Ana tantamar makomar Ronaldo a Al-Nassr, Zubimendi zai koma Arsenal

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ana tantama kan makomar Cristiano Ronaldo a Al-Nassr, Martin Zubimendi ya amince baka da baka zai koma Arsenal daga Real Sociedad, Erik ten Hag ko Cesc Fabregas ne zai maye gurbin Xabi Alonso a Bayer Leverkusen.

Ɗan wasan Real Sociedad, Martin Zubimendi, mai shekara 26, ya amince baka da baka zai koma Arsenal - kuma ɗan wasan tawagar Sifaniyar zai je Gunners da zarar ta biya ƙunshin kwantiraginsa (£50.75m). (Talksport).

Sai dai wasu rahotanni daga Sifaniya na cewa Xabi Alonso, kociyan Bayer Leverkusen ya saka sunan Zubimendi cikin ƴan wasan da zai je da su Real Madrid da zarar ya maye gurbin Carlo Ancelotti. (AS),

Ƙungiyar da ke buga gasar Saudiyya, Al-Hilal na shirin yin taro karo na uku da wakilan ɗan wasan tawagar Portugal, Bruno Fernandes domin ya koma can da taka leda, duk da cewar kociyan Manchester United, Ruben Amorim na fatan ɗan ƙwallon zai ci gaba da taka leda a Old Trafford. (Mirror)

Tsohon kociyan Manchester United, Erik ten Hag da na Como, Cesc Fabregas suna daga cikin waɗan da ake cewa ɗaya ne zai maye gurbin Xabi Alonso a Bayer Leverkusen. (Kicker - in German)

Daraktan wasannin Arsenal, Andrea Berta na kokarin sayo mai cin ƙwallaye, yanzu yana hangen ɗan wasan tawagar Sweden, Viktor Gyokeres ko kuma mai taka leda a RB Leipzig ɗan kasar Slovenia, Benjamin Sesko, (TBR Football)

Ɗan wasan tawagar Belgium, Leandro Trossard na tattaunawa da Arsenal kan batun tsawaita yarjejeniyarsa, bayan da ƙungiyoyin Saudiya ke son sayen ɗan ƙwallon mai shekara 30. (Mail)

Ana tantama kan makomar Cristiano Ronaldo a Al-Nassr, bayan da aka dakatar da batun tsawaita kwantiraginsa kaka biyu a ƙungiyar. (Marca)

Manchester United ta zaɓi ta taya ɗan wasan Bournemouth, Antoine Semenyo, maimakon na Brentford, Bryan Mbeumo. Haka kuma tana fatan sayen ɗan wasan Wolves, Matheus Cunha da na Ipswich Town, Liam Delap. (Sky Sports, via Teamtalk)

Ɗan wasan tawagar Jamus, Leroy Sane bai yi farin ciki da ƙunshin yarjejeniyar da Bayern Munich ta gabatar masa ba, kenan zai bar ƙungiyar a karshen kakar tamaula, bayan da ake alakanta shi da Arsenal ko kuma Chelsea ko kuma gasar La Liga. (Sky Sport Germany)

Ana ta alakanta mai taka leda a Bayer Leverkusen, Jonathan Tah da Bayern Munich ko kuma Barcelona da zarar yarjejeniyarsa ta kare - ɗan kasar Jamus ya ce ya kusan ya fayyace makomarsa nan gaba kaɗan. (Sport Bild - in German)

Marseille tana duba yadda za ta ɗauki matashin Arsenal, Jakub Kiwior a shirin da take na ɗaukar masu tsare baya (Foot Mercato - in French)