Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jamus ta kawar da kai daga gargaɗin Saudiyya kan harin Magdeburg
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Security correspondent, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Na samu labarin cewa a yanzu haka hukumomin Saudiya sun duƙufa wajen tattara duk bayanan da su ke da shi kan wanda ake zargi da kashe mutane a kasuwar Magdeburg, Taleb al-Abdulmohsen, kuma su aika wa masu gudanar da bincike a Jamus.
Tun a baya, ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen waje ta Saudiya ta gargadi gwamnatin Jamus kan tsattsauran ra'ayin al-Abdulmohsen.
Ta ce ta aike da wasiƙun gargaɗi har karo huɗu, uku daga ciki zuwa hukumomin tattara bayanan sirri na Jamus, ɗaya kuma zuwa ma'aikatar harkokin waje a Berlin. Sai dai ma'aikatar ta ce ba su mayar da amsa kan wasiƙun ba.
Wani ɓangare daga cikin dalilin hakan zai iya zama saboda a shekarar 2016, Jamus ta bai wa Taleb al-Abdulmohsen mafaka, shekara guda bayan tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta buɗe iyakokin ƙasar domin bai wa baƙin haure fiye da miliyan ɗaya daga gabas ta tsakiya damar shiga ƙasar, kuma shekara 10 bayan al-Abdulmohsen ya fara zama a Jamus.
A matsayinsa na mutumin da ya fito daga ƙasar da addinin musulunci ne kawai addinin da ake yi a bayyane, al-Abdulmohsen ya kasance daban.
Ya juya wa musulunci baya, wanda hakan ya sa mutane ke kallon sa a matsayin ɗan bidi'a.
An haife shi a birnin Hofuf mai cike da bishiyoyin dabino a shekarar 1974, kuma bayanai ƙalilan aka sani a kan rayuwarsa ta baya kafin ya yanke hukuncin barin Saudiyya ya koma Turai a lokacin yana da shekara 32.
A shafukan sada zumunta, musamman a shafin Twitter wanda a yanzu ya koma X, yana bayyana kansa a matsayin likitan ƙwaƙwalwa kuma wanda ya kafa ƙungiyar kare haƙƙin ƴan ƙasar Saudiyya mai taken @SaudiExMuslims.
Ya kuma samar da wani shafin yanar gizo domin taimakawa mata ƴan ƙasar Saudiyya barin ƙasarsu zuwa Turai.
Ƴan Saudiya na cewa yana safarar mutane, kuma ana ganin masu bincike a ma'aikatar harkokin cikin gida na da bayanai da dama a kansa.
A shekarun baya, an samu rahoton cewa gwamnatin Saudiyya na sanya ido kan ƴan ƙasar masu adawa da tsarin gwamnati da ke Canada, Amurka da Jamus.
Babu shakka hukumomin Jamus, na tarayya da na jiha, sun tafka babban kuskure kan kawar da kai daga wasu muhimman batutuwa game da al-Abdulmohsen.
Ko ma mene ne dalilinsu na ƙin amsa wasiƙun gargadi kan tsattsauran ra'ayin shi, kamar yadda Saudiyya ta yi iƙirari, dama ya kasance mai haɗari ga ƙasar da ta ɗauke shi.
A gefe guda kuma akwai gazawarsu na rufewa, ko kuma aƙalla kula da hanyoyin wucingadi da ke kai wa zuwa kasuwar Magdeburg waɗanda ake zargin su ne suka ba shi damar bi ta kan mutane da motarsa ƙirar BMW.
Sai dai hukumomin Jamus din sun kare tsarin kasuwar, kuma sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan rayurwarsa ta baya.
Amma wani abun dubawa shi ne duk da ana kallon Saudiyya a matsayin abokiyar ƙasashen yamma, amma tana da tarihin tauye haƙƙin ƴanadam.
Har zuwa watan Yunin 2018, an haramta wa matan Saudiyya tuƙin mota, kuma waɗanda suka fito fili suka yi kira da a ɗage haramcin kafin lokacin, an gurfanar da su kuma an kai su gidan yari.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, wanda shekarunsa ba su wuce 30 ba, na da farin jini sosai a ƙasarsa.
Bayan shugabannin ƙasashen yamma sun nisanta kansu daga shi sakamakon zargin sa da ake yi da hannu a kisan Jamal Kashoggi a shekarar 2018, wanda Yariman mai jiran gado ya musanta, a ƙasarsa, har yanzu tauraronsa na ci gaba da haskawa.
A ƙarƙashin mulkinsa, rayuwa a ƙasar ta sauya, a yanzu maza da mata na iya hulɗa ba takura, kuma ana sake buɗe gidajen kallo, ana kuma shirya manyan tarukan wasanni da na nishaɗi, har ma da bukukuwan da mawaƙa daga ƙasashen yamma kamar David Guetta da Black Eyed Peas ke halarta.
Sai dai kuma har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da ƴancin al'ummar ƙasar ta Saudiyya.
Duk da cewa rayuwa a ƙasar ta bunƙasa, a gefe guda kuma ana ci gaba da daƙile duk wani abu da yayi kama da ƙarin samun ƴancin siyasa ko na addini.
Ana yanke wa mutane hukuncin zaman gidan yari na shekara goma ko fiye saboda rubutu a shafin twitter (X).
Babu wanda ke da damar yin tambaya kan yadda ake mulki a ƙasar.
Wannan ne ya sa ake ganin Jamus ta ƙyale Taleb al-Abdulmohsen.