Yadda cutar kwalara ke hallaka jama'a a Zambia

- Marubuci, Daga Kennedy Gondwe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC daga Lusaka
Lokacin da na hadu da Andrew Kazadi jim kadan bayan da dan yarsa mai shekara 26 ya rasu a wata cibiya ta kula da masu fama da cutar kwalara, a Lusaka, na gan shi a dimauce.
Ya ce, "an bukaci mu je mu kawo makara, amma idan muka yi jinkiri to za a binne shi haka.'' Wadannan na daga irin kalaman da ya furta min cikin damuwa, kan irin matakan takaita al'amura da gwamnati ta dauka a lokacin annobar korona.
A yanzu cutar kwalara wadda gurbataccen ruwan sha ke haddasawa tana yi wa al'ummar Zambia ta'annati inda a yanzu sama da mutum 15,000 suka kamu kuma kusan 6000 suka mutu, yawanci a yankin da ta fi kamari a babban birnin kasar, Lusaka, tun farkon damina a watan Oktoba.
Yayin da hadari ya gangamo kafin wani ruwan sama ya sake barkewa, Mista Kazadi ya ce, : "Dole ne mu yi sauri mu samo makara."
Na hadu da shi ne a wajen babban filin wasa na Heroes Stadium mai cin mutum 60,000, inda aka mayar da wurin cibiyar kula da wadanda cutar ta amai da gudawa ta kama, inda ake da ma'aikatan lafiya 800 da ke kula da marassa lafiya daga fadin kasar.
Idan kana wurin za ka rika jin karan jiniya ba kakkautawa, yayin da ake shiga da maras lafiya ko fita da gawarwakin wadanda rai ya yi halinsa a sanadiyyar cutar.
Ba karamin abin tashin hankali ba ne ga Mista Kazadi, ya ga gawar Charles, dan yayarsa, abin ya dugunzuma shi.
Charles ya yi fama da amai da gudawa. Daga nan ne aka kai shi asibiti inda a can aka fada musu cewa ya kamu da kwalara ne.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga nan ne aka garzaya da shi wannan filin wasa da aka mayar cibiyar kula da masu cutar ta amai da gudawa, inda a can ne bayan kwana takwas ya ce ga garinku nan.
"Mun dauka cewa zai samu sauki sannu a hankali. A gaskiya muna cikin bakin ciki," in ji Mista Kazadi, yana mai nuni da cewa dan yayar tasa ya rasu ya bar da mai shekara uku.
To amma ga irin yadda iyalan suka yi imani da kaddara, sai ya kara da cewa: "A duk lokacin da wani ba shi da lafiya, muna mayar da komai ga Ubangiji - wannan mutum zai iya rayuwa ko kuma ya mutu. Duk da irin kalubale da faman da muka yi, ba abin da za mu ce sai godiya ga Allah."
Bisa dokokin da gwamnati ta bullo da su na hana bazuwar cutar, jami'ai sanye da kayayyakin kariya sun nade gawar Charles a cikin leda kafin a sanya ta a cikin makara.
An hana iyalan taba gawar domin kada su kamu da cutar. Mutum biyar kawai daga cikin 'yan gidansu aka bari su halarci jana'izarsa.
Ka'idojin gwamnatin daidai suke da na hukumar lafiya ta duniya, wadda ta bayar da shawarar cewa kada a bari iyalan wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar su taba ko yin ta'amalli da gawar sosai. Kuma lalle ne a tabbatar an binne gawar cikin sa'a 24.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce amai da gudawa kamar kwalara na iya yaduwa cikin sauki ta hanyar bayan gidan da ya fito daga jikin mamaci.

Asalin hoton, Andrew Kazadi
Sai dai abin takaici wasu iyalan na fama da damuwa fiye da wadda iyalan su Kazadi suka shiga.
Ba su san halin da 'yan uwansu ke ciki ba saboda ma'aikatan lafiyar da aiki ya yi musu yawa ba sa ma iya gaya musu halin da marassa lafiyar ke ciki ko 'yan uwan suna nan da rai ko kuma ma sun mutu ba.
Wadannan iyalai sun hada da Eunice Chongo, wadda ta gaya min cewa an kawo danta Boniface, mai shekara 34, cibiyar a motar asibiti kusan mako daya da ya gabata, to amma tun lokacin ba ta sake jin wani abu ba a game da shi.
"Abin da nake so kawai shi ne gwamnati ta fito fili ta gaya min inda dana yake," in ji Madam Chongo wadda ke cike da damuwa.
Gwamnatin kasar ta samar da wata cibiyar kirin waya, inda ta bukaci mutane, kamar Madam Chongo su bayar da rahoton duk wani nasu da ya bata, domin a taimaka wajen gano shi.
Zambia ta yi fama da annobar kwalara akalla sau 30 tun shekarar 1977, inda kungiyar agaji taWaterAid ta ce wannan ita ce annobar mafi muni tun shekarar 2017.
Hakan kuwa ta kasance ne duk da alkawarin da gwamnati ta yi a 2019 na kawar da cutar zuwa shekarar 2025.
Babban darektan kungiyar ta WaterAid a Zambia Yankho Mataya ya ce gwamnati ba za ta iya cimma burinta ba, ba tare da samun karin kudade ba da karin hadin kai da tsare-tsare don dakile ainahin abubuwan da ke haddasa cutar - wato rashin samun tsaftaceccen ruwa da kuma bandaki da ya dace.
Wani bincike da aka wallafa a 2019 ya nuna cewa kusan kashi 40 cikin dari na al'ummar Zambia suna rayuwa ne ba tare da hanyoyin samun ruwan sha mai kyau ba, yayin da kusan kashi 80 cikin dari ba su da kwararan hanyoyin kawar da shara da sauran kazanta.

