Sauye-sauyen da ake samu a jikin halittu daga haihuwa zuwa mutuwa

Asalin hoton, Getty Images
A cikin dukkan halittun ruwa masu ban al’ajabi, ba abin mamaki ba ne idan mutum bai san wata halitta mai suna hydra ba.
An samo sunan halittar ne daga daga tatsuniyar macijin nan da ke iya sake hada kansa. Hydra wani nau’in kifi ne da ke rayuwa a tsabtataccen ruwa.
Yana dan kama da kwayar shukar dandelion, amma yana da tsawo da dogayen hannaye a gefe daya sannan kuma ba shi da baki a bayyane.
Sai dai halittar na dauke da muhimman abubuwa da suka sa take jan hankalin masu nazarin halittu.
Halittar na iya gina kanta. Idan ka daddatsa hydra zuwa kanana, kowane bangare zai iya zama kifin hydra guda daya.
Wannan yanayin nasa na iya hada kansa da kansa ne ya yi matukar jawo hankalin masu nazarin halittu domin binciko ko akwai tabbatacciyar shaidar cewa ba ya mutuwa.
Me ya sa dangogin wannan halittar ba sa mutuwa haka nan da kansu? Sannan shin mutuwa dole ce?
A tsakanin karni na 20, an bayyana tsufa a matsayin sauyi tsakanin hayayyafa da kula da kwayoyin halitta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da farko, halittu na amfani da sinadaran jikinsu ne wajen kara girma da samun lafiya da kuma kula da kwayoyin halittarmu.
Daga yarinta zuwa girma, an fi mayar da hankali a kan a rayu sannan jiki ya yi karfi sannan a kasance cikin koshin lafiya.
Idan aka kai lokacin balaga da za a iya haihuwa, sai hankali ya koma kan hayayyafa.
Domin a halittu da dama, sinadaran rayuwa da dama sukan yi kadan, hakan ya sa mayar da hankali kan hayayyafa yakan zo da kalubale ga lafiya.
Dauki kifin salmon a misali da yake iya yin ninkaya da kansa ya fito wajen teku ya yi kwai, sai kuma ya mutu daga baya.
Yana yin komai domin zuwa wajen da zai yi kwai din, sannan da ya samu zuwa wajen, yakan yi duk mai yiwuwa ya yi abin da ya kamata.
Sai dai kifin ya samu komawa cikin tekun har ya iya rayuwa zuwa wata shekara a cikin ruwan sannan ya samu dawowa wajen yin kwan da wahalar gaske.
Sai dai ko da kafin ya mutu din, ya riga ya hayayyafa kuma ya gadar da kwayoyin halittarsa ga ‘ya’yansa.
Amma fahimtar yadda abubuwa suke mutuwa a yanzu na takaita ne.
Duk lokacin da halitta ta balaga, wasu abubuwa a jikinta sukan yi sanyi, sai kuma tsufa ya fara zuwa, wanda shi ke kaiwa zuwa ga mutuwa.
Amma sai dai hakan ba yana nufin gadar wa ’yan baya rayuwa ba ne, wanda hakan abin murna ne “a bangaren fifita wasu a kanka” kamar yadda Alexei Maklakov, wanda Farfesan nazarin halittu ne da ya kware a bangaren evolutionary biology and biogerontology a Jami’ar East Anglia da ke Ingila ya bayyana.
Sauyin rayuwa da kwayoyin halitta
A lokuta daban-daban na rayuwarmu, kwayoyin halittarmu suna canjawa.
Wasu canje-canjen da kansu suke faruwa, wasu kuma yanayin cimakarmu suke jawowa, wasu kuma wasu abubuwan ne daban kamar hasken layin wuta da sauransu.
Yawancin canje-canjen ba sa jawo komai ko kuma ba su da illa, amma akwai kadan masu amfani.
Kafin lokacin balaga, “duk wata kwayar halitta da ke rage damar haihuwa ga wata halitta ko kuma ke iya kashe halittar kafin ta haihu, ana iya tsince ta,” kamar yadda Gabriel Kountourides wanda masanin fannin canje-canjen halittu ne wato evolutionary biologist a Jami’ar Oxford ya fada.
Amma da zarar halitta ta kai balaga, za ta gadar da kwayoyin halittarta ga 'ya'yanta. A wannan lokacin ne canje-canjen da suke faruwa da kansu suke yin sanyi.
Dauki kifin salmon a misali. Kifin yana iya girma har ya manyanta ya hayayyafa.
'Ya'yan da ya haifa ma za su iya yin kwai. Idan aka samu canji a kwayar halittar kifin bayan ya yi kwai, wanda ya kara masa tsawon rayuwa da har zai iya kai wata shekarar (duk da cewa hakan zai yi matukar wahala) wadannan 'ya'yan ba za su nuna bambanci daban da ’yan uwansu ba.
