Wenger zai jagoranci kwamitin kula da lafiyar ƴan wasa na Fifa

Arsene Wenger

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger zai jagoranci kwamitin kula da walwalar ƴan wasa na Fifa a sakamakon damuwa da ake nunawa game da jadawalin wasannin ƙwallon ƙafa.

A farkon wannan watan ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon kafa na Turai da ƙungiyar ƴan wasa Fifpro suka shigar da ƙara a gaban hukumar tarayyar Turai kan zargin babakere da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ke yi kan jaddawalin wasannin ƙasa da ƙasa.

Wakilan ƙungiyar ƴan wasan dai na cikin kwamitin da ke ƙarƙashin jagorancin shugaban sashen ci gaban ƙwallon ƙafa ta duniya na hukumar FIFA. Wenger tare da wakilai daga ƙungiyoyin hukumomin ƙwallon ƙafan ƙasashe da ke mambobin Fifa da na ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya.

Manufar kwamitin ita ce ta bincika yadda za a iya aiwatar da matakan kariya masu dacewa da inganci ga ƴan wasa, wanda ya haɗa da yawan wasannin da ƴan wasa ke bugawa a shekara.

Ana sa ran kwamitin zai fara zama nan da wasu makonni masu zuwa.

Tuni dai jaddawalin wasannin ƙwallon ƙafa na Turai ke fama da cunkoso sakamakon faɗaɗa gasar cin kofin duniya na ƙungiyoyi da za a gudanar a Amurka daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli na shekara mai zuwa.

A baya bayan nan da ɗan wasan tsakiya na Sifaniya da Manchester City kuma zakaran kyautar Ballon d'Or na bana, Rodri ya ce ƴan wasa na dab da shiga yajin aiki domin nuna adawa da ƙaruwar wasanni.