Ƴan Najeriyar da aka yi ta neman bayanai kansu a Google a 2022

Peter Obi, Oxlade, Asake, Yul Edochie

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Peter Obi, Oxlade, Asake, Yul Edochie

Shafin matambayi baya ɓata na Google, ya fitar da jerin fitattun mutanen da abubuwan da aka fi neman bayani a kan su a shafin cikin shekarar 2022 da ke gab da karewa.

Cikinsu akwai dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) Peter Obi, sai kuma sabuwar wayar salula ta Iphone 14, da mawakin nan dan Najeriya Oxlade da Asake na ciki.

Idan kuma aka zo kan batun da ya karade shafin shi ne, Afcon ne ke kan gaba, sai kuma batun yajin aikin malaman jami'o'in Najeriya na Asuu.

Amma ta fannin fitattun mutane, Oxlade ne a sahun gaba, yayin da Will Smith ya zama ja gaba a fannin jaruman fina-finai.

Batun yajin aikin Asuu ya shiga ciki ne saboda tsahon lokacin da aka dauka ana sa toka sa katsi tsakaninsu da gwamnati, lamarin da ya kai sun shafe wata takwas babu koyarwa.

Wasu labaran da za ku so

Shi kuwa Oxlade sunan shi ya karade Google ne, saboda bullar bidiyon tsiraicinsa a watan Junairun shekarr 2022.

Shi ma Peter Obi, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Party an yi ta neman bayanai a kansa ne saboda amfani da shafin intanet domin yada manufarsa ta siyasa.

Will Smith ya yi fice da zama na farko da aka fi neman bayanansa, bayan wanke Chris Rock da mari da ya yi, lokacin bikin ba da kyautar Oscar a watan Maris din shekarar nan.

Shi ma Yul Edochie ya karade shafin bayan sanarwar da ya yi na bayyanar matarsa ta biyu Judy Austin da ɗansu a watan Afirilu.

Ga bayananin yadda mutane sukai ta neman sunayen shafin google;

Bincike

1. Gasar cin kofin nahiyar Afirka

2. Yajin aikin Malaman jami'o'i na ASUU

3. Wayar salula samfurin IPhone 14

4. Oxlade

5. Kungiyar kawance ta NATO

6. Wakar Buga

7. Peter Obi

8. Ukraine

9. Gasar cin kofin duniya.

10. Asake

Mutane

1. Oxlade

2. Peter Obi

3. Asake

4. Black Sheriff

5. Casemiro

Taurarin fina-finai

1. Will Smith

2. Johnny Depp

3. Yul Edochie

4. Osita Iheme

5. Judy Austin

Fitattun 'yan wasa

1. Casemiro

2. Lisandro Martinez

3. Antony

4. Gabriel Jesus

5. Raphinha

Wakoki

1. Finesse lyrics

2. Overdise lyrics

3. Rush lyrics

4. If i broke na my business lyrics

5. Palazzo lyrics

Girke-girke

1. Fried Rice recipe

2. Afang soup recipe

3. Jollof Rice recipe

4. Banana bread recipe

5. Parfait recipe

Fitattun mutane

Peter Obi, Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar

Asalin hoton, Others

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

1. Wane ne dantakarar mataimakin shugaban kasa ga Peter Obi

2. Wace ce Sarauniya Elizabeth

3. Wace ce greek god of war

4. Wanene dan takarar shugaban kasa na jam'iyyr APC

5. Wane ne abokin takarar Atiku

Wayoyin salula

1. Iphone 14 pro max

2. Iphone 13 pro max

3. Tecno Camon 19

4. Infinix Note 12

5. Tecno Spark 12

6. Infinite Note 11

7. Redmi Note 11

8.Infinix Smart 6

9. Tecno Spark 9

10. Tecno Spark 8

Fina-finai masu gajere da dogon zango

1. Anikulapo

2. Blood Sisters

3. House of Dragon

4. Thor - Love & Thunder

5. The Woman King

6. Selina Tested

7. Tinder Swindler

8.Black Panther 2

9. Eternals

10. All of us are dead

Wakoki

1. Buga - Kizz Daniel

2. Overdose - Mavin

3. Machala - Berri Tiga ft Carter Efe

4. Calm Down - Rema

5. Rush - Ayra Starr

Mace-mace

1. Queen Elizabeth

2. Osinachi Nwachukwu

3. Ada Ameh

4. Rico Swavey

5. Takeoff

Mawaka

1. Oxlade

2. Asake

3. Black Sherrif

4. Portable

5. Lil Tjay

Me ake nufi da.....

1. Me ake nufi da Lupus

2. Me ake nufi da NATO

3. Me ake nufi da NFT

4. Me ya ya haddasa yaki tsakanin Rasha da Ukraine

5. Me ake nufi da Zazu Zeh

6. Mene ne PVC

7. Me ake nufi da jinsi

8. Me ake nufi da Sapa

9. Da me Greta Thunberg ta yi fice

10. Me ake nufi da dan kunne a kimiyyance