Saboda kifin ya riga ya samar da 'yay'yan kafin a samu canjin na kwayar halittar.
Babu wani karin amfani da ake samu daga sauye-sauyen da suke faruwa da kansu a wajen ci gaba da kokarin zama cikin koshin lafiya ko hayayyafa.
Don haka duk wata kwayar halitta da ke da alaka da hakan, ba ta shiga cikin wadanda ake iya zaba domin kada su zama marassa muhimmanci sosai.
“Dole mutum na so ya kasance a raye. Amma sauye-sauyen da suke faruwa da kansu ba su da wani tasiri a kan hakan domin babu karin wasu abubuwan da za a iya gadarwa ga ‘yan baya,” in ji Kountourides.
Sai dai ba kowace halitta ba ce ke da irin yanayin kifin salmon na yin kwai sau daya kawai ba.
Wasu na ci gaba da rayuwa tsawon lokaci su cigaba da hayayyafa.
Yawancin canje-canjen da suke faruwa a kwayoyin halittarmu suna da ko dai illa ko rashinta ga jikinmu.
Jikinmu kan iya gyara wasu daga cikin canje-canjen da kansa, amma karfin jikin wajen gudanar da gyare-gyaren yana raguwa idan shekaru suka ja.
Sai dai tsufa da mutuwa suna faruwa ta hanyoyi biyu-idan canje-canjen kwayoyin halitta suka yi yawa saboda sauye-sauyen da suke faruwa da kansu sun yi sanyi.
Da kuma canji a kwayar halitta da ya kamata ya zama yana da amfani wajen haihuwa amma ya kasance yana da illa saboda tsawon rayuwa.
Misalin irin wannan shi ne sauyi a kwayar halittar BRCA.
Sauye-sauye a wadannan kwayoyin halittar suna jawo cutar kansar mama da ta mahaifa, amma kuma suna da alaka da kara karfin haihuwa ga mata.
Don haka zai iya yiwuwa sauye-sauye a kwayar halittar BRCA suna da amfani wajen kara yiwuwar haihuwa ga mata a farkon balagarsu, amma daga baya su zama suna da illa.
Wannan ba zai rasa nasaba ba da kasancewar sauye-sauyen da jiki ke yi da kansa suna yin sanyi bayan mutum ya balaga. Sai dai amfanin hayayyafar ya fi rashinsa.
“Duk abin da ya faru a farkon rayuwa, zai kasance ya danne duk wani abin da zai faru bayan lokacin daina haihuwa domin samun damar haihuwa shi ne ya fi muhimmanci,” in ji Kaitlin McHugh, wanda masanin halittu ne a Jami’ar Jihar Oregon.
Matsalar rashin hayayyafar kwayoyi
Matsalar rashin hayayyafar kwayoyin rayuwa wata alama ce ta sauyin da ke da amfani a farkon rayuwa, amma ke da illa daga baya.
Daina hayayyafar na kare mu daga cutar kansa domin zai hana kwayar halitta mai dauke da cutar kansar ta hayayyafa.
Amma daga baya kuma, irin wadannan kwayoyin halittar za su taru a jiki su jawo illa da kumburi, kuma su ne suke jawo cututtuka da dama na tsufa.
Duk da cewa mafi yawan halittu suna tsufa, akwai wasu da ba sa bayyana hakan. Tsirrai da dama suna bayyana ‘rashin hayayyafa’, misali akwai nau’ukan halittun da suke rayuwa na dubban shekaru.
Misali daya da ya fi jan hankali shi ne bishiyar pando da ke Dajin Fishlake na Gwamnatin Utah.
Bishiya ce ta hadakar kwayoyin halittar bishiyoyi masu kama da juna da suka hada tushe daya.
Bishiyar na da fadin eka 100 (400,000 sqm) kuma an kiyasta za ta yi nauyin da ya haura tan 6613 (tan 6,000). Wasu sun kiyasta cewa ta haura shekara 10,000.
‘Ya’yan kifin nan da ba ya mutuwa, wato hydra suna da wasu hanyoyi da suke bi wajen tsawaita rayuwarsu-domin suna iya sauyawa daga tsufa su dawo jariransu idan suna rashin lafiya ko sun gaji ko sun ji rauni.
“Amma a wani lokacin sai mutum ya tambayi kansa shin asalin kifin ne ya sauya ko kuma wani ne daban?” in ji McHugh.
Akwai kuma wasu bayanai da ke nuna cewa wasu na’ukan halittun sun fi samun yadda suke so idan sun girma- abin da ake kira da rashin hayayyafa mai illa ke nan- amma tabbacin hakan bai fito fili ba sosai, in ji Majlakov.
