An ɗage wasan da Real Madrid za ta je Valencia

Asalin hoton, Getty Images
Wasan gwarzuwar gasar La Liga Rwal Madrid da Valencia da aka tsara yi a ranar Asabar, an ɗage shi saboda mummunar ambaliyar da ta auku a Spain.
Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ta ɗage duka wasannin da za a yi a yankin Valencia, inda aƙalla mutuim 59 suka mutu gwammai kuma suka ɓata sakamakon wani mamakon ruwa.
Shi ma wasan Villareal da Rayo Vallecano na La Liga an ɗage shi, tare da wasanni uku na ƙaramar gasar Segunda - Castellon da RC Ferrol, CD Eldense da SD Huesca sai kuma wasan da Malaga za ta ziyarci Levante.
A ɓangaren wasan mata ma an ɗage wasan Valencia da Deportivo La Coruna, Real Madrid da Levente.
Hukumar kwallon ƙafa ta Spain ta samu neman buƙatar hakan daga La Liga da La Liga F na mata da ƙungiyoyinsu kan cewa suna so a ɗage wasannin.
An sauya ranar wasannin Copa del Rey da za a yi, ciki har da wasan da Valencia za ta je Parla Escuela.
Hukumar ta ce za a yi shiru na minti ɗaya a wasannin da za a yi a ƙarshen mako domin nuna jajajntawa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.







