Aurena na ƙarshe shi ne mafi muni - Ƙalubalen da Mr Ibu ya fuskanta kafin rasuwa

Asalin hoton, MR IBU/INSTAGRAM
- Marubuci, By Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
- Aiko rahoto daga, Kano
Wannan shi ne fitaccen ɗan wasan fina-finai a Najeriya, John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu, wanda ya shahara wajen barkwanci ta yadda ba ma ya buƙatar buɗe baki kafin sanya mutane dariya.
"An zaɓe ni na taka rawar likita a wani fim wani lokaci kuma da na zo sanye da kayan likita, kafin ma na ce komai, mutanen da ke shirya fim ɗin kawai suka fashe da dariya," kamar yadda ya tuna.
Mutuwarsa yana shekara 62 ta jefa iyalai da abokai da masu kallon fina-finan masana'antar Nollywood da ke sassan Afirka cikin jimami.
Ya fara fitowa cikin fina-finai a 2004 a cikin fim ɗin da aka yi wa take Mista Ibu wanda ya bayar da labarin wani magidanci da ɗansa inda suke tafiyar da rayuwarsu inda suka yi ta fama da ƙalubale da matsaloli na rayuwa - masu sarƙaƙiya da ban dariya." Yanayin fuskarsa da jikinsa su ne ke jan hankalin masu kallonsa," kamar yadda daraktan fim, Babangida Bangis ya shaida wa BBC inda ya bambanta shi da sauran masu fina-finan barkwanci da ke amfani da kalamai wajen sanya mutane dariya.
"Mista Ibu na daban ne saboda ba ya buƙatar yin magana domin sa mutum dariya, saboda fuskarsa kamar ta Mista Bean [Rowan Atkinson] na sanya mutum dariya," in ji shi.
Tabbas, ɗaya daga cikin shirinsa mafi ban dariya kuma wanda ya haska shi ga masu kallon fina-finai a Afirka, shi ne wanda a ciki, bai cika yin magana ba.
A fim ɗin Mista Ibu, shi da ɗansa suna komawa gida daga gona inda suka yi aiki kuma kekensu guda ɗaya ne.
Da farko, mahaifin ya bar ɗansa ya tuƙa keke yayin da shi kuma yake daɓa sayyada.
Amma masu wucewa sun tsayar da su domin su tambayi me ya sa ɗan bai nuna girmamawa ga mahaifinsa da shekarunsa suka ja ba ta hanyar ba shi keken ya tuƙa.
Sai suka yi musanya.
Sai kuma wani mai wucewa ya ce ai mahaifin mugu ne saboda ƙyale ɗansa ya yi tafiya a ƙasa shi kuma yana kan keke.
Sai dukkan su suka yanke shawarar tafiya a ƙasa.
Sai kuma mutane suka kira su marasa tunani saboda yin takawa a ƙafa alhalin kuma suna da keke.
Fim ɗin ya shahara sosai har ta kai an ƙara gina labari a kansa kuma tun lokacin aka san Okafor da Mista Ibu.
Cike giɓin rarrabuwar kan Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Za kuma a ci gaba da tunawa da shi a arewacin Najeriya saboda yana cikin tsirarun masu fim ɗin Nollywood da suka tsallaka zuwa masana'antar fim ta Kannywood, wadda galibi waɗanda suka fito daga kudancin ƙasar ke yi wa masana'antar gani-gani.
Fitaccen fim ɗin da ya yi a Kannywood shi ne na Hajiya Babba wanda aka gina labarin kan wasu yara biyu daga kudancin Najeriya suka ɓata waɗanda suka gano mahaifinsu a arewa sannan suka fara sabuwar rayuwa da shi.
"Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka taimaka wajen cike giɓi tare da kawo haɗin kai tsakanin Kannywood da Nollywood ta hanyar zuwa arewa ya yi fim," in ji Bangis.