“Idan alakar halittun da inda suke rayuwa yana nuna cewa hayayyafarsu kadan ne, ko kuma ba za su iya hayayyafa da farko ba, wannan na iya sauya yadda canje-canjen rayuwarsu suke gudana,’ in ji Maklakov.
Za a iya samun misalin irin haka a dabbobin da namiji daya yake tarawa da mata da yawa kamar dabbar ruwan nan da ake kira walrus da kanki.
Namiji daya na iya kasancewa da mata da yawa. Don haka yawan wannan taron wanda hakan ke nufin ‘ya’yansa da jikokinsa za su karu ne a lokacin da ya kara girma sannan karfin haihuwarsa ke karuwa.
Duk da cewa gaskiya ne akwai wasu na’ukan halittu da suke iya zama da karfin haihuwarsu ko sun tsufa, ba sa cikin misalan rashin hayayyafa mai illa sannan bincike ya nuna yawancin lokuta ba su da nagarta, in ji Maklakov.
Sannan kuma ai dole walrus din ba zai ci gaba da rike garken ba har abada.
Sai dai saduwa na da alaka sosai da yadda za mu tsufa. Macen da ke saduwa akai-akai tana samun jinkirin daina haihuwa kamar yadda wani bincike da Megan Arnot da Ruth Mace na Jami'ar London ya nuna.
Sun ce wannan misali ne na musayar karfin jiki da ake amfani da shi lokacin daukar ciki da zai fi cancanta dukkan sauran jiki ya yi amfani da shi idan ba za ta iya daukar ciki ba.
Amma a sauran dabbobi, karin damar haihuwa na nufin saurin tsufa. Misali jemagen da ta haifa ‘ya’ya da yawa ta fi saurin mutuwa.
Watakila idan suka samun damar haihuwar, suna sanya dukkan karfinsu ne.
“Akwai wannan musayar a lokaci ma, halittar da ta samu haihuwa da kyau a farkon lokaci, ba ta iya samun hakan idan ta tsufa,” in ji McHugh, (Haka kuma ita dai hydra ba sa cikin wannan tsarin domin karfin haihuwarsu baya raguwa a rayuwarsu.)
Akwai kuma na’ukan halittun da tsawon rauwarsu ke bambanta tsakanin mace da namiji.
Misali kwari da kudar zuma da tururuwa za a iya samun sarki ko sarauniya da za su rayu sama da sauransu.
A wadannan misalan, me ya sa hayayyafar ba ta rage musu tsawon rayuwa?
Amsar ita ce watakila saboda sarakunan ko sarauniyoyin suna samun kariya daga hare-hare ba kamar sauran ba sannan akwai bambancin a tsarin rayuwarsu ta yadda tsarin tsufansu ba ya yin daidai.
Don idan har hayayyafa na da alaka mai karfi da tsawon rayuwarmu, me ya sa mutane suke ci gaba da rayuwa mai tsawo bayan sun daina haihuwa?
Bincike
Wani bincike da aka yi mai suna The grandmother hypothesis ya bayyana cewa yana da kyau manyan ’yan uwa su kasance a raye saboda hayayyafa tana zuwa da nata matsalolin.
Kaka za ta iya tabbatar da wasu kwayoyin halittarta suna nan domin ta taimaki jikokinta da su, don haka tsawon rayuwa zai iya kawo amfani idan aka yi la’akari da tsarin sauye-sauyen da suke faruwa da kansu.
“Zuriyar da suke tare da kakanninsu za su fi samun karfin hayayyafa, watakila saboda mahaifiyar za ta mayar da hankali wajen hayayyafar ne, ita kuma kakar ta dauki dawainiyar rainon wadanda aka haifa,” in ji Kountourides.
Amma lura da cewa jikoki suna da kamanceceniya a kwayoyin halitta da kakansu ne da kashi 25 kacal, suna da alaka da ita ne kamar yadda suke da alaka da ‘ya’yansu da ba iyayensu da ya ba.
“Wannan zai iya nufin cewa a da, ba mata da yawa ba ne suke iya rayuwa su ci gaba da hayayyafa bayan sun kai shekara 50.
Don haka karfin haihuwar mace da ta kai shekara 50 yake baya matuka,” in ji Maklakov, wanda hakan ke komawa ga ainihin bayanin tsufa, wanda ke nufin bayan hayayyafa, sauye-sauyen da ke faruwa kansu suna yin sanyi.
Yawancin abubuwan da suke faruwa da mu daga baya a rayuwa ba za su kasance na jin dadi ba-amma sai dai babu wani tabbataccen sauye-sauyen halittu da zai taimaka mana wajen kare mu daga faruwar hakan kuma.










