Mutane na ci mana fuska suna kiranmu 'yan bola

Asalin hoton, GABRIEL CHAIM
A tsakiyar shara da wasu ɓaraguzai da robobin da aka ƙona, wasu taron mutane na neman abinci da kuma robobin da za a ƙara maidawa kamfani a sake sarrafawa.
Amma ba wannan ba ce rayuwar da Alia ke fatan ganin ‘ya’yanta a ciki ba.
Kimanin shekaru uku kenan, take shiryawa kullum da ƙarfe 7:00 na safe, ta yi tafiyar awa biyu domin zuwa wajen zubar da shara na Tell Beydar da ke arewa masu gabashin Syria, a mafi yawan lokaci tana tafiya tare da Walaa.
Alia ta haifi ‘yarta ta farko lokacin da take tsakanin shekaru 12 zuwa 15, tana zama a gida ta kula da kananan yaranta.
Alia da Walaa ba sa dawowa gida sai bayan faɗuwar rana. A wannan lokacin, duka iyalin gida sun galabaita saboda yunwa.
“ Ko da yaushe burina shi ne ‘ya’yana mata su yi karatu kamar ko waɗannan yara mata,” in ji Alia.
“Amma yanzu sun biyo tafarkina, ba su san yanda za su yi karatu ba ko rubutu.”
Sharar ta sojin Amurka ce, a wajensu nan ne wurin samun abincinsu da kuma kudin shigarsu.
“Mutane suna kunyata mu; suna kiranmu ‘yan bola,” in ji Alia mai shekara 25.

Asalin hoton, GABRIEL CHAIM
Bayan kwashe sama da shekara 10 ana fama da yaƙi, an yi hasashen mutum 15.3 na buƙatar taimako, kamar yadda alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna. Kuma hudu cikin biyar na wannan adadi ba sa samun isasshen abinci.
‘Yar Alia, Walaa na ɗaya daga cikinsu.
“Muna nan ne domin neman nama, muna neman abinci saboda yunwa na damunmu,” in ji ‘yar shekara 12.
A yankin arewa maso gabashi da Ƙurdawa ke da iko da shi, yaƙin da ake yi da IS ya ɗaiɗaita tattalin arziƙin yankin.
Mijin Alia ma’aikacin gona ne. Amma bayan ya mutu shekara 10 da suka gabata haɗin kan iyalinsu ya ruguje.
Yaƙi da ƙazamin fari da yanayin da tattalin arziƙi ke ciki ya firgita ta.
Waye ke da iko da arewacin Syria
Da mota taje zubar da shara za ka ga yara na rige-rigen zuwa jikinta.
Su riƙa bincike cikin sharar da ake zubarwa a baƙaƙen ledoji, a nan Amer ɗan shekara 15 ke samun naman kazar da aka ci aka rage.
Ana yi yana tsotsar ƙashi yana kuma neman wani ƙari.
“Da akwai wani aiki da zanje na yi a wani wurin. Amma ba wani abu da zan iya yi,” in ji shi.

Asalin hoton, GABRIEL CHAIM
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amer shi ne zakaran gwajin dafi a gidansu da ke da yara 11.
Yana samun fam din Syria 3,000 zuwa 5,000 a kullum (wanda bai fi dalar Amurka 1-2) Idan ya siyar da robobin da ya samu. Hakan na isarsu rayuwa.
“Abubuwa sun ta’azzara bayan yaƙin. Ba ma iya sayan biredi,” in ji shi.
Ɗan uwan Amer na yaƙi da dakarun Amurka da ke yaƙi da IS a yankin.
A baya-bayan nan ya jikkata a wani samame da suka kai, kuma da wuya yake samun isassun kuɗaɗe da zai taimakawa gidansu.
“Ya kamata Amurkawa su ƙara taimaka mana,” in ji Amer.
Yaƙin da ake yi da ƙungiyar IS
A 2015, Amurka ta girke dakarunta a Syria domin goyon bayan mayaƙan Ƙurdawa a Syria a yaƙin da suke IS. Shekara hudu bayan nan kuma, sun bayyana samun nasara kan masu iƙirarin jihadin a Syria.
Yanzu yankin na ƙarƙashin gwamnatin Ƙurdawa, amma rayuwa ta sauya ba kamar a baya ba.
“Abin da yake faruwa a arewa maso gabashi sakamako ne na taɓarɓarewa halin da ƙasar ke ciki,” in ji shugaban kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ke aikin ci gaba a yankin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda dalilin tsaro.
Ƙasar arewa maso gabashi da ake da ita mai albarka ta noma da kuma mai da ke a ƙasanta ta taɓa zama hanyar samun kuɗin shiga ga Syria.
Yanzu tashin farashin kayan abinci, taɓarɓarewar tsaro da kuma shigar da waɗanda rikici ya raba da muhallansu ƙasar ya ƙara ta’azzara halin talauci da ake fama da shi.
Da yawan mutane yanzu sun dogara ne kan taimako da ake kaiwa domin su rayu, amma karanci kuɗaɗe da kayan aikin da za a shiga ko ina ya sanya taimakon ba ya shiga inda ake so.

Asalin hoton, GABRIEL CHAIM
A yanzu akwai dakarun Amurka 900 da ke aikin bayar da kariya ga barazanar tsaro.
Amma babu wanda ya san zuwa yaushe ne waɗan nan dakaru za su fice daga yankin.
“Idan Amurka ta fice daga yankin, ba za a ƙara awa 24 ba sai yankin ya koma ƙarƙashin ikon Turkiyya ko gwamnatin Syria,” in ji shi.
Mutane ba su da matsala da ko wanne ɓangare. Kawai mutane suna son su rayu da ƙima ne”.
Yara irinsu Amer da Walaa sun shafe duka rayuwarsu babu abin da suka sani sai yaki da damuwa.
“Na yi fatan inama muna da kuɗi da mun koma makaranta da aiki mai kyau a wani wurin na daban,” in ji Amer.











