Jamus ta kawar da kai daga gargaɗin Saudiyya kan harin Magdeburg

Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a lokacin da ya haɗu da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Riyadh, babban birnin Saudi Arabiya a ranar 23 ga watan Oktoban 2024.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hoton Yarima mai jiran gado a Riyadh lokacin wata ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a watan Oktoba.
    • Marubuci, Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Security correspondent, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Na samu labarin cewa a yanzu haka hukumomin Saudiya sun duƙufa wajen tattara duk bayanan da su ke da shi kan wanda ake zargi da kashe mutane a kasuwar Magdeburg, Taleb al-Abdulmohsen, kuma su aika wa masu gudanar da bincike a Jamus.

Tun a baya, ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen waje ta Saudiya ta gargadi gwamnatin Jamus kan tsattsauran ra'ayin al-Abdulmohsen.

Ta ce ta aike da wasiƙun gargaɗi har karo huɗu, uku daga ciki zuwa hukumomin tattara bayanan sirri na Jamus, ɗaya kuma zuwa ma'aikatar harkokin waje a Berlin. Sai dai ma'aikatar ta ce ba su mayar da amsa kan wasiƙun ba.

Wani ɓangare daga cikin dalilin hakan zai iya zama saboda a shekarar 2016, Jamus ta bai wa Taleb al-Abdulmohsen mafaka, shekara guda bayan tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta buɗe iyakokin ƙasar domin bai wa baƙin haure fiye da miliyan ɗaya daga gabas ta tsakiya damar shiga ƙasar, kuma shekara 10 bayan al-Abdulmohsen ya fara zama a Jamus.

A matsayinsa na mutumin da ya fito daga ƙasar da addinin musulunci ne kawai addinin da ake yi a bayyane, al-Abdulmohsen ya kasance daban.

Ya juya wa musulunci baya, wanda hakan ya sa mutane ke kallon sa a matsayin ɗan bidi'a.

An haife shi a birnin Hofuf mai cike da bishiyoyin dabino a shekarar 1974, kuma bayanai ƙalilan aka sani a kan rayuwarsa ta baya kafin ya yanke hukuncin barin Saudiyya ya koma Turai a lokacin yana da shekara 32.

A shafukan sada zumunta, musamman a shafin Twitter wanda a yanzu ya koma X, yana bayyana kansa a matsayin likitan ƙwaƙwalwa kuma wanda ya kafa ƙungiyar kare haƙƙin ƴan ƙasar Saudiyya mai taken @SaudiExMuslims.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya kuma samar da wani shafin yanar gizo domin taimakawa mata ƴan ƙasar Saudiyya barin ƙasarsu zuwa Turai.

Ƴan Saudiya na cewa yana safarar mutane, kuma ana ganin masu bincike a ma'aikatar harkokin cikin gida na da bayanai da dama a kansa.

A shekarun baya, an samu rahoton cewa gwamnatin Saudiyya na sanya ido kan ƴan ƙasar masu adawa da tsarin gwamnati da ke Canada, Amurka da Jamus.

Babu shakka hukumomin Jamus, na tarayya da na jiha, sun tafka babban kuskure kan kawar da kai daga wasu muhimman batutuwa game da al-Abdulmohsen.

Ko ma mene ne dalilinsu na ƙin amsa wasiƙun gargadi kan tsattsauran ra'ayin shi, kamar yadda Saudiyya ta yi iƙirari, dama ya kasance mai haɗari ga ƙasar da ta ɗauke shi.

A gefe guda kuma akwai gazawarsu na rufewa, ko kuma aƙalla kula da hanyoyin wucingadi da ke kai wa zuwa kasuwar Magdeburg waɗanda ake zargin su ne suka ba shi damar bi ta kan mutane da motarsa ƙirar BMW.

Sai dai hukumomin Jamus din sun kare tsarin kasuwar, kuma sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan rayurwarsa ta baya.

Amma wani abun dubawa shi ne duk da ana kallon Saudiyya a matsayin abokiyar ƙasashen yamma, amma tana da tarihin tauye haƙƙin ƴanadam.

Har zuwa watan Yunin 2018, an haramta wa matan Saudiyya tuƙin mota, kuma waɗanda suka fito fili suka yi kira da a ɗage haramcin kafin lokacin, an gurfanar da su kuma an kai su gidan yari.

Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, wanda shekarunsa ba su wuce 30 ba, na da farin jini sosai a ƙasarsa.

Wani mutum ya na makoki a wurin zaman makoki da ke gaban cocin St John bayan wani mota ya bi ta kan mutane a kasuwar krisimeti a Magdeburg da ke Jamus a ranar 22 ga watan Disemba 2024.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane na ta barin furanni domin jaje ga wadanda harin ranar Juma'a da akayi a kasuwar Krismeti da ke Magdeburg a Jamus ya rutsa da su.

Bayan shugabannin ƙasashen yamma sun nisanta kansu daga shi sakamakon zargin sa da ake yi da hannu a kisan Jamal Kashoggi a shekarar 2018, wanda Yariman mai jiran gado ya musanta, a ƙasarsa, har yanzu tauraronsa na ci gaba da haskawa.

A ƙarƙashin mulkinsa, rayuwa a ƙasar ta sauya, a yanzu maza da mata na iya hulɗa ba takura, kuma ana sake buɗe gidajen kallo, ana kuma shirya manyan tarukan wasanni da na nishaɗi, har ma da bukukuwan da mawaƙa daga ƙasashen yamma kamar David Guetta da Black Eyed Peas ke halarta.

Sai dai kuma har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da ƴancin al'ummar ƙasar ta Saudiyya.

Duk da cewa rayuwa a ƙasar ta bunƙasa, a gefe guda kuma ana ci gaba da daƙile duk wani abu da yayi kama da ƙarin samun ƴancin siyasa ko na addini.

Ana yanke wa mutane hukuncin zaman gidan yari na shekara goma ko fiye saboda rubutu a shafin twitter (X).

Babu wanda ke da damar yin tambaya kan yadda ake mulki a ƙasar.

Wannan ne ya sa ake ganin Jamus ta ƙyale Taleb al-Abdulmohsen.