Nasarori da ƙalubalen da shafin BBC Hausa na Facebook ya sukanta Shekara 12 da kafa shi

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Bayanin Aliyu Tanko kan shekara 12 da kafa shafin BBC Hausa Facebook
Lokacin karatu: Minti 3

Shafin Facebook na BBC Hausa ya cika shekara 12 da kafuwa a ranar 4 ga watan Agustan 2021.

Shafin na daya daga cikin hanyoyi daban-daban na zamani da BBC Hausa ke amfani da su wurin isar da labarai ga mabiyanta musamman matasa.

Mutum sama da miliyan hudu ne ke samun labarai ta wannan kafa da BBC Hausa ta samar shekaru 12 da suka wuce.

A yau za mu yi waiwaye ne kan yadda aka kafa shafin, da irin abubuwan da yake wallafa, da nasarori da kuma ƙalubalen da yake fuskanta.

Yaushe aka buɗe shafin?

An buɗe shafin BBC Hausa Facebook ne a ranar 4 ga watan Agustan 2009, a lokacin Hajiya Jamilah Tangaza ce shugabar sashen.

Sai dai abu na farko da aka wallafa a shafin an yi shi ne a ranar 11 ga watan Janairun 2010.

"Shafin BBC Hausa Facebook na daga cikin shafukan kafofin yaɗa labarai na farko-farko da aka buɗe a Najeriya," kamar yadda shugaban sashen Hausa na yanzu Aliyu Abdullahi Tanko ya ce.

"A lokacin Facebook kansa bai samu karɓuwa sosai ba don wasu ma sun zata shafi ne na soyayya.

"Amma ga shi cikin shekaru Facebook ya zama wata babbar kafa ta yaɗa labarai," kamar yadda Aliyu ya ƙara da cewa.

Wannan layi ne

Su waye suka fara bin shafin?

Kamar yadda aka sani a duk lokacin da aka samu sabon shafi a Facebook ko wani dandalin daban, to dole akwai wadanda suka fara bin sa.

Mutum 10 na farko da suka fara bin shafin BBC Hausa a lokacin da aka buɗe shi sun haɗa da shugabar sashen ta lokacin Jamilah Tangaza.

Wani mai bin shafin tun lokacin da aka buɗe shi har zuwa yau Zaydu Bala Ƙofa Sabuwa ya ce "ina iya tuna lokacin da aka buɗe shafin Jamila Tangza ta turo min saƙo.

"A cikin saƙon ta ce yau mun buɗe shafin BBC Hausa, kuna iya fara bin mu, sannan ka gayyato mana mutane don ku bayyana ra'ayoyinku," a cewar Zaidu.

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Ya ce daga cikin mutanen farko bayan Jamilah Tangaza da suka fara bin shafin akwai;

  • Bashir Sa'ad Abdullahi, editan ofishin BBC Hausa na Abuja
  • Aliyu Abdullahi Tanko, editan sashen Hausa na BBC na yanzu
  • Nafisa Ahmed, tsohuwar ma;aikaciyar BBC Hausa
  • Suwaiba Ahmed, tsohuwar ma'aikaciyar BBC Hausa
  • Aliyu Muktar Kwalli.
  • Marigayi Bilyaminu Abdullahi Adanji
  • Muntaka Abdulhadi Dabo Zaria
  • Ishak Abdullahi Dan Rimi Bena
  • Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi.
Wannan layi ne

Nasarori

Wannan shafi na BBC Hausa Facebook ya samu nasarori da dama kama daga kan yawan mabiya, zuwa yawan labaran da ake sakawa don mutane su karanta, da kuma yadda ake samun labarai daga wajen masu bin shafin.

Mabiyan shafin BBC Hausa a yanzu sun haura miliyan huɗu. Sannan ita ce ta biyu a yawan masu bibiya kuma ta huɗu a mafi yawan masu bibiyar shafin a jerin kafafen yada labaran Najeriya.

BBC Hausa Facebook na ɗaya daga cikin manyan shafuka biyar na kafafen yaɗa labarai a Najeriya da ya fi ɗaukar hankalin mutane da yawan tattaunawa da kallon bidiyonsu da hotuna.

Kazalika shafin ya zama hanyar samo labarai da bayanan abubuwan da suke faruwa a wasu sassan da mabiyansa suke, inda BBC kan yi bincike da neman ƙarin bayani a wajensu.

Sannan shafin ya kasance mai tafiya da zamani ta yadda yake taɓo batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar masu bibiyarsa.

A kan wallafa labaran duniya da na nishaɗi da na ilimintarwa da na zaburar da mutane don su yi wani abin kirki da dai sauransu.

Bidiyo da hotunan da ake wallafawa a yanzu a shafin sun nunka na da nesa ba kusa ba.

"Kusan kullum a yanzu har a ƙarshen mako a kan sa a ƙalla bidiyo ɗaya," kamar yadda Aliyu Tanko ya ce.

Wannan layi ne

Matsaloli?

Aliyu Tanko

Babu wata tafiya da ba a samun matsala a tattare da ita.

A tafiyar shafin BBC Hausa ta shekara 12 babu wata gagrumar matsala sai dai rin ta fama da jama'a.

Babban ƙalubalen kamar yadda Aliyu Tanko ya ce shi ne yaɗa labaran ƙarya da sunan BBC Hausa, "ana buɗe shafukan boge da wallafa bidiyo da hotuna na ƙarya a ce daga BBC ne."

"Amma Alhamdulillahi a yanzu muna ƙoƙarin ƙaryata hakan ta wajen yin bayani ga mabiyanmu," in ji shi.

Sau tari mutane ba sa gane yadda kan abubuwa suke sai su fara zagi da cin mutunci.

Wannan wani abu ne da BBC ɗin take haƙuri da kawar da ido a kansa amma kuma duk da haka "akwai ciwo, kana bakin ƙoƙarinka amma ana zagi na rashin dacewa," a cewar da yawan ma'aikatan.

Baya ga haka kuma wani ɗan ƙalubalen shi ne na yadda aikin ya ƙaru a yanzu, yawansa da kuma yadda masu bibiyar suke son komai sai an amsa musu idan sun yi magana.

"Hakan abu ne mai matuƙar wahala ganin irin dubban saƙonnin da ake aika wa a kan kowane labari," in ji Umar Rayyan, babban mai kula da shafin.

Daya matsalar kuma ita ce ta yadda masu yin tsokaci sai yawanci su dinga ƙorafin cewa sai an karanta saƙonninsu a rediyo a yayin shirye-shirye.

Amma dai duk da irin wadannan abubuwa, a iya cewa BBC Hausa Facebook dai kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Wannan layi ne