Tun kafin na sauka daga jirgi aka kama ni - Fulanin da DSS ta kama bayan aikin Hajji

Asalin hoton, Getty Images
Wasu mutane 'yan ƙabilar Fulani da hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta tsare sun bayyana farin ciki da ɓacin rai bayan sakin su da ta yi ranar Alhamis.
DSS ta kama mutanen uku ne yayin da suke sauka a Najeriya daga aikin Hajji a watan Yunin 2024 bisa zarge-zarge hannunsu a ayyukan garkuwa da mutane a arewacin ƙasar.
Yayin wani taron manema labarai a hedikwatarta da ke Abuja babban birnin Najeriya, DSS ta gabatar da Rabiu Alhaji Bello, da Umar Ibrahim, da Bammo Jajo Sarki duka 'yan jihar Kwara da ke tsakiyar ƙasar.
Hukumar ta ce ta kammala bincike kan su kuma ba ta same su da laifin komai ba, abin da ya sa ta bai wa kowannensu kyautar naira miliyan ɗaya.
Ƙungiyoyin Fulani sun sha kokawa kan kama mutanensu game da zargin garkuwa da mutane da kuma ta'adanci ba tare da wata hujja ba, suna masu cewa abin takaici ne.
Wannan ne karo na biyu da DSS ke sakin tsirarrun 'yan ƙabilar Fulani a 2025 bayan dawowarsu daga Hajji, bayan ta saki bakwai a watan Oktoban da ya gabata tare da ba su miliyan ɗaya-ɗaya.
Yayin sakin mutanen ranar Alhamis, babu ko ɗaya daga cikin jami'an hukumar DSS ɗin, wada ke gudanar da mafi yawan ayyukanta a ɓoye, da ya yi magana da 'yanjarida.
'Tun kafin na sauka daga jirgi aka kama ni'
Mutanen sun ce sun shafe tsawon lokaci suna jiran samun ƴanci amma sai yanzu hakan ta tabbata.
Umar Ibrahim, ɗaya daga cikin mutanen da suka kuɓuta, ya faɗa wa BBC cewa "tun kafin na gama sauka daga jirgi aka riƙe ni".
Rabiu Alhaji Bello ya ce a birnin Ilori na jihar Kwara aka fara tsare su.
"Mun yi kwana guda a Ilori, sai kuma aka ɗauko mu zuwa nan [Abuja]," in ji shi. Ya ƙara da cewa ba su fuskanci wata azabtarwa ba yayin tambayoyi da kuma bincike.
"Suna ma faɗa mana cewa iya abin da ka sani za ka faɗa mana, saboda haka ba su ma tilasta mana mu faɗi abin da ba mu sani ba," a cewarsa.
Shi kuwa Bammo Jajo ya bayyana irin farin cikin da ya ji lokacin da aka faɗa masa cewa ba shi da laifi.
"Na dinga tuna ɗan'uwana da mahaifina."
Umar Usman ɗan'uwan mutanen ne, kuma ya faɗa BBC irin faɗi-tashin da suka yi wajen kuɓutar da ƴan'uwan nasa.
"Mun shiga damuwa tare da 'yan'uwa, saboda dukkansu suna da mata da 'ya'ya. Mun yi ta bibiya, sai daga baya muka gano cewa suna hannun 'yansandan farin kaya," kamar yadda ya bayyana.
Ya ƙara da cewa bana mutanen ba su samu damar yin noma ba saboda dukkansu ba su gida. "Yanzu daminar bana ta ƙare, sai dai a yi shirin baɗi."
To ko me Bammo Jajo zai yi da zarar ya saka ƙafarsa a wajen magarƙama?
"Yau [Alhamis] idan na fara bacci ƙila sai an tashe ni," kamar yadda ya bayyana.










