Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da Saudiyya, wane alfanu za ta samu?

Asalin hoton, others
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Masana harkokin alaƙa tsakanin ƙasashe sun bayyana yarjejeniyar ƙawancen tsaro da Najeriya ta ƙulla da Saudiyya a matsayin mai muhimmanci, kodayake suna cewa ba zai yiwu Najeriya ta dogara da ita ba wajen shawo kan matsalolin tsaron da take fama da su.
A ranar Laraba ne ƙasashen biyu suka saka hannu kan yarjejeniyar domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da ayyukan soja tsakaninsu.
Wata sanarwa daga Ma'aikatar Yaɗa Labarai ta Najeriya ta ce Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ne ya wakilci Najeriya, yayin da Mataimakin Ministan Tsaro Dr. Khaled H. Al-Biyari ya wakilci Saudiyya.
"Ƙulla wannan yarjejeniya muhimmin mataki ne," a cewar Matawalle. "Ta kwana biyu ana tsara ta kuma amincewa da ita zai ƙarfafa ayyukan tsaro a Najeriya da kuma kyautata ayyukan dakarunmu."
Yarjejeniyar na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar barazanar tsaro iri-iri, ciki har da satar ɗaruruwan ɗalibai a jihohin Kebbi da Neja, da kuma hare-hare kan wuraren ibada da 'yanfashin daji ke yawan kaiwa a arewa maso yammacin ƙasar.
A gefe guda kuma ga hare-haren ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi na Boko Haram da Iswap, waɗanda ke alaƙanta kansu da tafarkin Sunna a addinin Musulunci, koyarwar da ake yi wa Saudiyya kallo a matsayin cibiya.
Me yarjejeniyar ta ƙunsa?

Asalin hoton, Saudi Ministry of Defense
Yarjejeniyar ta tanadi cewa za a fara aiwatar da ita tsawon shekara biyar kafin a sake dubawa da kuma tsawaita ta tsawon wasu shekaru biyar, kamar yadda sanarwar gwamnatin Najeriya ta bayyana.
Kazalika, kowace ƙasa za ta iya fita daga yarjejeniyar duk lokacin da take so bayan ta bayar da wa'adin wata uku a rubuce.
"Daga cikin abubuwan da ta ƙunsa akwai haɗa kai a fannin tsaro da ayyukan soja da suka haɗa da bayar da horo, yin atasaye na haɗin gwiwa, bayar da taimakon aiki, musayar bayanan sirri, jigila, da kuma ayyukan da za a daddale a kansu," a cewar sanarwar.
Saudiyya ta shiga sawun ƙasashe kamar Amurka da Ingila da Faransa da kuma maƙwabtanta da suka ƙulla irin wannan yarjejeniyar.
"Muhimmancin wannan yarjejeniyar zai fi yawa a fannin yaƙi da ta'addanci saboda kowa ya san ta'addanci na samun tallafi daga wurare da yawa, kuma Saudiyya na ɗaya daga cikin ƙasashe na kan gaba wajen yaƙi da shi," kamar yadda Dr. Riyauddeen Zubairu Maitama na Jami'ar Bayero ya shaida wa BBC.
Ta yaya Najeriya za ta amfana?
Akwai hanyoyi da yawa da ɓangarorin biyu za su amfana ta hanyar yarjejeniyar.
Sai dai Dr. Riyauddeen ya ce Najeriya ce za ta fi amfana saboda yaƙi da ta'addanci ya zama a duniya a yanzu.
"Saudiyya ta ƙware wajen tattara bayanan sirri kan ta'addanci, musamman wajen gudanar da kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta'addanci, har ma da makamai," in ji shi.
Ma'aikatar Yaɗa Labarai ta Najeriya ta zayyana ɓangarori uku da Najeriya za ta amfana daga yarjejeniyar kamar haka:
- Kaifafa ƙwarewa da bayar da horo: Samun damar ƙara ƙwarewa a fannin ilimin tsaro, da musayar ƙwararru tsakanin ƙasashen domin inganta ƙwarewar dakarun Najeriya
- Kyautata aiki: Yin atasayen soja tare wanda zai taimaka wa dakarun Najeriya kasancewa cikin shiri
- Yaƙi da ta'addanci da tsaron cikin gida: Kyautata aiki tare a yaƙi da ta'addanci, da musayar bayanan sirri domin daƙile ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da muggan masu aikata laifi
'Ba zai yiwu Najeriya ta dogara da Saudiyya ba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saudiyya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da kayan aikin soja na zamani a duniya. Sai dai akasari tana sayensu ne daga Amurka da ƙasashen Yamma.
A cewar alƙaluma daga hukumar samar da kayayyakin soja a cikin gida ta General Authority for Military Industries, yawan kayan aikin soja da Saudiyya ke samarwa a ƙasar bai wuce kashi 4 cikin 100 ba a 2018, kafin ya koma 24.89 zuwa ƙarshen 2024.
Hakan na nufin ta dogara da ƙasashen waje, musamman Amurka, wajen sayen kashi 76 cikin 100 na makaman da take amfani.
Wannan dalilin ya sa Dr. Riyauddeen yake ganin Najeriya ba za iya dogara da Saudiyya ba wajen samun kayan aikin da za su taimaka wajen daƙile matsalar tsaro.
"Idan magana ake yi ta samun kayayyakin yaƙi na zamani, Saudiyya ba ƙasa ce da za a dogara da ita ba saboda ita ma ba ta dogara da kanta ba," kamar yadda ya bayyana.
"Ta dogara ne da Amurka wajen samun makamai, da horo, da kayan aiki. Wasu makaman da take da su ma ba ta iya sarrafa su sai dai 'yan kwangila ne ke taimka mata."
Sai dai masanin ya ce Najeriya za ta fi amfanuwa ta fannin jari ko kuɗin da Saudiyya za ta zuba a fannin tsaron ƙasar.
"Idan har yarjejeniyar ta ƙunshi wannan, to Najeriya za ta fi amfana a fannin ƙere-ƙeren makamai da kuɗin da Saudiyya za ta zuba wajen samar da su a Najeriya, saboda ƙasa ce mai arziki sosai."