An haife shi ranar 17 ga watan Oktoban 1961 kuma ɗan asalin Enugu ne da ke kudu maso gabashin Najeriya, jihar da ta samar da jaruman Nollywood da dama.
Okafor bai yi rayuwar jin daɗi ba a tasowarsa, ya koma wani gari domin rayuwa da ɗan'uwa inda ya riƙa aikin hannu domin samun kuɗin tallafa wa iyalinsa.
Bayan da ya shiga sana'oi kamar na gyaran gashi da ɗaukan hoto, ya shiga a tantance shi domin soma fim inda shahararren ɗan fim ɗin nan Pete Edochie ya gano baiwar da yake da ita inda kuma ya buɗe masa ƙofar shiga fina-finan Nollywood.
'Wannan ne aurena mafi muni'
Tun bayan sanar da mutuwarsa, al'umma suka yi ta aika saƙonnin ta'aziyya.
Fitaccen mai wasan barkwanci Bovi ya bayyana Mista Ibu a matsayin ɗaya daga cikin shahararru.
"Mutuwar John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu mummunan labari ne a masa'antar nishaɗantawa ta Najeriya. Mu samu nutsuwa da cewa fina-finan za su ci gaba da kasancewa kuma za su zaburar da har waɗanda ba a haifa ba. Allah ya ji ƙansa" kamar yadda saƙon Bovi ya bayyana a shafin X.
Ministar al'adu ta Najeriya, Hannatu Musawa ta bayyana shi a matsayin mutumin da ya sanya iyalai murmushi tsawon lokacin da ya yi yana fina-finai.
A shekarar da ta gabata ne labarin rashin lafiyar ɗan wasan fina-finan ya fito fili. An yanke ɗaya daga cikin ƙafafunsa a Nuwamba bayan da mutane suka yi cincirindo wajen tallafa masa da kuɗin magani.
Ana ganin ɗan wasan fim ɗin ya yi fama da cutar suga sai dai iyalinsa ba su faɗi abin da ya janyo mutuwarsa ba.
Duk da yadda ya sa mutane da dama cikin nishaɗi, bai samu kwanciyar hankali ba a gidan aure.
Ya yi aure sau biyar, wanda galibi suka kai ga rabuwa.
A baya-bayan nan ne ya bayyana aurensa na biyar a matsayin wanda ba ya samun farin ciki idan ya kwatanta da sauran aure-auren da ya yi a baya.
"Wannan ne aurena na ƙarshe. Idan wannan ya lalace, ba zan sake aure ba. Wannan ne karo na biyar kuma mafi muni," kamar yadda ya faɗa wa shafin labarai na Daily Post a farkon shekarar nan.
Kafafen yaɗa labarai a ƙasar sun ce ya bar ƴaƴa 13 sai dai su ma sun kasance batu na damuwa.
Bayan da masu sha'awar fina-finansa suka ba shi tallafin kuɗi domin yi masa tiyata, an kama ɗansa Daniel Okafor da ƴar da ya riƙa Jasmine Chioma bisa zargin kutsawa cikin wayarsa ta hannu tare da sace naira miliyan hamsin da biyar. Sun dai musanta zargin.
Duk da cewa an daɗe ba a ga fuskarsa a wani sabon fim ba, ya ci gaba da tashe har zuwa lokacin da rashin lafiya ta zamar masa cikas.
A Oktoban 2020, ya saki wasu waƙoƙi biyu - 'This Girl' da 'Do You Know' waɗanda ake gani sune ayyukansa na ƙarshe.
Sai dai shigarsa harkar waƙa ba ta yi nasara ba kuma za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin mutumin da ya sanya nishaɗi tsakanin al'ummar Afirka.
Wani mai son fina-finansa Aminu Hamisu ya ce zai tuna da marigayin ta hanyar sake kallon wasu daga cikin tsofaffin fina-finansa a shafin YouTube.
Da alama ba shi kaɗai ne yake da wannan ra'ayi ba.