Shugaban hukumar kare annoba na kasar ta Zambia Gabriel Pollen, ya ce har yanzu ana tattara bayanai dominsanin irin cigabanda aka samu tun 2019 wajen inganta ruwan sha da wuraren tsabta.
Ya ce, ''yawan mutanen na tayar da hankali, kuma muna ganin yadda al'ummomi ke dogara ga hukuma kan lamuran tsafta.''
Wuraren da cutar ta kwalara ta fi tsanani a babban birnin kasar, Lusaka, unguwanni ne na talakawa, inda jama'a ke rayuwa a cakude.
Yawanci ana gina salga a kusa da inda rijiyoyi marassa zurfi suke, kuma daga rijiyoyin ake samu ruwan sha.
Idan aka yi ruwan sama to akwai hadarin ruwan wadannan rijiyoyi zai iya haduwa da kazantar da ke salgar nan - kuma rashin magudanun ruwa masu kyau ke iya sa wannan ruwa ya gudana zuwa cikin gidajen jama'a.
Domin yaki da cutar ta kwalara, gwamnati ta bullo da wasu matakai da suka hada da hana gina rijiyoyi marassa zurfi da kuma sayar da kayan abinci a yanayi maras tsafta.
A wani jawabi da ya yi a farkon watan Janairu Shugaba Hakainde Hichilema ya yi alkawarin gyara unguwannin da aka yi ba tsari na hukuma, tare kuma da hana gina wasu sabbin unguwannin awon-igiya.
A jawabin nasa a wannan lokaci, shugaban ya koka da yadda ya ce wasu matasa na yawo a birane ba tare da abin yi ba maimakon su koma karkara su yi noma.
Ya ce, "Akwai filaye da yawa a kauyuka. Akwai ruwa mai tsafta. Za mu iya gina gidaje masu kyau, wadanda ba za a gurbata su ba."
Yayin da gwamnatin ke kallon rage cunkoso a birane a matsayin wata doguwar hanya ta magance matsalar, a yanzu abin da ta fi bai wa fifiko wajen shawo kan annobar da ke ta hallaka mutane, shi ne shirin allurar riga-kafi.
A farkon watan nan gwamnatin ta karbi kwalabe kusan miliyan 1.6 na allurar kuma zuwa yanzu ta yi amfani da yawanci a galibi Lusaka.
"Yadda mutane ke karbar riga-kafin abu ne mai karfafa gwiwa. Sai dai muna fargabar cewa ko yawan allurar ba zai kai abin da muke bukata domin yi a yankunan da cutar tafi kamari ba,'' in ji ministar lafiya Sylvia Masebo.
Amma kuma ta nuna takaici kan yadda wasu ke nokewa kan karbar riga-kafin musamman a tsakanin wasu kungiyoyin addini.
Ministar ba ta bayar da cikakken bayani a game da hakan ba, amma dai abu ne da aka sani cewa wasu mutanen na daukar yarda da riga-kafi a matsayin rashin tawakkali ko raunin imani.
Sakonta ga irin wadannan mutanen shi ne: "Don Allah kada mu yaudari kanmu da wannan. Dukkanmu mun san cewa addinin gaskiya ya damu da kare lafiyar mabiyansa."
Ministar ta kuma gano yadda wasu matasa ma ke dari-dari da riga-kafin.
Nan ma dai ba ta bayar da cikakken bayani ba, illa dai ta yi nuni da yadda wasu matasa ke tunkahon cewa su jikinsu na da garkuwar jiki mai karfi saboda haka su suna ganin ba sa bukatar riga-kafin.
Wasu mazajen kuwa suna ta shan barasa ne saboda sun yi amanna tana kashe kwayar cutar bakteriya wadda ke haddasa cutar ta kwalara.
A wani abu da ke zaman kamar sako ga wannan rukunin jama'a, ministar ta ce kamata ya yi mutane su rika kashe kudinsu a kan sinadarin kulorin ( chlorine) wanda ke kashe kwayoyin bakteriya a ruwa maimakon barasa.
To amma lalle sai Ms Masebo ta dage a kan wannan fadakarwa kafin matasan su sauya wannan halayya tasu, domin kusan a kodayaushe za ka gan su ne suna kara-kaina a shagunan shan barasa a Lusaka.











