Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitar da ɗantakarar gwamna a Kano a APC a yanzu zai haifar da rarrabuwar kai — Ganduje
Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najerya, kuma jagoran jam'iyyar APC mai Mulki a jihar, ya gargadi masu fitowa suna ayyana wani mutum a jam'iyyar da cewa shi aka amince ya yi takarar gwamnan jihar a babban zaben 2027.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba da wasu za su rika fitowa suna cewa ga wanda zai yi takara ba saboda a cewarsa hakan zai sake haifar da rarrabuwar kai a jam'iyyarsu ta APC.
Tun da farko dai wasu manyan 'yan jam'iyyar APCn ne a Kano suka amince da cewa sanata Barau Jibrin, shi ne zai yi takarar gwamna a jihar a 2027.
Ga alama dai wannan dambarwa ta ayyana sanata Barau Jibrin, a matsayin wanda wa su ke so ya yi wa jam'iyyar APC takarar gwamnan jihar na ci gaba da daukar hankali, musamman bayan da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya takawa maso fitowa suna nuna goyon baya ga wani mutum guda birki.
Kuma tun kafin Gandujen ya yi wannan kakkausan gargadi wani daga cikin wadanda suka ayyana sanata Barau din a matsayin wanda suke bukatar ya yi takara wato Baffa Takai, ya fito ya ce ya janye wannan kira tare da bai wa 'yan jam'iyyar hakuri.
Dakta Ganduje, ya shaida wa BBC cewa ya kamata mutane su daina zuguguta 'yan takara ace wannan yafi wannan ko wannan baya yin wannan, to irin wannan babu abin da zai kawo mana sai rarrabuwar kai a jam'iyya.
Ya ce,"A bari lokacin fitar da 'yan takara ya yi sai a fitar da wadanda ake gani sun cancanta, ba wai mun ce ba za a tsayar da wanda ya cancanta ba, a'a a bari lokaci ya yi."
Bayanai dai na cewa a baya-bayan nan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APCn a Kano, mahalarta taron sun ce suna sauraron umarnin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne kasancewar shi ne zai saita alkiblar inda za a dosa, amma duk da haka an yi ta samun wadanda suka rika fitowa suna ayyana mutumin da suke ganin shi suke so ya tsaya takarar gwamna, kuma har yanzu babu tabbas ko taka birkin da Ganduje ya yi wa masu ayyana gwanayen na su dadi.
Tun da farko dai wani ɓangare na tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jam'iyyar ta APC a Kano ne ya amince da cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin shi ne zai yi takarar gwamnan jihar a 2027.