Su wane ne masu aƙidar Alawi na Syria kuma me ya sa ake kai masu hari?

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban riƙon-ƙwarya a Siriya, Ahmad al-Sharaa, ya yi kira kan haɗin kai kasancewar ana ci gaba da yaƙi da kashe-kashen ramuwar gayya a yankunan da ake gani na magoya bayan hamɓararren shugaban ƙasar Bashar al-Assad.

Ya yi kiran ne sakamakon kwanakin da aka shafe ana rikici inda ake zargin dakarun sabuwar gwamnati da kashe ɗaruruwan farar hula daga al'ummar Alawi waɗanda suka kasance tsiraru.

Masu sharhi sun yi hasashen cewa za a iya samun tashin-tashina bayan kawar da gwamnatin Assad a shekarar da ta gabata. Su wane ne ƴan Alawi kuma mece ce aƙidarsu? Sannan me ya sa ake kai wa al'ummar hari a yanzu?

Tarihin muzgunawa da siyasa

Ƴan ɗarikar Alawi, wani ɓangare ne na mabiya Shi'a, kuma ɗariƙar ta ɓulla a Siriya a ƙarni na 9 zuwa 10.

Alawiyyun na nufin "mabiya Ali" - wanda ɗan'uwa kuma suruki ne ga Annabi Muhammad SAW. Suna bin wasu aƙidojin ƴan Shi'a cewa Imam Ali shi ne Khalifa na farko bayan Manzon Allah.

Tsiraru ne a Siriya da suka fuskanci tsangwama kala-kala har suka ƙwace iko lokacin mulkin iyalan Assad na tsawon fiye da shekara 50 wanda kwaf ɗaya aka kawo ƙarshensa a bara.

Aƙidojin ƴan ɗariƙar Alawi, da suka haɗa da gudanar da bikin kirsimeti da murnar zuwan kalandar Zoroastria, ba a san su ba har ma ga yawancin musulmai.

Su ne kashi 10 cikin 100 na al'ummar Siriya sannan kuma na biyu mafi girma cikin ɗariƙoƙi bayan ƴan aƙidar Sunnah.

Sune suka fi yawa a lardunan Latakia da Tartus, amma akwai masu aƙidar a Turkiyya da Iraƙi da Lebanon.

Bayan juyin mulki a 1970, da mahaifin tsohon shugaba Bashar al-Assad, Hafez, Alawiyyawa sun ƙara samun iko kan muhimman cibiyoyin Siriya da rundunar tsaronta.

Sauran musulmai na ganin Alawiyyawa a Gabas ta Tsakiya a matsayin masu sassaucin ra'ayi ko ma waɗanda ba su damu da addini ba. A ƙarƙashin mulkin Assad, ba a tilasta wa mata sanya hijabi sannan wasu da dama na ƙin yin sallah ko ma azumi. Wasu musulmai na yi wa Alawiyyawa kallon masu aƙidu na daban.

Tasiri da kuma iko kan shugabanci ƙarƙashin ƴan ɗariƙar da ke zaune a ƙasar da ƴan akidar Sunna suka mamaye sun ɓace lokaci guda bayan da Assad ya tsere zuwa Rasha a Disambar bara.

Me ya janyo kashe-kashen?

Hamɓararren shugaban Siriya Bashar al-Assad ɗan ɗariƙar Alawi ne. Ya kuma yi wa ƴan ɗariƙar alfarma tare da ɗaga darajarsu a rundunar sojin ƙasar da, a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙokin bil adama, suke kai wa ƴan aƙidar Sunnah masu rinjaye hari.

Duk da haka, ƴan Alawi da dama sun ce a ƙarƙashin Assad, an muzguna masu sun kuma ha wahala, musamman idan suka nuna adawa ga gwamnatinsa.

Tashin hankalin baya-bayan nan ya soma ne a makon da ya gabata bayan da masu biyayya ga Asad da suka ƙi ajiye makamai - suka yi wa sojoji kwanton ɓauna a lardunan Latakia da Jbleh, inda suka kashe gomman su.

Ghiath Dallah, wani tsohon soji mai muƙamin birgediya janar a rundunar sojin Assad, ya sanar da sabon bore ga sabuwar gwamnati, inda ya ce yana kafa "Majalisar Soji ta ƴantar da Siriya".

Wasu rahotanni sun nuna cewa tsoffin jami'an tsaron gwmanatin Assad da suka ƙi ajiye makamansu na kafa wata ƙungiyar masu turjiya a tsaunuka.

A lokacin ana ganin hare-haren da ake kai wa ƴan Alawi a matsayin ramuwar gayya daga sojojin sabuwar gwamnati.

Mazauna yankin suna shaida wa BBC cewa akasarin Alawiyyawa sun ƙi amincewa da yunƙurin kafa waɗannan ƙungiyoyin masu turjiya inda suke zargin Dallah da sauran masu matuƙar biyayya ga Assad da haifar da tashin hankalin.

Tun soma yaƙin, an bayar da rahoton tserewar ɗaruruwan mutane daga gidajensu a lardunan Latakia da Tartus - wurare biyu da magoya bayan Assad suka fi yawa.

Mazauna yankunan sun bayyana yadda suka ga sace-sace da kuma kashe-kashe, har da na yara da yadda gawawwaki suke yashe a tituna.

BBC ba ta iya tabbatar da alkaluman mace-macen ba. Sai dai wata kungiya mai sa ido ta ce aƙalla farar hula 1,200 aka kashe a hare-haren da aka kai wa Alawiyyawa a ranar Juma'a da Asabar ɗin makon da ya gabata.

An kuma kashe wasu jami'an tsaro 231 da magoya bayan mayaƙan Assad 250 a rikicin, a cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights.