Hassan Nasrallah: Abin da ya kamata ku sani kan jagoran Hezbollah da Isra'ila ta ce ta kashe

Asalin hoton, Jamaran
- Marubuci, Kayvan Hosseini
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
- Lokacin karatu: Minti 8
Hassan Nasrallah wanda ya kasance malamin addini kuma ɗan Shi'a, shi ne shugaban ƙungiyar Hezbollah tun watan Febrairun 1992. Ana ganin ƙungiyar a matsayin jam'iyyar siyasa mai muhimmanci a Lebanon, wadda dakarunta ke cikin sojojin ƙasar ta Lebanon.
A ranar Asabar 28 ga watan Samtumba ne rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe Sheikh Hassan Nasarallah bayan jerin hare-haren da ta shafe tsawon daren ranar taka kai wa wasu sassan birnin Beirut.
Ana ganin Nasrallah, wanda sananne ne a Lebanon da kuma ƙasashen Larabawa, a matsayin jagoran Hezbollah kuma ya taka rawa wajen mayar da ƙungiyar shiga harkokin siyasa da samun iko a tsarin gwamnatin Lebanon.
Yana da alaƙa ta musamman da Iran da kuma jagoran addini a ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Duk da cewa Amurka ta ayyana Hezbollah cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci, sai dai hakan bai saka shugabannin Iran ko Nasrallah ɓoye alaƙa da ke tsakaninsu ba.
Hassan Nasrallah yana da masoya da kuma maƙiya. A kan wannan dalili ne, bai bayyana gaban jama'a ba na tsawon shekaru saboda fargabar hallaka shi daga Isra'ila.
Sai dai ɓoyewarsa ba ta hana magoya bayansa ci gaba da jin jawabansa ba kowane mako.
Waɗannan jawabai sun kasance babban makamin Nasrallah wajen nuna iko, kuma ta haka, yana magana kan batutuwa da dama a Lebanon da kuma duniya da ƙoƙarin matsa wa abokan gaba lamba.

Asalin hoton, Getty Images
Yarunta da kuma girmansa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Hassan Nasrallah a watan Agustan 1960. Ya taso ne a cikin wata al’umma da ke rayuwa da ɗan rufin asiri a gabashin Beirut. Mahaifinsa yana da wani karamin kanti, kuma Hassan ya kasance babban ɗansa cikin ƴaƴa tara da yake da su.
Yana da shekara biyar lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke a Lebanon; yaƙin da ya ɗaiɗaita karamar ƙasar da ke jikin tekun Bahar Rum na tsawon shekara 15, inda a lokacin ne kuma ƴan ƙasar ta Lebanon suka raba iyaka tare da yin faɗa da juna a rikicin addini da kuma kabilanci.
Soma yaƙin ya sanya mahaifin Hassan Nasrallah yanke shawarar barin Beirut da komawa ƙauyensu na asali da ke kudancin Lebanon: wani ƙauye da ake kira "Al- Bazouriyeh" wadda mazaunansa suka kasance ƴan Shi'a kamar na sauran ƙauyuka da kuma lardin Al-Janub.
Ya shafe shekarunsa na makarantar firamare da sakandari a kudancin Lebanon, cikin ƴan Shi'a. Waɗannan ƴan Shi'a sun yi imanin cewa lokacin mulkin mallaka na daular Ottoman da kuma Faransa, sun fuskanci cin zarafi da rashin adalci. Hakan ya ci gaba har bayan samun ƴancin kai lokacin da Kiristoci da ƴan Sunni suka samu iko.
A wannan lokaci, an zargi mayakan Kiristoci da ƴan Sunni da samun taimakon ƙasashen waje domin samun karfin soji.
A dai wannan lokaci, ana ganin al'umar Shi'a, waɗanda suke da rinjaye a kudancin Lebanon da yankin Beqaa da ke gabashin Lebanon, haɗe da Kiristocin Orthodoxm, a matsayin sahun gaba wajen yaƙi da Isra'ila na tsawon shekaru da kuma kirkiro da mulkin yahudawa a yankin Falasdinawa.
Lokacin da ya kai shekara 15, Hassan Nasralla ya zama mamban ƙungiyar siyasa ta ƴan Shi'a, wadda malamin addinin Iran Musa al-Sadr ya kafa.

