Yadda siyasa ke raba kan iyali a Pakistan gabanin zaɓen firaminista

Two women cast their ballots in the parliamentary election on 18 February 2008 in Peshawar, Pakistan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata biyu da suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa a shekara ta 2008, a Peshawar
    • Marubuci, Tarhub Asghar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Urdu

Idan aka zo batun siyasa a Pakistan, "babu wanda ya ke da ƴancin magana ", Amma wata ɗaliba a Lahore ta tattauna da BBC.

Yayin da ƙasar ke shirin kaɗa ƙuri'a a ranar 8 ga watan Fabrairu domin zaɓen firaministanta na gaba, masu kaɗa ƙuri'a sun shaida min cewa rarrabuwar kawuna a Pakistan na janyo fargaba game da zaɓen.

Musayar ra’ayin siyasa takan yi matuƙar ƙamari, har a wani yanayi mai tsanani, an zargi wani uba da kashe ɗansa, Ata ur Rehman, bayan da aka samu rashin jituwa tsakaninsu kan batun siyasa.

‘Dukkan iyalanmu suna cikin jimami,’ kamar yadda ɗan'uwan Ata, Arif, ya shaida wa BBC.

Arif ya ce ɗan'uwansa yana zama tare da mahaifinsa a Peshawar, yayin da yake hutu daga wurin aikinsa a Qatar. ‘An samu hatsaniyar ce a lokacin da Ata ya nemi maƙala tutar jam’iyyar PTI a rufin gidan, duk da cewa mahaifina ba ya goyon bayan kowace jam'iyyar siyasa, bai ji daɗin hakan ba.’

PTI, ko Pakistan Tehreek-e-Insaf, ita ce jam'iyyar tsohon Firaminista Imran Khan, wanda aka hambarar a shekara ta 2022 bayan ƙawancen jam'iyyun adawa sun kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa, kuma yanzu haka yana gidan yari bisa samun sa da laifin cin hanci da rashawa da fallasa wasu bayanan sirri, an kuma haramta masa tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Arif ya ce ‘an fara cece-ku-ce mai zafi’, kafin mahaifinsa ya harbe Ata, sannan ya gudu. Ƴansanda sun tabbatar da mutuwar Ata daga baya.

Koda yake wannan lamari ba kasafai yake faruwa ba, mutane da yawa sun bayyana cewa suna yawan samun rashin jituwa da iyalansu a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓe.

Imran Khan
Bayanan hoto, Tsohon firaminista Imran Khan yana kurkuku kuma an hana shi tsayawa takara a zaɓen 2024

"Ni da ƴar'uwata mun shafe wata uku ba mu yi magana da mahaifinmu ba," in ji Nida Zeshaan, wata mai goyon bayan Imran Khan.

Nida da ƴar'uwarta sun zaɓi jam'iyyar PTI a zaɓen da ya gabata a 2018, inda suka taimaka wa Khan ya yi nasara amma ya haifar da rikici a gida.

"Mahaifina bai amince da kundin manufofin Khan ba, ya ce Khan ba ɗan siyasan ƙwarai ba ne."

Nida ba ta ji tsoron faɗin ra'ayinta ba. "Na kasance ina jayayya da mahaifina sosai, zan ce: "Ina son Khan da halayensa." Na ji daɗin bayanan manufofinsa."

Nida ta ce lamarin bai sauya ba a zaɓen 2024 kuma idan suka samu bambancin ra’ayi da wasu za ta ‘daina haɗuwa da su idan ba haka ba za su rabu da rikici’.

Amma ta ce ƙawayenta na mutunta matsayinta, koda ba su amince da shi ba. "Mijin abokina yana takara a wannan zaɓen ƙarƙashin inuwar wata jam'iyya, tabbas ta san cewa ba zan zaɓe shi ba don haka ba ta nemi in goyi bayansa ba."

Me ya sa zaɓen ke da muhimmanci?

Rikicin Pakistan da Indiya, da rashin kwanciyar hankali kan iyakokinta da Iran da Afghanistan da Taliban ke iko da ita, da dangantaka mai kwan-gaba kwan-baya da Amurka da kuma kusancinta da China sun sanya ta zama muhimmiyar ƙasa a siyasar duniya, kuma duk wanda ya hau kan karagar mulki a wannan ƙasa wadda ta mallaki makamin nukiliya ya shafi sauran duniya baki ɗaya.

A cikin Pakistan, wannan zaɓe yana da mahimmanci yayin da mutane ke neman kwanciyar hankali bayan wani lokaci na rikice-rikicen siyasa da matsalolin tattalin arzƙi da kuma musayar hare-haren makamai masu linzami da Iran.

