin jirgin da ya taɓa zama na zirga-zirgar ƙasashen duniya, yanzu mafi yawa yana karɓar jiragen sama masu jigila a cikin gida ne kawai.
Isra'ila ta raba hotunan filin jirgin tana kai farmaki kan wasu jiragen yaƙin F-14 ƙirar Tomcat, waɗanda basaraken ƙasar Shah ya saya kafin juyin juya halin Musulunci na 1979.
Wani hoto ma da aka ɗauka a shiyyar masana'antu a kudu da titin tashin jirgin, ya nuna ɓarnar da aka yi wa gine-gine birjik.
Wani hoto kuma ya nuna wani sashe a yamma da titin saukar jirgi, inda aka ga aƙalla wani gidan ajiyar kaya gaba ɗaya an lalata.
Sashen na ƙunshe da kamfanonin harkokin sararin samaniya da dama masu alaƙa da masana'antun tsaron Iran.