Asalin hoton, FARS NEWS
Komawa Lebanon da shiga gwagwarmaya
Hassan Nasrallah ya koma birnin Najafat da ke Iraqi lokacin da yake shekara 16.
Iraqi ta ƙasance ƙasa mai fama da rikice-rikice a lokacin da kuma samun sauye-sauye na tsawon shekaru 20, juye-juye mulki da kisan ƴan siyasa.
A lokacin, duk da cewa Hassan al-Bakr na kan mulki, Saddam Husseini wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙasa, ya yi babban tasiri a ko'ina.
Bayan shafe shekara biyu da Hassan Nasrallah ya yi a Najaf, shugabannin jam'iyyar Ba'ath musamman ma Saddam Husseini, suka yanke shawarar cewa za su dauki matakai na karya lagon ƴan Shi'a. Ɗaya daga cikin matakan shi ne korar dukkan ɗalibai ƴan Shi'a daga Lebanon waɗanda ke karatu a makarantun Iraqi.
Duk da cewa Hassan Nasrallah ya yi karatu ne na tsawon shekara biyu a Najaf, kasancewarsa a birnin ya yi tasiri kan rayuwar wani matashin Lebanon: ya haɗu da wani malamin addini mai suna Abbas Mousavi a Najaf.
An taɓa sanin Mousavi a matsayin ɗaya daga cikin ɗaliban Musa al-Sadr a Lebanon kuma lokacin zamansa a Najaf, akidojin siyasar Khomeni sun yi tasiri kan Nasrallah.
Ya fi Nasrallah da shekara takwas kuma ya zama babban malami a rayuwar Hassan Nasrallah.
Bayan komawa Lebanon, waɗannan mutane biyu suka shiga yaƙin basasar ƙasar da ake yi. A lokacin, Nasrallah ya tafi wajen Abbas Mousavi wanda ke garin Beqaa, domin yin karatu a can.

Asalin hoton, Getty Images
Juyin-juya-halin Iran da kafa ƙungiyar "Hezbollah"
An samu juyin-juya hali a Iran shekara ɗaya bayan komawar Hassan Nasrallah Lebanon.
Ayattulah Khamenei, wanda ya samu goyon bayan malaman addini kamar Abbas Mousavi da Hassan Nasrallah, ya kwace mulki. Abin da ya farun ya sauya dangantaka tsakanin ƴan Shi'ar Lebanon da na Iran.
Gwagwarmayar siyasar yan Shi'ar Lebanon ta samu tasiri ne kan irin abubuwan da suka faru a Iran da kuma akidar ƴan Shi'a.
Ga Hassan Nasrallah, sauyin da aka samu ya faru ne saboda mulkin Ayatollah Ali Khamenei.
A 1981, Nasrallah ya haɗu da jagoran Jamhuriyar Iran na wancan lokaci a Tehran. Khamenei ya naɗa shi a matsayin mai taimaka masa a Lebanon domin kula da harkokin addini.
Daga baya, Nasrallah ya fara yin tafiye-tafiye zuwa Iran daga lokaci zuwa lokaci, inda ya kulla dangantaka da manyan masu faɗa a ji na gwamnatin Iran.
A wannan lokaci, Lebanon wadda yaƙin basasa ya yi wa ƙawanya, ta kasance wurin zaman mayakan Falasɗinawa. Sun fi yawa ne a kudancin Lebanon, ƙari da Beirut.
Isra'ila ta far wa ƙasar Lebanon a watan Yunin 1982 lokacin da yaƙi ya fara yaɗuwa. isra'ila ta yi iƙirarin cewa harin yana a matsayin takalarta da Falasɗinawa suka yi.
A 1985, aka kafa ƙungiyar Hezbollah a hukumance. Hassan Nasrallah da Abbas Mousavi, tare da wasu mambobin gwagwarmayar Amal, sun shiga cikin wannan sabuwar ƙungiya.
Ƙungiyar ta samu jagoranci daga wani mai suna Subhi al-Tufayli. Ƙungiyar tayi saurin karaɗe wurare musamman ta hanyar shiga siyasa a matakin yankuna da kuma daukar makamai don faɗa da dakarun Amurka da ke Lebanon.

Asalin hoton, Getty Images
Haurawa matakin jagoranci
Nasrallah yana da shekara 22 lokacin da ya shiga ƙungiyar Hezbollah.
A shekarun 1980, lokacin da dangantakar Nasrallah da Iran tayi nisa, ya yanke shawarar komawa birnin Qom domin ci gaba da karatun addini. Lokacin zamansa a Qom, ya zama kwararre a yaren Farisa kuma ya kulla alaƙa ta kut-da-kut da manyan ƴan siyasa a Iran.
Lokacin da ya koma Lebanon, an samu saɓani tsakaninsa da Abbas Mousavi. A lokacin, Mousavi ya goyi bayan ƙaruwar ayyukan Siriya da kuma tasirin ƙasar a Lebanon karkashin shugabancin Hafez Assad.
Nasrallah ya hakikance cewa ƙungiyar ta mayar da hankali kan kai wa sojojin Amurka da na Isra'ila hare-hare.
Ya samu kansa cikin ƴan Hezbollah marasa rinjaye, kuma jim kaɗan bayan nan, aka naɗa shi "Mataimakin Hezbollah a Iran." Wannan mukami ya mayar da shi zuwa Iran a lokaci guda da nisanta shi da ƙasar.
Daga baya, alamu sun nuna cewa tasirin Iran kan Hezbollah na raguwa. Duk da gagarumin goyon bayan Tehran, sanya baki a al'amuran Hezbollah ya zama kalubale.
Hankula sun tashi, inda a 1991, aka tsige Subhi al-Tufayli daga mukamin Babban Sakataren Hezbollah, inda aka naɗa Abbas Mousavi a madadinsa.
Bayan cire Al-Tufayli, Hassan Nasrallah, wanda ke ganin rawar da Syria ke takawa a Lebanon ta ragu, ya koma ƙasarsa inda ya zama shugaba na biyu a ɓangaren iko a ƙungiyar Hezbollah.