Badges to be used for campaigns of political parties, on display at a shop ahead of general elections in Karachi, Pakistan 18 January 2024

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hotunan yaƙin neman zaɓe akan nuni a wani shago a Karachi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Pakistan na da daɗaɗɗen tarihin mulkin soja da mulkin kama-karya kuma wannan zaɓe zai gudana ne yayin da ake zargin tsoma bakin soja.

Jama’a da dama na cewa jam’iyyar PTI ta Imran Khan ba a ba ta dama ba, domin an ɗaure ƴan takara, wasu kuma sun tsere ko kuma sun tsaya takara a matsayin ƴan takara masu zaman kansu.

An kuma hana jam'iyyar amfani da alamar sandar wasan kurket, wanda ke da muhimmanci don taimaka wa miliyoyin masu jefa ƙuri'a waɗanda ba su iya karatu ba su zaɓi inda za su yi alama yayin kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓe.

A wani sauyin matsayi kuma, wanda ya yi firaminista har sau uku Nawaz Sharif, daga jam'iyyar Pakistan Muslim League (Nawaz) (PML-N) ya dawo. Shi dai an dakatar da shi ne daga tsayawa a karon ƙarshe kasancewar yana gidan yari bisa laifin cin hanci da rashawa amma ya sake fitowa daga gudun hijirar da ya ɗaura wa kansa kuma an wanke shi daga dukkan laifuka.

Wani ɗan takara kuma shi ne shugaban jam'iyyar Pakistan People's Party (PPP), Bilawal Bhutto-Zardari, wanda a shekaru 35 a duniya shi ne mafi karancin shekaru cikin ƴan takaran. Mahaifiyarsa ita ce tsohuwar Firaminista Benazir Bhutto, wadda aka kashe a shekara ta 2007 kuma mahaifinsa da kakansa tsoffin shugabannin ƙasa ne, don haka masu suka sukan zarge shi da cin gajiyar son zuciya.

Me ke janyo rarrabuwar kawuna a Pakistan?

Wani mutum a Punjab yana tunanin dalilin da ya sa ƙasar ta rarrabu. "Mutanen Pakistan suna bin sawun shugabanninsu ne kawai," in ji shi, yayin da yake bayar da misali da yadda wani ɗan siyasa ya ce yana so ya ja abokin hamayyarsa "kan titi".

Yayin da wani mutum ya jingina wa Khan laifin baki ɗaya. "Wannan rashin haƙuri ya bazu ne da zuwan Khan cikin siyasa. Ya zargi kowa, ya kira kowa da kowa da ɓarayi."

Magoyin bayan jam’iyyar PTI, Muhammad Hafeez ya yarda cewa Khan ya ba da gudummawar rarrabuwar kawuna amma ya ce hakan ba lallai ne ya zama mummunan abu ba. "A da mutane ba su da masaniya a siyasance don neman hakkinsu. Khan ya bayyana yadda jam'iyyu biyu ke wawushe dukiyar al'umma.

Ya koya mana yadda za a kawo sauyi."

A group of students in Lahore
Bayanan hoto, Ƙungiyar ɗalibai a birnin Lahore na muhawara kan zaɓen Pakistan da ke tafe

Khan na janyo rarrabuwar ra'ayi a Pakistan.

Da nake magana da ƙungiyar ɗalibai a Lahore, wata matashiya mai suna Ayesha ta shaida mun cewa: "Imran Khan ƙwararren mai magana ne, ya san ƙarfin kalamansa amma maimakon ya haɗa kan matasa, sai ya haifar da rarrabuwa."

Wani dalibi ya nuna matukar bacin rai kan wannan sharhi yana mai cewa: "Imran Khan ya yi wa ƙasar nan komai kuma me ya faru? An kai shi kurkuku."

Wannan ya haifar da zazzafar cece-ku-ce. Sai da na kai ga shiga tsakani, ina tunatar da su: "Lamarin ba na faɗa ba ne, muna magana ne kawai."

Sau da yawa muhawarar siyasa a Pakistan haka take ƙarewa yanzu. Sai dai wani abu da daliban za su iya samun daidaito a kai shi ne cewa zaɓen ya kasance ba tare da maguɗi ba.

"Shin muna da ƴancin fitowa fili mu ba wa kowa goyon baya a ƙasar nan?" Amna take tambaya. "Idan ka ce wani abu ƴan sanda za su ɗauke ka, sun murƙushe muryoyin da suka bambanta da nasu."

Ita kuma ɗalibar kimiyyar siyasa Humaira ta yarda da cewa: "Tsarin dimokradiyya yana bunkasa ne kawai ba tare da tsangwama ba. Wannan ita ce kaɗai hanyar da za a kawar da mummunar rarrabuwar kawuna a Pakistan."