Ƙoƙon kan da zai iya sauya tunanin masana kan tarihin ɗan'adam

Asalin hoton, BBC News
- Marubuci, Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
Wani ƙoƙon kan mutum da aka gano a ƙasar China ya nuna cewa mutane irin mu da ake kira a nazarin kimiyya da Homo sapiens sun samo asali ne kimanin shekaru kusan rabin miliyan kafin asalin zamanin da aka yi tunani.
Haka kuma binciken masana ya nuna cewa ƴan'adam sun yi rayuwa da wasu na'ukan halittun, ciki har da halittun neanderthals fiye da tunaninmu, kamar yadda masanan suka nuna.
Masu nazarin kimiyya sun ce sabon binciken nasu "ya sauya" tunanin da ake da shi game da tsarin halittar ɗan'adam, wanda idan aka tabbatar, zai iya sauya tarihin ɗan'adam baki ɗaya.
Sai dai wasu masanan suna da ra'ayin cewa duk da masu binciken sun yi ƙoƙari, lallai suna ganin akwai sauran rina a kaba.
Sabon binciken, wanda aka wallafa a ɗaya daga cikin manyan mujallum kimiyya na duniya ya zo da ba-zata, inda duniyar masana kimiyya ta shiga ruɗu, ciki kuwa har da su kan su masu binciken, waɗanda suka ƙunshi masana kimiyya daga jami'o'i a China da Birtaniya da gidan adana tarihi na Birtaniya.
"Da farko da muka fara ganin sakamako, mun yi tunanin hakan ba zai yiwu ba,'' in ji Farfesa Xijun Ni na Jami'ar Fudan wanda yake cikin masu binciken.
''Sai muka sake gwadawa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba ta hanyoyi daban-daban, wanda hakan ya sa muka aminta da sakamakon, kuma mun yi farin ciki sosai."

Asalin hoton, Fudan University
Lokacin da masana suka gano ƙoƙon kan mai suna Yunxian 2, sai suka yi tunanin na kakanninmu ne na asali da ake kira Homo erectus wato ƴan'adam masu faɗaɗɗar kai. Saboda ya kai kimanin shekara miliyan ɗaya da ya gabata, kafin lokacin da aka yi tunanin ƴan'adan irin na yanzu sun fara rayuwa.
Nau'in ɗan'adam na homo erectus sun fara rarrabuwa ne kimanin shekara 600,000 da suka gabata zuwa nau'ukan Neanderthals da nau'inmu na Homo sapiens.
Amma sai binciken Yunxian 2, wanda masana masu zaman kan su suka ƙara nazarta, ya nuna cewa ba Homo erectus ba ne.
Yanzu ana tunanin ƙoƙon kai ne na Homo longi, wanda nau'in halitta ne dangin irin na neanderthals da Homo sapiens.
Nazarin ƙwayoyin halitta sun nuna cewa a tare suka yi zamani, don haka idan Yunxian 2 ya yi rayuwa kimanin sama da shekara miliyan ɗaya da ya gabata a duniya, masana sun ce lallai hakan na nufin cewa nau'in halittar neanderthals na irin halittarmu ma sun yi rayuwa a lokacin.
Wannan nazarin ya canja lokacin da aka yi zaton ɗan'adam mai faɗaɗɗan kai ya samo asali, inda aka samu ɗoriyar kusan shekara rabin miliyan kan asalin lokacin da aka daɗe ana tunani, kamar yadda Farfesa Chris Stringer na gidan adana tarihi a Birtaniya.

Asalin hoton, Fudan University
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai hanyoyi biyu na fahimtar na'ukan halittar mutanen da suka rayu a ban ƙasa - ta hanyar nazarin ƙoƙon kai da ƙwayoyin halitta.
A nazarin ƙoƙon kan Yunxian 2, an yi amfani da hanyoyin biyu, kuma duka sakamako iri ɗaya aka amu.
Amma wasu masu binciken, kamar Dr Aylwyn Scally, masanin sauye-sauyen halittu a Jami'ar Cambridg ya ce akwai abubuwa da dama da suke buƙatar ƙarin bayani a sakamakon.
"Ko da kuwa akwai alƙaluma na bayanan ƙwayoyin halitta, zai yi wahalar gaske a iya daddale lokacin da wasu nau'ukan halittu suka rayu a cikin shekara 100,000 ko sama da haka."
Ya ƙara da cewa duk da cewa binciken Farfesa Ni da abokan bincikensa abin a yaba ne, lallai akwai sauran aiki a gaba, kuma ana buƙatar ƙarin bayani kafin a daddale maganar.
"Wannan hoton bai bayar da gamsasshen bayani ba, amma idan aka samu wasu bayanan daga wasu masu binciken daban, ina tunanin daga lokacin ne za mu fara amincewa da sakamakon," in ji shi a tattaunawarsa da BBC.
Asali an yi tunanin nau'in halittar ɗan'adam na Homo sapiens ya faro ne a Afirka kimanin shekara 300,000 da suka gabata, amma akwai alamomin tambaya kan cewa nau'in halittarmu ya samo asali ne daga nahiyar Asia.
Amma dai babu hujja mai ƙwari har zuwa yanzu, kamar yadda Farfesa Stringer ya bayyana, saboda akwai wasu gurabun rayuwar mutane a Afirka da Turai miliyoyin shekaru da dole a ƙara a ciki kafin a tabbatar da sakamakon binciken.
Gano halittun Homo sapiens da Homo longi da Neanderthals ya warware matsaloli da dama. Wannan na nufin za a iya tattara alamomi masu yawa daban-daban, sannan a alaƙanta su da asalin siffar halittar ɗan'adam na Homo erectus na nahiyar Asia da hiedbergergensis kamar yadda Farfesa Ni ya ce.
"Sauye-sauyen halittun ɗan'adam tamkar bishiya ne," in ji shi. "A bishiya akwai rassa da dama, waɗanda suka tsira daga asalin manyan rassan bishiyar waɗanda su kuma suna da alaƙa da juna. To a halittun ɗan'adam akwai rassa guda uku da suke da alaƙa da juna, kuma wataƙila sun rayu tare na kusan shekara miliyan ɗaya."
An gano ƙoƙon kan ne tare da wasu guda biyu a lardin Hubei, amma sai aka lalata su, wanda hakan ya sa aka yi zaton Yunxian 2 ƙoƙon kan halittar ɗan'adam na erectus ne.
Domin mayar da su asalin yadda suke, sai Farfesa Ni da abokan bincikensa suka ɗauki hoton ƙoƙon kan ta hanyar amfani da na'urar ɗaukar hoto ta musamman mai ƙarfin gaske.
Hoton ƙoƙon kan ne ya taimaka wa masanan su fahimci asalin nau'in halittar na asali.