Asalin hoton, Getty Images
Shugabancin Hezbollah a Lebanon
Isra'ila ta kashe Abbas Mousavi kasa da shekara ɗaya, bayan an zaɓe shi a matsayin Baban Sakataren Hezbollah.
Duk dai a shekarar, a 1992, shugabancin ƙungiyar ya koma hannun Hassan Nasrallah.
A lokacin, yana da shekara 32, kuma mutane da yawa na kallon zaɓarsa da aka yi na da alaka da kyakkyawar dangantaka da yake da shi da Iran.
Wani abu mai muhimmanci da Nasrallah ya yi a lokacin shi ne naɗa waɗand ke alaƙa da kuma mambobin Hezbollah a zaɓen Lebanon da aka yi.
Ya yanke shawarar saka reshen siyasar Hezbollah a matsayin mai karfin faɗa a ji, shekara ɗaya bayan da Saudiyya ta shiga tsakani a yaƙin basasar Lebanon da kawo karshensa.
Sakamakon haka, Hezbollah ta samu damar cin zaɓen kujeru takwas a majalisar dokokin Lebanon.
A dai lokacin, aka zargi Hezbollah da tsara aiwatar da ayyukan ta'addanci. An kai harin bam kan cibiyar yahudawa a tsakiyar Argentina da kuma wani hari kan ofishin jakadancin Isra'ila a Argentina a lokaci.
Bisa yarjejeniya da aka cimma da ya kawo karshen yaƙin basasar Lebanon, Hezbollah ta amince ta ajiye makamanta.
A lokacin, Isra'ila ta mamaye kudancin Lebanon, kuma Hezbollah a matsayin ƙungiya da ke faɗa da dakarun da suka yi mamayar, ta ci gaba da riƙe makamai.

Asalin hoton, Getty Images
Janyewar Isra'ila da shaharar Nasrallah
A shekara ta 2000, Isra'ila ta sanar da cewa za ta janye gabaki-ɗaya daga Lebanon, abin da ya kawo karshen mamayar da ta yi wa kudancin ƙasar. Hezbollah tayi murnar da hakan, inda ta ce babban nasara ce da kuma jinjinawa Nasrallah.
Wannan ne lokaci na farko da Isra'ila ta fice daga wata ƙasar Larabawa bisa raɗin kanta ba tare da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, kuma Larabawa da dama a yankin sun ɗauki hakan a matsayin babbar nasara.
Sai dai, tun bayan lokacin, batun makaman ƙungiyar Hezbollah ya zama muhimmin tambaya dangane da tsaro da kuma ɗorewar zaman lafiyar Lebanon.
Janyewar Isra'ila daga ƙasar ya tabbatar da hujjara Hezbollah na ci gaba da riƙe da makamai, abin da ya janyo ƙungiyoyin adawa da kuma masu iko na ƙasashen waje yin kira ga Hezbollah da ta ajiye makamai - buƙatar da Nasrallah ya ki aminta.
Daga baya, Nasrallah ya cimma yarjejeniyar musayar fursunoni lokacin tattaunawa da Isra'ila, abin da ya kai ga sake ƙarin Falasɗinawa sama da 400, da fursunonin Lebanon da kuma ƴan wasu ƙasashen Larabawa.
A wannan lokaci, Nasrallah ya kasance yana da karfin iko da kuma tasirin da bai taɓa samu ba, kuma ƴan adawarsa a siyasar Lebanon sun fuskanci babban kalubale wajen yin gaba da gaba da shi da kuma hana shi faɗaɗa tasirinsa da ikoonsa.
Nasrallah wanda ke da shekara 64, ya kasance jagoran siyasa a Lebanon wanda ya shafe gomman shekaru yana gwagwarmaya.
Ya yi amfani da wannan shahara wajen kere wa abokan adawarsa na siyasa da kuma ɗabbaka aƙidar ƴan Shi'a.











