Ko duniya na fuskantar durƙushewar tattalin arziki?

Wata mata sanye da rigar sanyi yayin da take duba abin da za ta saya cikin wani kantin sayar da kayyaki.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Simon Jack
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business editor, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Ƙarin harajin baya-bayan nan da Shugaban Trump na Amurka, ya yi wa kayayyakin ƙasashen duniya da ke shiga ƙasar ya haifar da karyewar hannayen jari a faɗin duniya, to amma hakan na nufin duniya na fuskantar durƙushewar tattalin arziki?

Abu na farko da ya kamata a fahimta shi ne abin da ke faruwa a kasuwar hannayen jari ba daidai yake da abin dake faruwa a fannin tattalin arziki ba.

Faɗuwar darajar hannayen jari ba koyaushe yake nufin tattalin arziki ya shiga garari ba.

Amma a wasu lokutan yana janyo hakan.

Gagarumar faɗuwar darajar hannayen jari, irin wannan na nufin za a samu babban tarnaƙi a ribar da kamfanoni za su samu a gaba, wanda kuma hakan zai shafi kasuwar hada-hadar hannayen jari ta duniya.

Abin da kasuwannin hannayen jari ke hasashe shi ne ƙarin harajin na nufin farashin kayyaki zai ƙaru, kuma riba za ta ragu.

To amma hakan ba yana nufin za a samu durƙushewar tattalin arziki ba, to sai dai akwai damar samun hakan idan aka kwatanta da kafin Trump ya ayyana ƙarin harajin da ba a taɓa yin irinsa ba cikin ƙarni guda.

Durƙushewar tattalin arziki na samuwa ne idan kuɗin da mutane da gwamnati ke kashewa suka ragu, sannan abubuwan da ƙasa ke fitarwa suka ci gaba da raguwa har tsawon wata shida.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsakanin watan Oktoba da Disamban shekarar da ta gabata, tattalin arzikin Birtaniya ya yi ƴar ƙaramar ƙaruwa da kashi 0.1 cikin 100, kuma alƙaluman wata-wata na baya-bayan nan ya nuna irin wannan ƙaruwa a watan Janairun shekarar da muke ciki.

A ranar Juma'ar nan ne za a fitar da ƙiyasin yadda tattalin arzikin ƙasar ya gudana a watan Fabrairu.

Don haka har yanzu ba za mu iya tabbatar da ma'anar durƙushewar tattalin arziki kan ƙasar ba.

To amma yawaitar faɗuwar darajar hannayen jari da ake samu a baya-bayan nan na matuƙar tayar da hankali.

Ana yi wa bankuna kallon jakadun tattalin arzikin, a matsayinsu na ɗaya daga cikin manyan kasuwannin da ake auna tattalin arziki da su, wani babban ma'aikacin wani banki ya shaida wa BBC cewa ''Abin da ke tayar masa da hankali shi ne faɗuwar jarin bankuna.''

HSBC da Standard Chartered - waɗanda ke aiki a wasu ɓangarorin kasuwancin ƙasashen Yammaci da Gashin duniya, dukkansu sun samu raguwar kashi 10, kafin daga baya su farfaɗo.

Wata alamar kuma a kasuwannin da ake sayar da kayyaki ake ganinta ba ta hannayen jari ba.

Ana kallon farashin ma'adinai da man fetur a matsayin wani ma'auni na tattalin arzikin duniya.

Kuma duka farashinsu ya sauka da kashi 15, tun bayan da Trump ya ayyana matakin ƙarin harajin nasa.

An samu lokutan da duniya ta fuskanci durƙushewar tattalin arziki.

A shekarun 1930, duniya ta shiga matsalolin kuɗi da aka yi wa laƙabi da ''Great Financial Crisis'' da kuma razanin da aka shiga kan wata annoba, duka waɗannan misalai ne na lokutan da duniya ta shiga manyan matsalolin durƙushewar tattalin arziki.

Har yanzu ana ganin ba zai yiwu a samu irin abin da aka gani a baya ba, amma akwai yiwuwar koma-bayan tattalin arziki a Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai kamar yadda wasu masu sharhi suka yi hasashe.

A gefe guda ministar kuɗin Birtaniya, Rachel Reeves ta ce abin da gwamnati ke kashewa kan rance zai iya ƙaruwa zuwa fam biliyan biyar ko shida a shekara, yayin da masu zuba jari ke tururuwa zuwa ƙasar saboda sauƙaƙan matakan gwamnatin ƙasar.

Amma za a fi samun koma-baya sakamakon ƙarin harajin da gwamnati za ta saka.